#dora lall
Explore tagged Tumblr posts
gudrunvisuals · 2 years ago
Text
Tumblr media
0 notes
isausmanmohd · 2 years ago
Photo
Tumblr media
HIRA CIKIN SHEHU IBRAHIM(Kashi Na SHIDA(06); WANE NE SAHIBUL FAIDHA(Shehu Ibrahim Niasse(R.A)??? *. 'KIRANSA ZUWA GA ADDINI; 'Kira Zuwa Ga ALLAH Babu Kasar Da Bai Kai Shehu Ibrahim(R.A) Ba, Mutum Ya Karanta 'Kasidarsa Ta(Jama'ata Wajudan) Ya Sha Labari.. Har 'Kasar Italy Cibiyar Kiristancin Duniya Shehu Ya Je, Ko Da Yake Dai Bai Shiga Fadar Paparoma Ba, Ba Kamar Yadda 'Yan'uwa Da Yawa Suke Fada Ba.. Lalle Turawa Sun Nemi Shehu Ya Je, Bayan Da Suka Ga Girmansa Da Abubuwan Mamakinsa, Amma Sai Shehu Ya Raina Kasuwar: وجئت قصر الروم إن الروم *** قد غلبت وعوض لن تقوم قالوا: تزور الباب لو دراني *** حقا لهرول إلى بستاني حجبته بنفسه عن نفسه *** لو قدته عرف معنى قدسه ودام منه ذكره وعزه *** وغاب عنه أنسه وجنسه Wani Abin Sha'awa Shi Ne: Shehu Bai San Tsoro Ba a Halin Gwagwarmayarsa, Ya Tari Gaban Nasara Da Turawan Mulkin Mallaka, Kuma Ya Bayyana 'Kiyayyarsa Gare Su a Lokacin Da Kowa Ke Kaffa-Kaffa Da Su, Shehu Ya Zaga Duniya Ya Hadu Da Shugabannin 'Kasashe Ya Nemi Su Mara Masa Baya, Sannan Ya Shige Gaba Sai Da Aka Fatattaki Turawan Mulkin Mallaka Daga Afrika, Ya Kuma Katsattsare Ya Hana Su Komowa: "...حكم الأجانب في بلاد الأجانب مضى إلى غير رجعة، فأفريقيا للأفريقيين." Shehu Kenan Yake Dad'a Tauna Tsakuwa:"Mulkin Ba'ki a Kasashenmu An Gama Kenan Ba Kuma Za a Kuma Ba; Afrika Ta 'Yan Afrika Ce.." Shehu Ibrahim Niasse(R.A) Ba Wai Kadai Ya Kasance Mara Tsoro a Halin 'Kiransa Zuwa Ga ALLAH Ba, Amma Ya Kasance Tsayayye Ne Akan Aikata Abin Da Kitabu Da Sunna Suka Bayyana, Kamar Kuma Yadda Yake Tsaye Akan Tsawatarwa Muridansa a Ko Ina a Fad'in Duniya Domin Su Yi Ruqo Da Jelar Abin Da Ya 'Dora Su Akai; Ku Saurari Lafazinsa a Cikin Diwani: تمسك بأذيال النبي متابعا *** مذاهبه والمحدثات فلا لا Ma'ana: "Ka Yi Riqo Da Igiyar ANNABI Kana Mai Bibiyar Hanyarsa, Amma Kar Ka Yarda Da KA-JI-TSORO a Cikin Addini". (Daga Alkalamin; Dr. Muhammad Nazifi Bichi). Alhamdulillah🙏🙏🙏 ALLAH KA SADA MU DA DUKKAN ALKHAIRAN DAKE CIKIN WANNAN WATAN, YA BAMU ALBARKAR MASU ALBARKA, AMEEN🙏 (at Nigeria) https://www.instagram.com/p/CoAoII5IVUf/?igshid=NGJjMDIxMWI=
0 notes
Text
Tumblr media
*_🔦HAƘURI BISA JARABAWAR RAYUWA🔦_*
_🔦Labarin wani mutum daga cikin mutanen baya, wanda Allah ya ce: Bawa na ya rigaye ni da kansa, don haka a haramta masa Aljanna_
🔦Sahabi Jundubu Dan Abdullahi Albujali -Allah ya yarda da shi- ya ce: Annabi (SAW): *"An yi wani mutum cikin wadanda suka gabace ku yana da wani ciwo sai ya yanke kauna (daga samun lafiya), sai ya dauki wuka ya yanke hannunsa, jini bai dauke (daga zuba) ba har ya mutu. Sai Allah yace: Bawa na ya rigaye ni da kansa, don haka Na haramta masa Aljanna".*
*📚[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]*
*🔦Bayani:*
Annabi (SAW) ya bawa sahabbansa labarin wani mutum cikin al'ummar da suka gabace mu ya kasance yana da wani ciwo mai azabar ciwo, sai ya karaya ya yanke kauna da warkewa, ya kasa yin hakuri da azabar da yake sha, ko dan neman lada ma a wajen Allah, saboda karancin imani da sakankancewa da Allah, sai ya dauki wuka ya yanke hannnun sa da ita, sai jini ya yi ta zuba, yaki tsayawa har mutumin ya mutu.
Sai Allah yace: Wannan bawan nawa ne ya kagara ga zuwan rahama ta da waraka ta, ba shi da dauriya kan jarabawa ta, saiya yi gaggawar hallaka kansa, yayi tsammanin ya rage ajalinsa ta hanyar kashe kansa, sai Na haramta masa shiga Aljanna,, wanda aka haramtawa Aljanna kuwa, to wuta ce makomarsa.
*Faidojin Hadisin:*
1- Wajabcin haquri wajen fuskantar musibu da jarabawa daga Allah –Maɗaukakin Sarki – ta hanyar kiyaye harshe daga fadin abin da bai dace ba daga bakin mara lafiya, ko gayawa mara lafiya. Da dauriya akan ciwon, kamar yawaita kuka, ko, kamar jifa da burgima ko yaga kaya, ko kuma kamar mutum ya kashe kan sa.
2- Kowa da irin jarabawar da Allah yake yi masa. Hakuri da juriya ke sa mutum ya samu rahamar Allah.
2- Hadisin yana karantar da mu haramcin kashe kai; ko yin abin da zai jawo ga rasa rai.
3- Yana karantar da mu haƙuri da juriya akan jarabawar da Allah ya dora mana.
4- Mu fahimta cewa dukkan wani abu da ya same mu daga Allah ne, wani baya iya dorawa kan sa wani cuta sai da izinin Allah.
5- Mu tuna Fadin Allah cewa:
( وَلَنَبْلُوَنَّكُمْ حَتَّىٰ نَعْلَمَ الْمُجَاهِدِينَ مِنكُمْ وَالصَّابِرِينَ وَنَبْلُوَ أَخْبَارَكُمْ )
Kuma lalle ne, Munã jarraba ku, har Mu san mãsu jihãdi daga cikinku da mãsu haƙuri kuma Muna jbrraba lãbãran ku.
*🔦Allah Ka Bamu Ikon Juriya Da Cin Jarabawarka 🤲🤲*
*✍️Abdullah A Abdullah Abou Khadeejatu Assalafeey*
21/03/2022.
*🎙️SAWTUL HIKMAH MEDIA TV🎙️*
08032312988
0 notes
isiyasy · 5 years ago
Text
KASAR DA AKA YI ALKAWARI
Tumblr media
Haka dai kaddara ta gitta kan wannan al'amari kuma ta ci gaba da jagorantarsa, ta yadda bayan dan wani lokaci da kuma 'yar tafiya, sai sojojin Umayyawa suka katse wa Imam Husain (a.s) hanya lamarin da ya tilasta masa sauka. Daga nan sai Husaini (a.s) ya sauka yana tambaya, kamar yana neman Karbala ne: "Mene sunan wannan guri?", sai aka ce masa Kasar al-Taf, sai ya ce: "Shin akwai wani suna na daban kuma da ake kiran wannan waje da shi?", sai aka ce masa ana kiran wajen Karbala. Sai ya ce: "Ya Allah ina neman tsarinKa daga Karb (wahala, bakin ciki) da kuma bala' (bala'i)". Daga nan sai ya ce: "Wannan shi ne gurin wahala da bala'i (karb wa bala'), ku sauko, nan ne karshen tafiyarmu, wajen da za a zubar da jininmu, nan ne muhallin kaburburanmu, wannan dai shi ne abin da Kakana (s.a.w.a) ya ba ni labarinsa(1)". Wannan rana dai ita ce ranar Alhamis ta biyu ta cikin watan Muharram shekara ta 60 bayan hijira(2), inda Husaini (a.s) tare da sahabbansa suka sauka a kasar Karbala, kasar jini, sadaukarwa, shahada, tabbatuwa da kuma yunkuri. Daga nan sai Husaini (a.s) ya kafa tantinsa da gyara makamansa, yana rera wannan wakar: Ya kai lokaci, kaiconka a matsayin aboki, Shin kasa da sama kake da shi.Na daga mabukaci da abokai nawa suka mutu, Alhali kuwa lokaci ba ya wadatuwa da mamayi.Dukkan wani mai rai zai bi (wannan) hanya, Akwai alkawarin da yafi saukin cikawa kamar mutuwaLalle al'amarin yana hannun Mai Daukaka ne kawai(3). Haka Imam Husain (a.s) ya ci gaba da rera wannan waka ita kuwa Zainab, kanwarsa wacce kuma za ta kasance mai isar da sakon wannan yunkuri a nan gaba, ta saurara tana jinsa tana mai lura da irin halin da yake ciki da kuma abin da ya ke ji. Sai ita ma cikin sauti da ke cike da tausayi da kuma tada hankali ta ce: "Wannan kalami ne na mutumin da ya tabbatar zai mutu". Sai ya ce mata: "Lalle kan Ya 'Yar'uwata", sai ta ce: "A'a saboda irin halin da yake ciki, Husaini (a.s) yana sanar da ni mutuwarsa(4)". Haka dai wadannan sojoji suka ci gaba da kasancewa, shi kuma Ubaidullah bn Ziyad ya ci gaba da turo sojojinsa iyakan iyawarsa. Daga cikin mashahuran mutanen da ya dora wa wannan nauyi na aikata wannan mummunan aiki na kashe Imam Husain (a.s) shi ne Umar bn Sa'ad bn Abi Wakkas, duk da cewa daga farko ya ki amincewa da hakan, amma daga baya ya amince saboda barazanar da Ibn Ziyad din ya yi masa na hana shi mukamin da aka ba shi na gwamnan garin al-Ray. Kafin amincewa da wannan aiki dai, Umar bn Sa'ad ya shafe tsawon dare yana ta tunani kan ko ya zabi mulki da dan wani jin dadi na duniya ko kuma ya zabi kula da lahira da kuma kula da jiga-jiga na adalci da gaskiya wanda za su hana shi aikata wannan mummunan aiki da kuma zubar da wannan jini mai tsarki. Daga karshe dai ya amince da mulki da jin dadin duniya da kuma taimakawa wajen kashe masu kira zuwa ga gaskiya da kuma adalci. An jiyo shi yana ta nanata wadannan baituka na waka: Shin zan bar mulkin Ray alhali ya kasance burinsa, Ko zan koma in zama abin zargi don kashe Husaini. Lalle cikin kashe shi akwai wuta wacce ba ta da, Shamaki, sai dai mulkin Ray kuma abin so na ne(5). Don haka da gari ya waye sai ya amince da wannan nauyi da aka dora masa, ya kama hanya ya nufi inda Husaini (a.s) ya ke yana jagorantar kimanin dakarun dubu hudu, inda ya sauka a Nainawa da kuma mai da wurin sansanin sojojinsa. Lokacin da ya sauka a wurin da kuma kewaye Imam Husain (a.s) da sahabbansa, sai ya fara tattaunawa da Imam din (a.s) inda suka tsayar da wasu abubuwa tsakaninsu, daga nan sai ya rubuta wa Ibn Ziyad halin da ake ciki da kuma irin yarjejeniyar da suka kulla da Husaini (a.s) da ta hada da kawo karshen mamayan da suka yi wa masa da kuma ba shi damar komawa inda ya fito don kiyaye zubar da jinin da aka kama hanyar zubar da shi. Lokacin da wannan wasika ta Ibn Sa'ad ta shiga hannun Ibn Ziyad, da farko dai ya yarda da wannan shawara ko kuma yarjejeniya da Ibn Sa'ad ya cimma da Husaini (a.s), to sai dai kuma daga baya ya canza ra'ayinsa lokacin da Shimr bn Zil-Jawshan, wanda ya kasance daga cikin mafiya gaba da Husaini da kuma Ahlulbaiti (a.s), ya sa baki cikin lamarin da nuna masa cewa matukar ya bar Husaini (a.s) ya fita daga wannan hali da yake ciki, to kuwa zai sake zuwa ya tara karfi da kuma ganin bayan dakarun Umayyawan. Don haka babu wani abin da ya kamata ya aikata face ya bar shi cikin wannan hali da kuma tilasta masa yin mubaya'a da kuma mika wuya ga mulkin Ubaidullah bn Ziyad. Wannan shawara dai ita ce ta canza komai da kuma haifar da wannan mummunan ta'addancin da ya fi kowane ta'addanci cikin tarihi. Ta haka ne dai abubuwan da suka faru cikin tarihi suke fara faruwa saboda daukan wani mataki ko kuma bijiro da wani ra'ayi kamar wannan kalma ta Shimr bn Zil Jawshan, wacce ta taimaka nesa ba kusa ba wajen kisan gillan da aka yi wa Husaini (a.s) da mabiyansa, wacce daga baya ta yi sanadiyyar faduwar gwamnatin zalunci ta Umayyawa da kuma kawo karshenta. Ubaidullah bn Ziyad dai ya amince da wannan shawara ta Shimr, don haka sai ya rubuta wasika ta barazana ya ba wa Shimr din don ya kai wa Umar bn Sa'ad, yana mai umartansa da ya aikata abin da aka ce masa ko kuma ya sauka daga mukamin da aka ba shi ya mika shi ga Shimr bn Zil Jawshan. A cikin wannan wasika dai Ibn Ziyad ya rubuta cewa: "Ni ban tura ka wajen Husaini don ka yi sulhu da shi ko kuma ka lamunce masa ransa ba ko kuma ka nemi uzuri daga gare shi ko kuma ka nema masa ceto daga gare ni ba. Ka gane cewa, idan har Husaini da mutanensa sun yarda suka mika wuya, to ka aiko su zuwa gare ni, idan kuwa har sun ki amincewa da haka, to ka fada musu ka kashe su da kuma lalata jikkunansu, don kuwa sun cancanci hakan. Bayan kashe Husaini ka sanya dawaki su yi sukuwa akan kirgi da kuma bayansa, don kuwa shi dan tawaye ne, ina ganin hakan ba zai kasance mummnan abu ba bayan mutuwa. Wannan dai shi ne abin da nake so ka yi masa, in ka aikata hakan kuwa to za mu saka maka a matsayin mutum mai ji da kuma da'a. Idan kuwa ka ki aikatawa, to ka sauka daga aikinmu ka bar sojojinmu ka mika su ga Shimr bn Zil Jawshan, don kuwa mun riga da mun ba shi ikonmu. Wassalam(6)". Bayan rubuta wannan wasika sai Shimr ya karba ya kama hanya yana cike da sharri da kuma mugunta a cikin zuciyarsa, da isarsa sai ya mika wa Umar bn Sa'ad wasikar da take ba shi zabi biyu, ko ya fada wa Husaini (a.s) da mabiyansa, wanda zai kai shi ga samun mulki da kuma matsayi a wajen magabatansa, ko kuma ya ki aikata hakan ya rasa wannan matsayi, bayan karanta wasikar sai ya amince da zaban duniya da kuma mulki a kan gaskiya da kuma yardar Allah. Daga nan sai ya tsayar zai jagoranci wannan yaki da kuma zubar da jinin Husaini (a.s). Don haka a ranar 7 ga watan Muharram sai Umar bn Sa'ad ya tura sojojinsa da su kange Husaini (a.s) ta bangaren Kogin Furat, wato su shiga tsakanin Iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a) da yadda za su samu ruwan sha, don su mutu cikin kishin ruwa ko kuma su mika kai, hakan dai daya ne daga cikin makircin yaki. Kana kuma ya fara rarraba sojojinsa da kuma nada kananan kwamandoji da za su jagorance su, suna masu matsawa kusa da tantunan Husaini da mabiyansa. Wannan lamari dai na kusantan tantunan Husaini (a.s) ya faro ne daga ranar 9 ga watan Muharram, lokacin da sojojin Umayyawa suka fara daddaga takubba da masunsu cikin fushi da kurari. A daidai wannan lokaci kuwa Husaini (a.s) yana zaune a gaban tantinsa yana kallon wannan hamada ta al-Taf cike da tunanin irin wannan mawuyacin hali da ake ciki da kuma irin abubuwan da zai faru nan gaba ga wannan yunkuri da kuma ma'abuta son gaskiya da 'yanci. A daidai wannan lokaci dai Husaini (a.s) bai san matsayar da Umar bn Sa'ad ya dauka ba dangane da su na kai musu hari, don haka sai ga Zainab ta nufo shi tana mai cewa: "Ba ka ji sautin da ke zuwa kusa-kusa ba". Zainab ba ta bar wannan guri ba, sai ga Abbas bn Ali (a.s), kanin Imam Husain (a.s) ya iso yana cewa: "Ya Dan'uwana, abokan gaba fa sun iso". Nan take Husaini (a.s) ya mike yana ganin ya dace ya yi magana da sojojin Umayyawa don sanin halin da ake ciki, don haka sai ya bukaci Abbas da ya yi magana da su don jin ra'ayinsu. To sai dai kuma ina!, alkawarin mulki da shugabancin da aka musu ya sanya su cikin maye, don haka sai rige-rige suke yi wajen yakan Husaini (a.s) da zubar da jininsa mai tsarki don samun matsayi, mulki da kuma dukiyar da aka yi musu alkawari, don haka amsarsu dai ita ce: "Ko dai Husaini ya mika wuya ga mulkin sarki ko kuma mu yake shi". Daga nan sai Abbas ya komo ya gaya wa Husaini (a.s) matsayar kwamandojin sojin Umayyawan. Don haka dai Imam Husain (a.s) ba shi da wani abin yi in ban da yaki don kuwa ya riga da ya dau matsayar babu ja da baya "Hakika kamata ba zai yi mubaya'a ga mutum kamar Yazid ba", don haka sai ya ci gaba da fadin: "Wallahi ba na ganin mutuwa face sa'ada, rayuwa kuwa tare da azzalumai a matsayin wulakanci". Ya ci gaba kuma da bayyanar da taken nan da ya gada daga Manzon Allah (s.a.w.a), wanda kuma ya bayyanar da shi ga Umayyawa cikin 'yan kwanakin da suka gabata a yankin Al-Baidha': "Ya Ku Mutane! Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: 'Duk wanda ya ga wani ja'irin sarki, wanda ya ke halalta haramun din Allah, mai kwance alkawarin da ya yi, mai saba wa Sunnar Manzon Allah, mai zaluntar bayin Allah, amma ya zuba ido ba tare da ya yi kokarin gyara shi a aikace ko kuma da zance ba, to lalle hakkin Allah ne Ya shigar da shi makomarsa". Imam Husaini (a.s) dai yana ganin mulkin Yazid, siyasarsa da jami'an da suke tare da shi a matsayin misdaki ko kuma hakikanin irin mutanen da Manzon Allah (s.a.w.a) ya ke nufi a wannan kalami nasa, don haka babu wani abin da ya rage masa face shiri don fuskantar wannan makiyi, da kuma daga tutar jihadi da yunkuri don tabbatar da gaskiya da kuma gudanar da shari'ar Allah. Don haka sai ya bukaci Abbas da ya tafi wajen Ibn Sa'ad don neman ya ba su dama ta dare guda don yin tunani kan wannan al'amari da kuma daukar matsayar da ta dace a gobe (Goma ga watan Muharram -Ranar Ashura). Don haka Abbas ya tafi ya shaida wa Ibn Sa'ad wannan bukata ta Husaini (a.s), bayan tattaunawa da kwamandojinsa, ya amince da wannan bukata, shi kuwa Abbas ya koma ya gaya wa Husaini (a.s) abin da ya faru. ____________ (1)- Kamar na sama, shafi na 33. (2)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 227, Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 52, don haka shahadar Imam Husain (a.s) ta kasance ne ranar Juma'a ba ranar Litinin ba kamar yadda da dama suka tafi a kai. (3)- Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafi na 319, Maktal al-Husain (a.s) na Ibn Dawus, shafi na 33, haka nan kuma Shaikh Mufid cikin Al-Irshad, shafi na 232 ya ambato cewa, daga Aliyu bn Husain al-Sajjad (a.s) cewa Imam Husain (a.s) ya kasance yana rera wannan waka daren goma ga watan Muharram. (4)- Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafi na 319, Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 58 da kuma Maktal al-Husain (a.s) na Ibn Dawus, shafi na 34. (5)- Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 52, 53. (6)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 229 da kuma Tarikh al-Ummam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafi na 314.
from Blogger https://ift.tt/2QhewXp
0 notes
dakeake-blog · 6 years ago
Text
DILKAR LALLE
DAKE AKE🌹
  *ADO DA KWALLIYA SAI MACE GANGARIYA*
  *DILKAR LALLE*
  *Lalle*
*Madarar turare*
  Zaki samu ainihin ganyen lalle, ki daka da kanki saboda wanda ake siyarwa a kasuwa akan yi gauraye d mataccen ganyen.
  Ki samu ruwa ki zuba garin a ciki ki dora a wuta, tafasa daya sai ki sauke.
  Ki barshi ya huce, sai ki kawo madarar turarenki masu qamshi kamar kala 2 ki zuba.
  Da kin gama wanka sai…
View On WordPress
0 notes
isiyasy · 5 years ago
Text
WANI BANGARE NA GWAGWARMAYAR HUSAINI (A.S)
Tumblr media
Bayan kisan gillan da aka yi wa Halifa na uku, Usman bn Affan, al'umman musulmi sun zabi Imam Ali (a.s) a matsayin halifa, inda suka mika masa ragamar gudanar da mulki da kuma gwamnati. To amma sai Mu'awiyya bn Abu Sufyan ya ki yarda ya mika mubaya'arsa ga halifan da al'umman suka zaba (Imam Ali) yana mai zame kansa da kuma bayyanar da kansa a matsayin halifan Sham wanda da man shi ne gwamnan wannan gari a lokacin halifanci Usman bn Affan. Hakika duk wanda ya karanci tarihin siyasa na wancan lokacin mai tsananin wahala cikin tarihin Musu-lunci, zai ga cewa Imam Ali (a.s) ya fuskanci wasu manyan barazana guda uku na siyasa, su ne kuwa: 1- Barazanar Umayyawa karkashin jagoranci Mu'awiyya bn Abi Sufyan. 2- Barazanar Khawarijawa wadanda suka fice daga cikin rundunar Imam Ali (a.s) da kuma yi masa tawaye. 3- Barazanar A'isha(1), Dalha da kuma Zubair bn Awwam. Bayan wani lokaci na yaki da kuma cacan baki tsakanin Imam Ali (a.s) da wadannan kungiyoyi da jam'iyyu na siyasa, Imam Ali (a.s) ya sami nasarar gamawa da barazana kungiyar A'isha, Dalha da kuma Zubair a yakin nan da aka fi sani da "Yakin Jamal" (Rakumi) wanda ya abku a garin Basra. Haka nan kuma ya sami nasara a kan Mu'awiyya a "Yakin Siffin", lamarin da ya kare ta hanyar yin sulhu amma Imam Ali (a.s) ya ki yarda da hakan bayan da ya fahimci cewa wannan sulhun ba wani abu ba ne face kawai yaudara ta siyasa da Mu'awiyya da 'yan koransa suka tsara, lamarin da ya haifar da kungiyar Khawarijawa da kuma ballewarsu daga bangaren Imam Ali. Daga baya kuma suka yi fito-na-fito tsakaninsu a "Yakin Nahrawan", inda Imam Ali (a.s) ya sami nasarar tarwatsa su. A daidai lokacin da ake cikin wannan rikici na siyasa da kuma zubar da jini, Khawarijawa, wadanda daman tuni sun bayyanar da adawa da kuma tawayensu ga Shugaban Musulmi Imam Ali (a.s), sun tsara wani tsari na kashe Mu'awiyya, Amr bn al-Aas da kuma Imam Ali bn Abi Talib (a.s), ta haka ne duniya za ta rasa daya daga cikin mafiya daukakan mutanenta, madaukin tutar tabbatarta, ma'abucin ilmi, jihadi da ayyuka na kwarai, wato Imam Ali bn Abi Talib (a.s). Wanda kuwa ya dauki nauyi gudanar da wannan mummunan aiki da kuma yin kafar ungulu wa tarihin dan'Adam shi ne Abdul-Rahman bn Muljam, inda ya kashe Amirul Muminina Ali bn Abi Talib (a.s) ta hanyar sararsa da takobi mai guba a kansa a yayin da yake sallar Asuba a masallacin Kufa ranar 19 ga watan Ramalana shekara ta 40 bayan hijira, kana kuma ya yi shahada a ranar 21 ga wannan watan na Ramalana. Da wannan shahada ta Amirul Muminina Ali (a.s), wanda ya kasance shugaban gwamnati, jihadi da kuma siyasa, mutum mai riko da gaskiya da akida, wanda ya ba da dukkan karfinsa wajen tabbatar da adalci da daidaituwa, wanda ba ya taba yin sassauci a kan gaskiya ko kuma yin sako-sako da akida, al'amurra daban-daban na siyasa da kuma sabbin abubuwa suka kunno kai, haka nan kuma aka haifar da wani sabon yanayi cikin tarihi. An jujjuya al'amurra, an dagula al'amurran siyasa da zamantakewar al'umma, an shigar da wasu al'amurran da ba su dace ba cikin lamarin halifanci, haka nan kuma Mu'awiyya ya ci gaba da fadada mulkinsa da ikon da ya ke da shi. Duk da irin imanin da al'umman musulmi suke da shi kan girma da daukakar Imam Hasan (a.s) da kuma irin tsarki da matsayinsa na siyasa da zamantakewa wanda babu wanda ya mallake su a wancan lokacin, hakan nan kuma duk da irin bayyanar da matsayinsa da Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi cikin nassosi da hadisansa da kuma wasiyyar da mahaifinsa Imam Ali (a.s) ya yi da kuma mubaya'ar da al'umma suka yi masa a matsayin halifa bayan mahaifinsa, duk da wadannan abubuwa, to amma shahadar Imam Ali (a.s) ke da wuya, sai Mu'awiyya ya sanar da kansa a matsayin halifan musulmi. Bayan haka kuma ya rubuta wa Imam Hasan (a.s) yana bukatarsa da ya sauka daga matsayin da al'umma suka dora masa na jagorantarsu, yana mai masa barazanar yakansa matukar ya ki yarda da hakan. Hakika tarihi ya kiyaye mana dukkan wadannan wasiku guda biyu, wato wasikar da Mu'awiyya ya rubuta wa Imam Hasan bn Ali (a.s) da kuma amsar da shi Imam Hasan din ya rubuta masa. Ga wasikar da Mu'awiyyan ya rubuta wa Imam Hasan (a.s) yana bukatarsa da ya saukar daga karagar halifancin musulmi: "Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai. Bayan haka, hakika Allah Madaukakin Sarki Yana yi da bayinSa yadda Ya so, kuma babu wanda ya isa ya yi jayayya da hukumcinSa, kuma Shi mai saurin yin hisabi ne. Ka yi hankali kada mutuwarka ta kasance a hannun mafi muguntar mutane, kuma ka bar tunanin za ka samu rauni a tattare da mu. Lalle matukar dai ka bar abin da kake kai, kana kuma ka yi min mubaya'a, to lalle zan cika maka alkawarin da na yi maka kuma zan ba ka abin da ka bukata. Kuma zan kasance kamar yadda A'sha bn Kais bn Tha'alabah ya bayyana (cikin baitoci): Idan wani ya baka amanar wani abu, Ka mayar masa, bayan mutuwarka za a kira ka amini. Kada ka yi hassada wa shugabanka in yana cikin wadata, Kada ka kaurace masa, idan ya talauce. Bayana halifanci zai kasance naka ne, don kuwa kai ne kafi dacewa da shi daga dukkan mutane. Wassalam". Daga nan sai Imam Hasan ya rubuta masa amsa yana mai cewa: "Bayan haka: wasikarka ta iso hannuna kana mai ambaton abin da ka ambata a cikinta. Ban ki amsa maka wasikar taka ba ne don kada in kasance ban maka adalci ba, Allah Ya tsare ni daga hakan. Ina kiranka da bin gaskiya za ka gano cewa ni ma'abucinta ne, lalle zan dauki alhakin abin da na fadi idan har karya ne, Wassalam(2)". Imam Hasan (a.s) dai bai amince da wannan bukata ta Mu'awiyya ba na ya sauka daga halifancin da al'umma suka dora masa ba, face ma dai yana ganin wajibcin ci gaba da rike wannan nauyi na jagorantar al'umma. Don haka sai ya fara shirya dakaru don yakan Mu'awiyya da kuma kare Musulunci daga sharrinsa, to sai dai kuma alamun nasara suna komawa ne ga bangaren Mu'awiyyan saboda ha'incin da wasu kwamandojin Imam Hasan din suka nuna saboda sayensu da Mu'awiyyan ya yi da dai sauran dalilai. Don haka Imam Hasan (a.s) ya kasance ba shi da wata mafita face ya yi sulhu da Mu'awiyya don kare zubar da jinin musulmi da kuma kare Musulunci wanda yake fuskantar barazanar bakin haure (daular Rum) da abokan gaba wadanda da man suke jiran faruwar hakan. Don haka sai ya yi sulhu na wani lokaci don ko yanayi zai dawo yadda ya kamata bayan mutuwar Mu'awiyya don ya samu damar yin gyara da kuma dawo da al'amurran yadda suke. Ta haka ne Imam Hasan (a.s) ya bar wannan hakki nasa, ya yi sulhu da Mu'awiyya kan wasu lamurra kamar yadda tarihi ya ruwaito mana su: 1- Wannan shi ne sulhun da aka yi tsakanin Hasan bn Ali bn Abi Talib da kuma Mu'awiyya bn Abi Sufyan, kan cewa Hasan bn Ali zai bar halifancin musulmi ga Mu'awiyya bisa sharadin zai yi aiki da littafin Allah da kuma sunnar Manzon Allah da kuma tafarkin shiryayyun halifofi, kuma cewa Mu'awiyya ba zai nada wani a matsayin halifa ba bayansa(3). 2- Kan cewa Hasan shi ne zai kasance halifa bayansa (Mu'awiyya)(4), idan kuma wani abu ya same shi to dan'uwansa Husaini ne zai kasance halifan(5). 3- Kan cewa (Mu'awiyya) ba zai bukaci wani abu akan mutanen Madina, Hijaz da Iraki kan yadda suka kasance lokacin halifanci Imam Ali ba(6). 4- Kuma jami'an gwamnatin Mu'awiyyan ba za su la'anci Imam Ali a kan mimbarorinsu ba haka nan kuma ba za su fadi muggan kalmomi akansa ba da kuma yin kunuti(7) a kansa ba. 5- Mutane za su kasance cikin aminci a duk inda suke(8). 6- Mu'awiyya ba shi da ikon sarrafa kudin da ke cikin Baitul Malin birnin Kufa, ikon sarrafasu yana hannun Imam Hasan (a.s) ne. 7- Mu'awiyya ba zai yi kokarin cutar da Hasan da Husaini ba, haka nan ma mabiyansu. Haka nan aka rubuta wannan sulhu kuma dukkan bangarorin biyu suka sanya hannu da kuma yarda da shi. To amma jin kadan da gama yarda da wadannan sharud-dan sulhun (bayan da ya dawo cikin mabiyansa) sai Mu'awiyya ya tashi a gabansu yana mai cewa: "Hakika na yi alkawarin ba wa Hasan wasu abubuwa kuma na ba shi, to sai dai dukkan wadannan abubuwa a yanzu suna karkashin tafin kafata ne kuma ba zan cika ko da guda daga cikinsu ba(9)". Ta haka ne shiryayyiyar halifanci ta kawo karshe ta hanyar saukar Imam Hasan (a.s) daga halifancin, inda ya komo birnin Madina bayan halifanci na watanni shida bayan babansa Imam Ali (a.s). Daga nan sai Mu'awiyya ya shiga garin Kufa tare da sojojinsa yana mai cewa: "Ya ku mutanen Kufa! Shin kuna ganin na yake ku ne don in tilasta muku yin salla, ku ba da zakka ko kuma ku je hajji, alhali kuwa na riga da na san kuna salla, kuna fitar da zakka kana kuma kuna zuwan hajji. Lalle ni na yake ku ne don in samu iko a kanku, kuma Allah Ya ba ni hakan alhali kuwa ku ba kwa so. Haka nan duk wata dukiya ko jinin da aka zubar a yayin wannan fitina sun zama ba a bakin komai ba, haka nan kuma dukkan wani sharadi da aka tsayar za su kasance ne a karkashin kafafuna ne wadannan(10)". Hakika da wannan jawabi Mu'awiyya yana so ne ya kafa wani karfafaffen shinge na fada da Imam Hasan (a.s) kamar yadda ya zo cikin bayanin nasa cewa: "Dukkan wani sharadi da aka tsayar za su kasance ne a karkashin kafafuna ne wadannan". Hakika babu wani abin da ya saura wa Mu'awiyya in ban da wasu 'yan kwanaki, inda ya fara gudanar da wasu abubuwa da suka saba wa wannan yarjejeniya ta sulhu da aka cimma. Wadannan tsare-tsare nasa kuwa na gaba (da Imam Hasan) suna nan ne kamar haka: 1- Gudanar da ta'addanci da cutarwa ga duk wani mutum ko kuma wata al'umma da take adawa da mulkin mulukiyyar Umayyawa musamman ma mabiya Imam Ali (a.s), da kuma amfani da duk wata hanya wajen rufe bakin duk wani dan adawa. Hakika, mai karatu, na iya gane yadda wannan lamari ya kai da baci ne cikin wannan wasiyya da Mu'awiyya ya aika wa daya daga cikin kwamandojin sojojinsa. Mu'awiyya ya aika masa da cewa: "Ka kashe duk wani mutumin da ka ci karo da shi wanda ya saba wa ra'ayin da kake kai, kana kuma ka ruguza duk wani kauye da ka bi ta cikinsa, ka lalata dukiya, don kuwa lalata dukiya tana daidai da kisan gilla, kai tafi hakan ma cutar da zuciya(11)". To wannan dai shi ne tsare-tsare da kuma dabi'ar Umayyawa, kamar yadda ya zo cikin wannan nassi da ya gabata, wanda kuma tun zamanin halifanci Imam Ali (a.s) suka tsara su, sai dai kuma sun fara gudanar da su ne cikin irin wannan mummunan yanayi na zubar da jinin bayin Allah da ba su ci ba su sha ba musamman mabiya Imam Ali (a.s). Har ila ya zo cikin wata wasika da Mu'awiyya ya rubuta wa gwamnoninsa da suke dukkan jihohin da suke karkashinsa cewa: "Ku duba ku ga duk wani wanda hujja ta tabbata a kansa cewa yana son Ali da Ahlulbaitinsa, to ku cire sunansa daga cikin diwani, ku hana shi abin da ake ba wa mutane(12)". Haka nan kuma ya zo cikin wata wasikar da ya rubuta cewa: "Duk wanda kuka zarga da yin biyayya ga wadannan mutane (Ahlulbaiti) to ku yi awun gaba da shi, kana kuma ku ruguza gidansa(13)". Imam Muhammad Bakir (a.s) ya bayyana irin wannan danyen aiki da cin zali cikin wannan bayani, inda ya ke cewa: "Suna kashe 'yan shi'anmu a dukkan garuruwa, sukan gutsure hannuwa da kafafu saboda zato kawai. Akan sanya duk wanda aka zarga da sonmu da komawa gare mu cikin gidajen yari, ko kuma a kwace dukiyarsa, ko kuma a ruguza gidansa, haka lamari ya ci gaba da baci da kuma karuwa har lokacin Ubaidullah bn Ziyad wanda ya kashe Imam Husaini (a.s)(14)". Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu cikin wannan zalunci da ayyukan ta'addanci mai tada hankali har da wasu sahabbai tsarkaka, irin su: Hijr bn Adi da al'ummarsa, Rashid al-Hijri, Amru bn al-Humk al-Khuza'iy, Awfa bn Husn da dai sauransu masu yawa. Mai son karin bayani kan irin wannan danyen aiki na Mu'awiyya da mutanensa sai ya koma cikin Tarihin Tabari, al-Kamil, Sharh Nahjul Balaga da dai sauransu. 2- Tattara dukiya da nufin sayan lamiran mutane don cin mutumcin gwarazan Musulunci da kuma yada bakar siyasa kaucacciya don cimma burinsu. Akwai nau'i biyu na mutanen da aka saye su a wancan lokacin don cimma wannan buri: (a)- Su ne malamai masu wa'azi da kuma tara hadisan Ma'aiki, wadanda suka ba da gagarumar gudummawa wajen kirkiro hadisan karya da kuma jingina su ga Ma'aikin Allah (s.a.w.a), wadanda babu bukatar sai mun kawo su a nan. (b)- Wasu masu fadi a cikin al'umma, wadanda ake jin tsoro tasirinsu matukar suka kirayi mutane wajen yin tawaye wa masu mulkin Umayyawa, wannan kuwa wani sanannen abu ne da aka san Mu'awiyya da shi da kuma mabiyansa. Misali kuwa shi ne makudan kudaden da Mu'awiyya ya aika wa Malik bn Hubaira al-Sukuni a matsayin cin hanci lokacin da labari ya zo masa cewa yana nuna rashin jin dadinsa da kisan gillan da Mu'awiyyan ya yi wa sahabin nan Hijr bn Adi da sahabbansa (r.a), da dai sauran irin wadannan misalai masu yawa. 3- Takunkumin tattalin arziki da kuma sauran nau'oi na cutarwa: Wannan yana daga cikin mafi muni da cutarwar tafarkin da Umayyawa suka dauka akan al'umma. Bisa la'akari da cewa wannan siyasa da muka ambata ta ginu ne akan fada da duk wani karfi da ke adawa da masu mulki na wancan lokacin (Umayyawa), don haka Mu'awiyya ya zabi mafi munin tafarki wajen takura wa mabiya Ahlulbaiti (a.s) kamar yadda tarihi ya tabbatar da haka. Daga ciki kuwa har da umarnin da ya aike wa gwamnoninsa kan cewa; "Ku duba ku ga duk wani wanda hujja ta tabbata a kansa cewa yana son Ali da Ahlulbaitinsa, to ku cire sunansa daga cikin diwani, ku hana shi abin da ake ba wa mutane". Yana da kyau mu yi tunani kan wannan mummunar siyasa wacce Umayyawa suka dauka, na lalata lamirin mutane da kuma sayansu da abin duniya, wacce babu shakka ba karamin abu ba ne kuma ba wani abu ne na dan karamin lokaci ba, face dai lamari ne da ya ci gaba tsawon shekaru, wanda ya lalata yanayin siyasa da zamantakewar al'umma. 4- Lalata dabi'un al'umma da kuma haifar da ruhin kabilanci, 'yan garanci da dai sauransu tsakanin al'umma da wannan ja'irar hukuma ta Umayyawa ta yi, lamarin da ya haifar da rikice-rikice da fadace-fadace. Misalin irin rikicin da ya barke tsakanin mutanen Yaman da Madina, ko kuma rikicin da ya faru tsakanin kabilun Iraki, da kuma wutar nuna banbanci da kiyayya da ta kunno kai tsakanin musulmi larabawa da wadanda ba larabawa ba, abin da tarihi ya kira shi da sunan Al-Mawali. Lalle ana iya ganin tasirin wannan bakar siyasa cikin wakokin Al-Darami, al-Farazdak, Jarir, al-Akhtal da dai sauransu(15). 5- Kisan gillan da aka yi wa Imam Hasan (a.s) a matsayinsa na mutum mai wakiltan tsarkakakken Musulunci a duniyar musulmi. Hakika al'umma sun riga da sun fahimci kuma ma suna ji a jikinsu cewa lalle fa har ya zuwa yanzu fa jinin Imam Husaini, jikan Manzon Allah (s.a.w.a) da aka zubar a Karbala yana nan yana gudana, haka nan kuma suna jin cewa babu wani abin da zai zama kaffara na wannan jini da kuma zaluncin da aka yi wa iyalan gidan Manzo in banda daukar fansa da kuma raya wannan yunkuri na Imam Husaini (a.s). Ta haka ne aka haifar da yunkurin Al-Tawwabun, jinin Imam Husaini (a.s) shi ne ya kasance wani abin da ya motsa jigon gwamnatin Umayyawa da kuma ka da shi. 6- Nadin da Mu'awiyyan ya yi wa dansa Yazid a matsayin halifan musulmi cikin tursasawa, barazana da kuma ba da cin hancin, sabanin yarjejeniyar da aka cimma tsakaninsa da Imam Hasan (a.s) na cewa ba zai nada wani a matsayin halifa ba bayansa in ba Imam Hasan din ba ko kuma Imam Husaini (a.s) idan har Hasan din ya rasu kafin wannan lokacin. Ta haka ne Mu'awiyya ya gama tsare-tsarensa na yin karen tsaye ga dukkannin sharuddan da aka tsayar a yayin yarjejeniyarsu da Imam Hasan ta sulhu, da kuma karen tsaye ga dukkan dokoki da kuma tsare-tsare da Musulunci ya tafi a kansu bugu da kari kuma kan gudanar da mulkin danniya da baba-kere, lamarin da ya sanya tsarin siyasar Musulunci cikin mawuyacin hali da kuma lalacewa, bugu da kari kan bakanta tarihin Musulunci. Hakika wannan karen tsaye wa dokokin Musulunci da Umayyawan suka tsara ma ya dada fitowa fili ne lokacin da Mu'awiyya ya nada dansa Yazid, wanda aka san shi da wargi da kuma aikata dukkanin sabo, a matsayin jagoran al'umman musulmi. Babu shakka, mika wa Yazid ragamar mulkin al'ummar musulmi da kuma tsara mata tafarkin da za ta bi, yana nufin ruguza kasantuwan Musulunci ne da kuma dokokinsa a aikace da kuma kowama zuwa ga jahiliyya, amma a wani tufafi na daban. Don kuwa shi wannan Yazid din - kamar yadda tarihi ya tabbatar - mutum ne maras dabi'u na kwarai, wanda kuma ba shi da wata masaniya kan dokokin Musulunci, wanda ya gudanar da dukkan rayuwarsa cikin wargi da munanan aiki na jahiliyya da ko kare ba zai iya cinsu ba saboda muni. Don haka ba abin mamaki ba ne idan Yazid ya yi kokarin lalata yanayin tarbiyyan al'ummar musulmi da Musulunci ya koyar da su. Hakika tarihi ya tabbatar mana da yadda wannan lalataccen da na Mu'awiyya yake gudanar da rayuwarsa a Sham, rayuwar da ke cike da wargi, caca, shan giya, wasa da birrai, neman mata, sauraron kide-kide da raye-raye da dai sauran nau'oi na sabon Allah(16). Yayin da yake ishara da irin wadannan halaye na Yazid, Al-Baladhuri yana cewa: "Yazid ya kasance yana da wani biri da yake tare da shi, ya kan kira shi da Abu Kais. Ya kasance yakan ce: Wannan dattijo ne daga cikin dattijan Bani Isra'ila da aka shafe saboda laifin da ya yi". Ya kasance ya kan sayar da shi wani nau'i na giya yana dariya kan yadda yake ni yayin da ya bugu...(17).". Haka nan Ibn Athir ma yana cewa: "An ruwaito cewa Yazid mutum ne da ya shahara da kide-kide, mashayin giya, mai wasa da maza, birrai da karnuka….babu yadda za a yi garin Allah ya waye face yana cikin maye...(18)". Al-Mas'udi ma cewa yake: "Yazid ya kasance ma'abucin kide-kide, wasa da dabbobin da ake farauta da su, karnuka da birrai, haka nan kuma mutum ne da ya shahara da shan giya….. "Ayyukan fasikancin da Yazid yake aikatawa ya yi tasiri akan abokai da da masu masa hidima, a lokacinsa ne kide-kide suka shiga Makka da Madina, haka nan kuma mutane suka dinga bayyana shan giya a fili. Ya kasance yana da wani biri da ya sa masa suna Abu Kais, ya kan tawo da shi fada, ya sanya masa mimbari, ya kan dora shi a kan doki ana yin gasa da shi. Ya kan sanya wa wannan biri alkyabba da aka yi ta da hariri, sannan kuma ya sanya masa hula wacce aka yi ta da zaren hariri mai launuka daban-daban....(19)". Hakika wannan lamarin dai bai tsaya a nan ba, kamar yadda kuma yakin da Umayyawa suke yi da Ahlulbaiti (a.s) wanda ya samo asali tun farkon Musulunci bai kare ba. Lalle Imam Hasan da Husaini (a.s) sun kauce wa fagen siyasa a aikace, to amma duk da haka Mu'awiyya da mabiyansa sun ci gaba da cin mutumcin Ahlulbaiti da mabiyansu har lokacin da Imam Hasan (a.s) ya yi shahada kana kuma al'umma suka juya kan Imam Husaini (a.s) da kuma yi masa mubaya'a don ya jagoranci ganin bayan wannan lalatacciyar hukuma ta Umayyawa. Mu'awiyya dai yana da wani abu a zuciyarsa, wannan abu kuwa shi ne yana son dora dansa Yazid a matsayin halifan musulmi a bayansa kana kuma ya karba masa mubaya'ar al'umma da kansa sabanin abin da shari'ar Musulunci ta tsayar wajen zaban halifa. Lalle wannan kuduri na Mu'awiyya ya tada hankulan al'umman musulmi musamman ma sanannu daga cikinsu irinsu Imam Husaini (a.s), Abdurrahman bn Abubakar, Abdullahi bn Zubair, Abudllahi bn Umar da dai sauran sanannu mutanen wancan lokacin. Babu shakka tarihi ya nakalto mana irin nuna rashin amincewa da aka nuna da wannan matsaya, ga kadan daga ciki: "A shekara ta hamsin bayan hijira, musulmi sun sami nasarar kame Kuhistan, don haka a lokacin sai Mu'awiyya ya kirayi mutane Sham da su yi mubaya'a wa Yazid a matsayin halifa bayansa, inda suka amsa masa suka yi mubaya'ar. Don haka Mu'awiyya ya zamanto mutum na farko da ya nada dansa halifa, kana kuma na farko da ya nada halifan da zai gaje shi yana cikin koshin lafiyarsa. Daga nan sai ya aika da wasika zuwa ga Marwan wanda ya ke shi ne gwamnan Madina kan ya karbi bai'ar mutane ga Yazid a maimakonsa, yana mai ce masa: "Amirul Muminina ya yanke zai nada dansa Yazid a matsayin jagoranku (halifa) daidai da sunnar Abubakar da Umar", nan take sai Abdurrahman bn Abubakar al-Siddik ya mike ya ce: A'a hakan sunnar Khosro da Kaisar ne dai, don kuwa Abubakar da Umar ba su nada 'ya'yayensu halifa ba, ko kuma daya daga cikin mutanen gidansu ma ba". Haka nan kuma a shekara ta hamsin da daya, Mu'awiyya ya yi aikin hajji, inda ya karbi bai'a wa dansa Yazid. Daga nan sai ya aika a kira masa Ibn Umar yana mai ce masa: "Ya Ibn Umar, ka kasance kana gaya min cewa ba ka son ka kwana alhali ba kana karkashin ikon wani shugaba ba, don haka ina gargadinka da kada ka haifar da rarrabuwa ko kuma yada fasadi tsakanin al'umma". Jin haka sai Ibn Umar ya gode wa Allah ya ce: "Bayan haka, hakika kafinka an yi halifofi wadanda suke da 'ya'yaye, kuma danka bai fi nasu 'ya'yan ba, amma ba su wa 'ya'yansu abin da ka yi wa naka dan ba (nada shi halifa), to amma su sun zaba wa musulmi ne abin da yafi musu alheri. Ka gargade ni da kada in shuka tsiron rarrabuwa tsakanin musulmi, lalle ba zan yi haka ba, don ni na kasance daya daga cikin musulmin, idan har sun tafi a kan wani abu ai ni ma daga cikinsu nake (zan yarda da shi)". Sai Mu'awiyya ya ce masa, Allah Ya yi maka rahama. Daga nan sai Ibn Umar ya fita ya yi tafiyarsa. Daga nan kuma sai ya aika a kira masa Ibn Abubakar, ko da ya iso sai ya fara gaya masa wannan bukata tasa ta nada dansa a matsayin halifa, sai Ibn Abubakar ya katse shi yana mai cewa: "Wallahi ba za mu taba yarda da haka ba, don Allah, ka mayar da wannan al'amari tsakanin mutane su zabi wanda suke so, ko kuma mu tilasta maka yin haka", sai ya fice. Sai Mu'awiyya ya ce: Ya Allah! Ka isar min a kansa da abin da Ka so, sai ya ci gaba da cewa: "Ya kai wannan kada ka gaya wa mutanen Sham (Siriya) abin da ya faru, don ina tsoron za su fada maka, ka hakura har sai da maraice lokacin da zan gaya musu cewa ka yi mana bai'a, daga nan sai ka yi duk abin da kake son yi". Sai ya aika a kira masa Ibn Zubair, ya ce masa: "Ya Ibn Zubair, hakika kai ba ka kasance ba face kamar dila mai wayo, ka shiga nan ka fita ta can, kai ne ka sanya wadannan mutane biyu suka canza ra'ayinsu. Sai Ibn Zubair ya ce: " Idan har ba ka son shugaban-cin ne to ka sauka, idan har muka yi mubaya'a wa danka, to a cikinku ku biyun wane ne za mu saurara da kuma yi masa da'a? Don kuwa ba abu ne mai yiyuwa ba mu yi mubaya'a gare ku ku biyun". Sai ya tashi ya fita: Sai Mu'awiyya ya hau kan mimbari, ya gode da kuma tsarkake Ubangiji sai ya ce: "Hakika maganar da mutane suke yi mai cutarwa ta iso gare mu, suna cewa Ibn Umar, Ibn Abubakar da Ibn Zubair ba za su taba yin mubaya'a wa Yazid ba, to amma tuni sun riga da sun saurara masa kana kuma sun mika mubaya'arsu gare shi". Sai mutanen Sham suka ce: "Wallahi ba za mu amince da hakan fa face sai sun yi mubaya'ar a gaban mutane, in ba haka ba kuwa mu sare kawukansu". Sai ya ce: "Godiya ta tabbata ga Allah! Kan yadda mutane suka gaggauta nufan Kuraishawa da sharri, kada in sake jin wannan zance daga bakinku daga yau". Sai ya sauka. Sai mutane suka fara cewa: "A'a ashe Ibn Umar, Ibn Abubakar da Ibn Zubair sun yi mubaya'a wa Yazid su kuma suka ce wa mutane: wallahi ba mu yi hakan ba, mutanen kuma suka ce: a'a kun yi mana. Daga nan sai Mu'awiyya ya tashi ya tafi(20)". Ta haka ne al'umma ta fada cikin wannan tsaka mai wuya na tarihin rayuwarta, ta kasance babu komai a gabanta face zabi biyu: Ko dai ta ki amincewa da wannan abu da ke fuskan-tarta koma dai me ya tafasa ya kone, ko kuma ta amince da wannan wulakanci da jifa da abin da Musulunci ya tafi a kai. To ya ya lamarin ya kasance? ____________ (1)- A'isha dai ita ce matar Annabi (s.a.w.a) kana kuma 'ya ta ke ga halifa na biyu Abubakar bn Abi Kahafa. (2)- Makatil al-Talibin na Abul Faraj al-Isfahani, shafi na 59. (3)- Al-Fusul al-Muhimma na Ibn Sabbagh al-Maliki, shafi na 163. (4)- Tarikh al-Khulafa' na Jalaluddeen Suyuti, shafi na 191. (5)- Sulh al-Hasan na Shaikh Radhi Al' Yasin, shafi na 260, yana mai nakaltowa daga littafin Umdatul Talib. (6)- Tarikh al-Khulafa' na Jalaluddeen Suyuti, shafi na 191. (7)- Wato ba za su dinga yin munanan addu'oi a kansa ba, saboda a wancan lokaci Mu'awiyya da jami'ansa sun kasance suna zagi da fadan munanan kalmomi ga Amirul Muminina Ali (a.s) a gaban jama'a bayan an idar da salla. Haka nan kuma sun kasance sukan ba da kyauta ga duk wanda yake zagin Imam Alin (a.s). Dubi Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 3, shafi na 414 da kuma 472, da kuma Sharh Nahjul Balagah na Ibn Abil Hadid, juzu'i na 3, shafi na 56-63. (8)- Al-Fusul al-Muhimma na Ibn Sabbagh al-Maliki, shafi na 163. (9)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 191. (10)- Sharh Nahjul Balagah Ibn Abil Hadid, juzu'i na 16, shafi na 15. (11)- Kamar na sama, juzu'i na 2, shafi na 86. (12)- Kamar na sama, juzu'i na 11, shafi na 45. (13)- Kamar na sama. (14)- Kamar na sama, shafi na 43. (15)- Thauratul Husainiyya na Muhammad Mahdi Shamsuddin, shafi na 61 zuwa sama. (16)- Al-Imam Husain na Abdullah al-Alayili, shafi na 345. (17)-Ansab al-Ashraf na Baladhuri, juzu'i na 4, shafi na 1 da 2. (18)- Al-Bidaya wan Nihaya na Ibn Athir, juzu'i na 8, shafi na 236. (19)- Muruj al-Zahab wa Ma'adin al-Jawhar na Al-Mas'udi, juzu'i na 3, shafi na 67 da 68. (20)- Tarikh al-Khulafa' na Jalaluddeen al-Suyuti, shafi na 196 da kuma 197.
from Blogger https://ift.tt/2LAx3Kf
0 notes
isiyasy · 5 years ago
Quote
Ruhin jihadi da gwagwarmaya a tafarkin Allah yana da tushe na akida da tarbiyya da kuma ta zamantakewa da siyasa duk tsawon rayuwar Imam Khumaini. Imam ya fara gwagwarmayarsa ne tun lokacin samartaka, kuma ya ci gaba da hakan a bangarori daban-daban na kyautata ruhi a bangare guda, a bangare guda kuma kan yanayi na siyasa da zamantakewar al'ummar Iran da sauran al'ummomin kasashen musulmi. Rikicin da ya faru a shekarun 1340-1341 hijira shamsiyya (1961-1962) kan (zaben) kananan hukumomi ya kasance babbar dama ga Imam wajen jagorantar yunkurin al’umma. Don haka, ana iya cewa, yunkurin gama-gari na malamai da al'ummar Iran na 15 ga watan Khordad 1342 (5 Yunin 1963) ya kebantu da wasu siffofi guda biyu su ne kuwa jagorancin Imam Khumaini da kuma riko da Musulunci, wanda hakan ya zamanto matakin farko na yunkurin al'ummar Iran wanda daga baya aka fi saninsa da sunan "Juyin Juya Halin Musulunci".Yayin da yake bayani kan abubuwan da ya tuna dangane da yakin duniya na farko, duk da cewa lokacin da aka yi yakin yana da shekaru 12 ne a duniya, Imam Khumaini yana cewa: "Lalle ina iya tuna abubuwan da suka faru a yakukuwan duniya guda biyu…a lokacin ina karami ne amma dai na kan je makaranta kuma ina ganin sojojin tarayyar Sobiyeti a sansanin da muke da shi a nan (garin) Khumain. A yakin duniya na farko a wasu lokuta akan kai mana hare-hare ma". A wani waje na daban Imam Khumaini ya kasance ya kan ambato sunayen wasu daga cikin ashararan da suke fakewa da hukuma wajen kai hare-hare da sace kayayyakin al'umma, inda yake cewa: "Tun ina karami nake cikin yaki….muna cikin mamayan Zulkawa da kai hare-haren Rajab'ali ne duk da cewa mu ma muna da bindiga. Mu kan je kai dauki alhali a lokacin ina cikin shekarun samartaka na ne. Mun kasance mu kan gina ramukan fakewa a inda muke… mu kan shiga cikin wadannan ramuka muna fada da wadannan ashararai da suke son kawo hari da mamaye mu".A bisa wasu hujjoji na tarihi an tabbatar da cewa gwamnatin Birtaniyya ne ta shirya da kuma goyon bayan juyin mulkin da Ridha Khan ya yi a ranar 3 ga watan Esfand 1299 hijira shamsiyya (1920). Duk da cewa an kawo karshen mulkin Kajariyawa da kuma rage karfin mulkin ha’inai da ashararai, to amma dai ya haifar da wani tsari na kama-karya da wasu ‘yan tsiraru ke mulkan mutanen wata kasa da tsara musu makoma, inda 'yan gidan sarautan Pahlawi suka maye gurbin ashararai.A irin wannan hali nea, duk da irin musgunawa malamai da gwamnatin lokacin da 'yan amshin shatan Birtaniyya da wasu 'yan boko da aka saya suke yi, amma (malaman) sun tsaya kyam wajen kare Musulunci. A wannan lokaci, bisa gayyatar da malaman Kum suka yi masa, Ayatullah Hajj Shaikh Abdulkarim Ha'iri ya yi hijira daga garin Arak zuwa Kum. Bayan wani lokaci kuma sai Imam Khumaini, sakamakon irin kokarin da yake da shi da kuma gama karatunsa na share fage a garuruwan Arak da Khumain, yayi hijira zuwa birnin Kum don ba da tasa gudummawar wajen karfafa sabuwar makarantar Hawzar garin. Daga baya ya yi fice wajen karantar da ilmummukan fikihu, falsafa da sufanci.Rasuwar Ayatullah Ha'iri a ranar 10 ga Bahman 1315 hijira shamsiyya (10 ga watan Janairun 1937) ta sanya makarantar Hawzar Kum cikin hatsarin rugujewa, sai dai wasu malamai masu sadaukarwa sun ba da ta su gudummawar wajen ganin hakan ba ta faru ba. Cikin shekaru takwas din da aka yi, kula da makarantar ta kasance ne karkashin kulawar manyan malamai irinsu Ayatullah Sayyid Muhammad Hujjat, Sayyid Sadraddin Sadr da Sayyid Muhammad Taki Khunsari. A daidai wannan lokaci, musamman bayan faduwar gwamnatin Ridha Khan, yanayi yayi kyau da ya ba da dama wajen sake samar da cibiyar marja'iyya. A lokacin babu wanda ya dace ya maye gurbin Ayatullah Ha'iri da kuma kare makarantar Hawza daga faduwa kamar Ayatullah Burujerdi. Wannan hukumci na nada Ayatullah Burujerdi ya samu goyon bayan daliban Ayatullah Ha'iri ciki kuwa har da Imam Khumaini. A daidai wannan lokaci Imam da kansa ya yi ta kokari wajen ganin Ayatullah Burujerdi ya dawo garin Kum don rike shugabancin makarantar garin.Imam Khumaini, sanadiyyar irin sanya ido kan yanayin da al'umma da makarantar Hawzar take ciki, da kuma karance-karance litattafa, jaridu da mujallu da kuma ziyarar da yake kai wa Tehran da ganawa da manyan malamai irin su Ayatullah Mudarris, ya fahimci cewa hanya guda ta magance mummunan yanayin da ake ciki bayan rashin nasarar yunkurin tsarin mulki musamman bayan darewar mulkin Ridha Khan ita ce taka tsantsan din makarantar Hawza, da tabbatar da alaka ta ruhi tsakanin malamai da al'umma.A wannan kokari da Imam yake yi na karfafa makarantar Hawza ne ya sa a shekarar 1328 (1949) bisa goyon bayan Ayatullah Murtadha Ha'iri suka tsara wani shiri na kawo canji inda suka gabatar da shi ga Ayatullah Burujerdi. Wannan shiri ya fuskanci amincewar daliban Imam da sauran daliban da suke da wayewa.Sai dai ita gwamnatin ta yi kuskure, saboda a ranar 16 Mehr 1341 (8 ga Oktoba 1962) majalisar hukumar Asadullah Alam ta amince da cire wasu dokokin karamar majalisar kasa, kamar dokar da ta shardanta cewa dole ne dan takara ya zamanto musulmi, rantsuwa da Alkur'ani mai girma, sharadin mazantaka ga 'yan takara da masu jefa kuri'a. Babu makawa akwai wata boyayyiyar manufa cikin amincewa da barin mata su kada kuri'a (da hukumar ta yi), kamar yadda cire sharadin Musulunci da mazantaka shi ma da wata manufa aka yi shi, ita ce kuwa shigar da 'yan Baha'iyya cikin al'amurran gudanarwa da ba su manyan mukamai cikin gwamnati.Kamar yadda muka nuna a baya, taimako da goyon bayan haramtacciyar kasar Isra'ila da fadada alakar Iran da ita na daga cikin sharuddan da Amurka ta kafa wa gwamnatin Shah matukar tana son goyon bayanta. Don haka ne ya zamanto dole a bar 'yan kungiyar Baha'iyya ta 'yan mulkin mallaka su kame manyan bangarorin gwamnati don cika wannan sharadi. Jin kadan bayan watsa wannan labari, Imam Khumaini da wasu manyan malaman biranen Kum da Tehran, bayan wata tattaunawa, suka sanar da rashin amincewarsu da dokar.Imam Khumaini ya ba da gagarumar gudummawa wajen fallasa asiri da manufofin gwamnatin Shah da kuma bayyana hakikanin nauyin da ya hau kan malamai da makarantun Hawza cikin halin da ake ciki. Hakan ne ya sa aka samu wasu malamai suka aike da wasu wasiku na nuna rashin amincewa ga Shah da priminista Alam, hakan ya faranta wa al'umma rai. Amma wasikun da Imam ya aike wa Shah da priministansa sun fi na sauran malaman tsauri da kuma jan kunne. A cikin daya daga cikin irin wadannan wasiku, Imam yana cewa: "Ina sake muku nasiha da tsoron Allah da kuma bin tsarin mulki, sannan ku guji saba wa Alkur'ani da dokokin malamai da shuwagabannin musulmi da kuma watsi da dokokin kasa; kada ku sanya kasa cikin hatsari da gangan, idan kuwa ba haka ba, malaman Musulunci ba za su daina yin maganganu a kanku ba".Haka dai wannan batu na dokar kananan hukumomi ya kasance nasara ga al'umma kana kuma lamari mai muhimmanci gare su, musamman ma ganin cewa sun fahimci siffofin mutumin da ya cancanci ya jagoranci al'ummar musulmi. Duk da wannan rashin nasara da Shah ya fuskanta, to amma Amurka ta ci gaba da matsa masa lamba wajen ci gaba da canje-canjen da zai ba ta damar cimma manufofinta. Don haka Shah a watan Dey 1341 (Janairun 1962) ya gabatar da jiga-jigan shirinsa na canji guda shida da kuma bukatar a gudanar da jin ra'ayin al'umma kansu.Har ila yau Imam Khumaini ya sake bukatar maraja'ai da manyan malaman garin Kum da su zauna don tattaunawa kan halin da ake ciki da kuma yiyuwar sake kaddamar da wani sabon yunkuri.A ci gaba da goyon bayan da mutane suke nuna wa Imam, al'umma sun kaurace wa bukukuwan "Nuruz" (sabuwar shekara) don nuna rashin amincewa da ayyukan gwamnati. A cikin sanarwar da Imam ya fitar kan hakan, ya ambaci "Farin Yunkuri" (White Rebolution) na Shah da sunan "Bakin Yunkuri" (Black Rebolution), sannan kuma ya tona asirin manufar Shah ta biyan bukatun Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila. A bangare guda kuma, Shah, wanda ya tabbatar wa Amurkawa cewa al'ummar Iran sun amince da canje-canjen da yake son yi don cimma manufofin Amurka da ya ba shi sunan "White Rebolution", ya fahimci cewa rashin amincewar da malamai suke yi gare shi zai haifar masa da matsaloli masu girman gaske.A cikin hudubobi da jawaban da ya dinga yi a gaban jama'a, Imam Khumaini ya dora alhakin wannan zalunci a kan Shah, kamar yadda kuma yake kiransa da dan koran haramtacciyar kasar Isra'ila da kiran al'umma da su yi masa bore. A wani jawabi da ya gabatar a ranar 12 ga Farbardin 1342 (1 Aprilu 1963) Imam ya yi Allah wadai da shirun da malamai suka yi a garuruwan Kum, Najaf da sauran garuruwan musulmi kan wannan danyen aiki na gwamnatin Shah, yana mai cewa: "Lalle a yau shiru yana nufin nuna goyon baya ga wannan hukuma ta zalunci". Washegari kuma wato ranar 13 ga Farbardin 1342 (2 Aprilu 1963) Imam ya fitar da sananniyar sanarwar nan tasa mai suna "Kaunar Shah Wasoso Ne".Haka nan idan ana son fahimtar irin tasirin da kalaman Imam suke da shi a zukatan masu sauraronsa da har suke iya fita su ba da rayukansu, to dole ne a dubi asali da kiran nasa yake da shi da kuma irin gaskiya ta hakika da ke tare shi.Shekarar 1342 hijira shamsiyya (1963) ta fara ne da kin fitowar da al'umma suka yi don bukukuwan "Nurooz" (sabuwar shekara) sakamakon kiran da malamai suka yi, da kuma zubar da jinin mutanen da ba su ci ba su sha ba a makarantar Fa'iziyya da ke birnin Kum. A bangare guda, Shah ya dage sai ya aiwatar da shirinsa na kawo canjin da Amurka ta ke bukata, a bangare guda kuma Imam Khumaini ya dage wajen wayar da kan al'umma wajen tsayawa da fuskantar tsoma bakin Amurka cikin al'amurran cikin gidan Iran da kuma ha'incin Shah.A ranar 14 ga watan Farbardin 1342 (1963), Ayatullah al-Uzma Hakim daga garin Najaf ya aike wa wasu manyan malamai da maraja'ai na Iran da wasika yana kiransu da yin hijira ta gaba daya zuwa garin Najaf. Wannan kira dai an yi ta ne da nufin kiyaye rayuwar malamai da makarantar Hawza.Imam ya yi kunnen uwar shegu da wannan barazana, don haka sai ya aikewa Ayatullah Hakim amsar wasikar da ya rubuto yana mai ce masa yana ganin babu wata maslaha ta Musulunci cikin yin hijira ta gaba daya da barin Hawzar Kum haka nan.Cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 12 ga watan Farbardin 1342 (22 Aprilu 1963) a lokacin bukukuwan kwanaki arba'in na shahadar (daliban) Fa'iziyya, Imam Khumaini ya jaddada goyon bayan malamai da al'ummar Iran ga jagororin kasashen musulmi da na larabawa wajen fuskantar haramtacciyar kasar Isra'ila, kamar yadda kuma yayi Allah wadai da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Sarki Muhammad Ridha Pahlawi da haramtacciyar kasar Isra'ila.
http://www.5five-stars.com.ng/2020/02/imam-khumaini-ra-fagen-gwagwarmaya.html
0 notes
isiyasy · 5 years ago
Quote
A lokacin da ya cika shekaru ashirin da biyar da haihuwa sai ya tafi kasar Sham don gudanar da kasuwanci da wannan dukiya da Khadija bint Khuwailid (r.a) ta ba shi, inda kamar yadda muka bayyana a baya aka riba mai girman gaske da ba a taba samun irinta, hakan kuwa saboda albarkar da ke tattare da Annabin ne da kuma irin gaskiya da rikon amanarsa. Wadannan abubuwa dai sun faranta wa Khadijah rai kwarai da gaske da kuma kaunar Annabin. Khadija dai ta kasance daga zababbun matan Kuraishawa kuma ta fi su kudi da kyau. An haife ta ne a garin Makka kuma a can ta girma, tun a lokacin jahiliyya ana kiranta da "Tahira" (tsarkakakkiya), saboda irin kyawawan halaye da take da su a tsakankanin matayen Kuraishawa. A lokacin da ta ba wa Manzon Allah (s) dukiyarta don kula mata da su wajen kasuwanci, Khadijah ta hada shi da wani amintaccen yaronta mai suna Maisara. Irin kyawawan halayen Manzon Allah (s.a.w.a) dai sun yi tasiri wa Maisara, don haka sai ya tafi wajen Khadiza yana gaya mata irin dabi'un Muhammad (s.a.w.a) da ya gani, wannan ya sa son Manzo ya shiga zuciyarta, sai ta bukace shi da ya aureta, ya zama mijinta, alhali kuwa ta ki amincewa da manyan Kuraishawa wadanda suka zo neman auren nata. Manzo (s.a.w.a) dai ya amince da wannan bukata ta Khadijah, inda ya aureta, inda suka tabbatar da mafi kyaun kusanci da ake iya mafarki, wanda ya kyautatu da kauna, alkawari da tausayin juna; suka shata mafi kyawun sura na rayuwar auratayya mai nasara. Bari mu ji wata hikaya daga Ammar bn Yasir wanda ya kasance abokin Annabi ne tun suna yara kan yadda aure nasu ya kasance da kuma yadda aka daura shi. Ga abin da Ammar din ya ke cewa: "Ni nafi kowa sanin auren Manzon Allah (s) da Khadijah bint Khuwailid; don na kasance abokin Ma'aiki (s). Wata rana muna tafiya tare da Manzon Allah (s) tsakanin Safa da Marwa sai ga Khadijah bint Khuwailid tare da 'yar'uwarta Hala. Lokacin da suka ga Manzon Allah (s) sai Hala ta ja ni gefe ta ce min: 'Ya Ammar! Abokinka ba shi bukatuwa (da auren) Khadijah? Sai na ce: 'Wallahi ban sani ba. Sai na koma na gaya masa. Sai ya ce min: "Koma ka sa mana lokacin da za mu je mu gana da ita....sai kuwa na koma na aikata hakan (wato muka sa rana). Da ranar ta zo.....sai Manzon Allah (s) ya zo da baffanninsa karkashin jagorancin Abu Talib, inda ya karbi aurenta a hannun baffanta Amru bn Asad, kasantuwan mahaifinta, Khuwailid bn Asad ya rasu. Bayan gama bukuwan aure, sai Manzon Allah (s) ya koma gidan Khadijah da zama, wannan gida da ke da dimbin tarihi wajen ci gabantar da musulunci da kuma taimakon marasa galihu. A yayin zamansu dai, Khadijah ta kasance mace mai tsananin biyayya ga mijinta da kuma taimaka masa a dukkan bangarorin rayuwarsa, kamar yadda shi ma ya kasance hakan tare da ita. A lokacin da aka aiko shi a matsayin annabi, ita ce mace ta farko da ta fara imani da shi, ta karbi wannan kira nasa, ta ba da dukkan abin da ta mallaka don Allah da kuma ci gabantar da wannan addini. Babu makawa, dole ne Manzon Allah (s) ya saka mata saboda irin wannan hidima da ta yi masa da kuma addinin Allah, don haka ya kasance mai tsananin sonta, girmama ta lokacin tana raye da ma bayan rasuwarta (a.s), saboda matsayin da take da shi a cikin zuciyarsa. Irin wannan kulawa da matsayi na Khadijah dai ya sa Annabi (s) bai auri wata mace a lokacin tana raye ba, ko da bayan rasuwarta lokacin da ya yi aure ya kan yawan tunawa da ita, har ya kan ce ita ce matan da ya fi so cikin dukkan matansa. A'a ya ya kuwa ba zai fadi haka ba, alhali kuwa ita ce ta tsaya kyam tare da shi a lokacin yunwa, talauci da wahalhalu wadanda mushirikan Makka suka dora masa, kuma ga ta ita ce uwar dukkan 'ya'yansa, in ban da Ibrahim. An ruwaito cewa, bayan rasuwarta, a duk lokacin da ya yanka wani abin yanka, ya kan dauki wani bangare na naman ya ce: "Ku aika wannan wa kawayen Khadijah'. An ce wata rana A'isha, matar Manzon Allah, ta tambaye shi me yasa yake haka: sai ya ce mata: "Saboda ina sonta". Haka nan ma an ruwaito cewa wata mace ta zo wajen Manzon Allah (s), a lokacin yana dakin A'isha. Nan take ya tashi ya karbe ta hannu bibbiyu ya gaggauta biya mata bukatan da ta zo nema. Wannan lamari ya ba wa A'isha mamaki, sai ta tambaye shi dalilin hakan, sai ya ce mata: "Ta kasance tana zuwa gurinmu lokacin rayuwar Khadijah". Har ila yau kuma an ruwaito A'ishan dai tana cewa: 'Wata rana Manzon Allah (s) zai fita daga gida, sai ya tuna da Khadijah, ya fadi wasu kalmomi na girmamawa gare ta. To amma sai na gagara rike kai na sai na ce masa; 'Ita dai ba wani abu ba ne face tsohuwar mace, kuma a halin yanzu Allah ya musanya maka wadanda suka fi ta'. Nan take Manzon Allah (s) ya mayar mata da martani, cikin fushi yana cewa: "Lallai ba haka ba ne...lalle ban samu wadanda suka fi ta ba. Don kuwa ita ce ta yarda da annabcina a lokacin da kowa ya kyale ni. Ta ba ni dukkan dukiyarta a lokaci mafi tsanani (na bukatuwa da su). Kuma Allah Ya ba ni zuriya ta hannunta, alhali kuwa ya haramta min daga wasunta". Khadijah ta ci gaba da taimaka wa Manzon Allah (s) har lokacin da Allah Ya karbi ranta a shekara ta goma bayan wahayi, wannan rasuwa nata dai ya kasance babban abin bakin ciki ga Manzo (s), bugu da kari kuma kan rasuwar Baffansa kana kuma mai kare shi Abu Talib (a.s), don haka ma ya kira wannan shekara ta sunan Shekarar Bakin Ciki
http://www.5five-stars.com.ng/2019/11/auren-manzon-allah-s-da-khadijah-al.html
0 notes
isiyasy · 5 years ago
Quote
Rakuma dai suka kama hanyar Kufa suna dauke da iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a) a matsayin fursuno-nin yaki. Sun kama hanyar ne kuwa a rana ta biyu da faruwar wannan aika-aika (sha daya ga watan Muharram). Haka dai wannan ayari na fursunonin suka tsaga zafin hamada ba abin da ke tare da su in ban da tunanin wannan bala'i da kuma daren rabuwa mai ban tsoro, wato daren sha daya ga wata, wanda suka kasance a cikinsa a kan jikkunan shahidai da aka kashe. A wannan lokaci dai wadannan iyalai na Manzon Allah (s.a.w.a) suna kewaye ne da wadannan marasa imani, mashaya jini, wadanda suke jin dadin ganin halin kuncin da wadannan fursunoni suke ciki da kuma kukan da mataye da kananan yara suke yi da kuma halin da Aliyu bn al-Husaini (a.s) yake cikin saboda tsananin rashin lafiya da kuma sarkokin da aka daure shi da su. Haka dai wannan ayari suka shigo garin Kufa, mutanen garin Kufan kuwa suka fito bakin tituna cikin mamakin ganin halin da suke ciki, wasu suna tambaya wadannan fa su wane ne, wasu kuma wadanda suke da masaniyyar abin da ya faru suka kasance cikin damuwa, nadama da kuma kunya kan abin da ya janyo hakan. Haka dai wannan ayari ya kutsa kansa cikin mutanen Kufa, wadanda suke a kan hanyarsu ta zuwa fadar Ubaidullah bn Ziyad, suna masu kuka da juyayin abin da ya samu Iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a) saboda ha'inci da suka yi wa shugaban musulmi kana kuma jikan Manzon Allah, Imam Husain (a.s). A halin yanzu ga su nan suna ganin iyalansa, matansa, matan sahabbansa a matsayin fursunonin yaki, suna fuskantar dukkan wani nau'i na azaba daga Iyalan Ziyad. A waje guda kuma ga kan jikan Manzon Allah nan an tsire shi a kan saman garin Kufa a kan mashi mai tsawon gaske, alhali kuwa su suka kira shi don ya zamanto shugaban al'umma kana mai shiryar da su zuwa ga tafarki madaidaici. Zainab 'yar Aliyu bn Abi Talib (a.s) ta dubi wadannan mutane da suka taru hawaye na zuba mata saboda tunanin rashin dan'uwanta Husaini (a.s) da ta yi, cikin fushi ta ce musu su yi shiru da bakinsu don ta gabatar musu da jawabi. Nan take suka yi shiru don sauraron abin da Zainab, 'yar Fatima al-Zahra, 'yar'uwar Husaini (a.s) za ta gaya musu, ta fara da cewa: "Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, tsira da aminci su tabbata ga Babana Muhammad da iyalansa tsarkaka zababbu. Bayan haka, Ya ku Mutanen Kufa, Ya ku ha'inai maciya amana; shin kuna kuka ne? To kada Allah Ya sa hawayenku ya bushe, sannan kuma kada wannan juyayi naku ya kare. Ku dai tamkar macen da ta kuncen igiyar da ta riga da ta kitsa ta ne(1), imaninku bai kasance ba face ha'inci da yaudara. Shin a cikinku akwai wani mutum in ban da mai da'awar karya na girman kai, wulakantacce, abin kyama, dan koran sarakuna, abin harin abokan gaba, tsiron da ke cikin bola(2), ko kuma kamar azurfar da ke cikin kabari(3)? Ya munana abin da zukatanku suka kitsa muku, Allah Yana fushi da ku, kuma lalle za ku tabbata cikin azaba. Shin kuna kuka da nuna juyayi ne? To wallahi ku yi kuka da yawa kana ku yi dariya kadan, don kuwa ayyukanku sun munana ta yadda ba za ku iya wanke su ba. Shin ya ya za ku iya goge laifin kashe silsilar Cikamakin Annabawa, ma'adinin sakon (Musulunci), shugaban matasan Aljanna, makomar zababbunku, makomar da kuke komawa yayin musiba, hasken hujjojinku kana kuma mai kare sunnoninku. Lalle laifin da kuka aikata ya munana, kuma ya koma gare ku, babu tuba gare ku. Hakika kokarinku ya gaza kamar yadda hannayenku ma suka gaza, kun yi asara, ba abin da kuka sa kawukanku a ciki face fushin Allah, kamar yadda wulakanci da kaskanci suka fada muku. Kaiconku Mutanen garin Kufa! Shin kun san yadda kuka keta hantar Manzon Allah? Kuma wace 'yarsa ce kuka keta huruminta? Kuma wani jininsa ne kuka zubar kana kuma wani haraminsa ne kuka keta? Hakika ayyukanku sun munana kwarai da gaske, wanda munin nasu ya cika sama da kasa. Shin za ku yi mamaki idan sama ya yi ruwan jini? Lallai azabar ranar lahira ya fi zafi kuma ba ku da mataimaki. Kada jinkirin da aka yi muku wajen azaba ya rude ku lallai Ubangijinku Yana nan a madakata(4)". Daga nan sai tawagar fursunonin gidan Manzon Allah (s.a.w.a) suka wuce cikin hanyoyin garin Kufa zuwa fadar mulki don su gana da Ubaidullah bn Ziyad wanda yake zaune a fadar tasa yana karban gaisuwar mutanen da suka zo masa barka da samun nasarar da ya yi kan wadanda suka yi kokarin tunkude mulkin Umayyawa. Ya zauna cikin girman kai alhali kan Husaini (a.s) yana gabansa yana wasa da shi da kuma bugun kan da bulaliyar da take hannunsa cikin farin ciki da annashuwa. Wannan yanayi dai ya sosa wa wani tsohon sahabi mai suna Zaid bn Arkam rai, sai ya kalli Ibn Ziyad wanda a daidai lokacin yana dukan fuskar Husaini (a.s) ya yi masa tsawa ya ce: "Daga bulaliyarka daga wadannan laba guda biyu, na rantse da Ubangijin da babu wani ubangiji sai shi, na ga labban Manzon Allah (s.a.w.a) guda biyu a cikinsu (labban Husaini) a lokuta da yawan da ba zan iya kirga su ba". Daga nan sai ya fashe da kuka. Sai Ibn Ziyad ya ce: "Allah Ya sa idanuwanka su zubar da hawaye, shin kana kuka ne saboda nasarar da muka samu? Da ba don kai tsoho ba ne wanda hankalinsa ya fita daga gare shi ba, da na sare kanka". Nan take Zayd bn Arkam ya fice daga fadar cikin fushi, yana mai share hawayen da ke zubo masa da kuma tunanin yadda yake daukan wannan abin kauna nasa Husaini a lokacin yana dan karami. Yayin fitarsa daga fadar, an jiyo shi yana cewa: "Daga yau Ya ku Larabawa kun zama bayi, kun kashe dan Fatima kuka dora Ibn Marjana (a matsayin shugabanku), alhali kuwa yana kashe mafiya daukakanku da kuma daukaka mafiya sharrinku, kun yarda da wulakanci, Allah wadaran wanda ya yarda da kaskanci(5)". Fitan wannan tsohon sahabi ke da wuya sai aka shigo da fursunonin(6) yakin gidan Manzon Allah (s.a.w.a) cikin fadan mulki. Aka gabatar da mata da yara da Aliyu bn al-Husain al-Sajjad (a.s) gaban Ibn Ziyad, inda Ibn Ziyad din ya dubi Zainab, 'yar'uwan Husaini (a.s) wacce kuma ta dau tuta da kuma nauyin isar da sakonsa iya tsawon rayuwarta, ya ce mata: "Godiya ta tabbata ga Allah da Ya wulakanta ku, Ya kashe ku da kuma bayyanar da ikirarinku na karya(7)". Nan take Zainab ta mayar masa da kakkausar martani da ya jijjiga duk wadanda suke wannan fada, inda ta ce: "Godiya ta tabbata ga Allah da Ya karrama mu da Annabinsa Muhammadu (s.a.w.a), Ya kuma tsarkake mu tsarkakewa(8), sannan kuma ya wulakanta fasiki, fajiri wanda ba shi daga cikinmu". Sai Ibn Ziyad ya ce: "Ya ya kika ga yadda Allah Ya yi da iyalanki?". Sai ta ce: "Allah Ya rubuta musu mutuwa, don haka suka gaggauta zuwa makomarsu, kuma da sannu Allah Zai tada kai da su, kuma za ka amsa tambayoyi a gabanSa(9)". Haka dai maganganu masu zafi suka ci gaba da fitowa daga bakin Zainab da Ibn Ziyad har lokacin da aka zo da Aliyu bn Husain al-Sajjad (a.s) don tsayawa gaba ga Ibn Ziyad. Sai Ibn Ziyad ya tambaye shi: 'Kai wane ne?', sai Imam Sajjad (a.s) ya amsa masa da cewa: "Ni ne Aliyu bn al-Husain". Sai Ibn Ziyad ya sake tambayarsa: "A'a ashe Allah bai kashe Aliyu bn Husain ba?, nan take sai al-Sajjad (a.s) ya mayar masa da martani da cewa: "Lalle ina da wani kani da ake kiransa shi ma Aliyu, amma mutanen sun kashe shi". Sai Ibn Ziyad ya ce: "A'a Allah ne dai Ya kashe shi", nan take sai al-Sajjad ya mayar masa da martani: "A'a, Allah Yana daukan rai ne lokacin mutuwarta". Wannan kalami na al-Sajjad dai ya bata wa Ibn Ziyad rai, don haka sai ya dubi sojojinsa yana ce musu: 'Ku sare kansa'. Ganin haka sai Zainab ta zabura ta ce: "Ya Ibn Ziyad zubar da jininmu ya ishe ka haka nan, wallahi ba zan rabu da shi ba, idan har za ka kashe shi sai dai ni ma ka kashe ni tare da shi(10)". Ibn Ziyad dai ya amince da wannan bukata ta Zainab, don haka sai ya fita ya tafi masallaci don yin jawabi ga mutane da kuma sanar da su batun kashe Husain (a.s) da kuma 'nasarar' da Yazid ya samu. Daga cikin wadanda suke gurin har da Abdullah bn Afif al-Azdi(11) wanda kuma ya ji shi yana cewa: "Godiya ta tabbata ga Allah Wanda ya bayyanar da gaskiya da ma'abutanta da kuma ba wa Amirul Muminina Yazid da 'yan kungiyarsa nasara, Ya kuma wulakanta makaryaci dan makaryaci Husain bn Ali da 'yan shi'ansa(12)". Wannan kalami dai ya bata wa Abdullah rai don haka sai ya mike don fuskantar Umayyawa duk kuwa da karfin takobi da bulali da suke da shi, yana mai cewa: "Ya Ibn Marjana, kai da babanka ne makaryaci kuma dan makaryaci da kuma wanda ya dora ka akan karagar mulki da kuma babansa. Ya Ibn Marjana, shin za ka kashe 'ya'yan Annabawa ne sannan ka yi magana da kalaman masu gaskatawa(13)". Wannan kalami na Abdullah dai ya yi girma wa Ibn Ziyad da kuma bata masa rai alhali kuwa ga shi nan yana cikin giyan mulki, babu wani abin da kawai zai sa ya huce face dai ya kashe shi, don haka sai ya ba da umarnin a kashe shi. To sai dai kuma hakan bai samu ba don kuwa kimanin mutane dari bakwai daga cikin kabilar su Abdullah din sun mike da kuma nuna rashin amincewa da hakan. To amma Ibn Ziyad dai bai hakura, don sai da ya aike da sojojinsa cikin dare suka tafi gidan Abdullah bn Afif din suka fito da shi, suka kashe shi da kuma tsire gawarsa. Ta haka ne dai ya samu ya yi shahada yana mai jaddada kalmar gaskiya ga ja'irin shugaba. Wannan gaba da kiyayya ta Ibn Ziyad dai ba ta kare ba, face dai sai da ya fito garin Kufa a rana ta biyu yana yawo da kan Husaini (a.s) a kan titunan garin, yana mai tsoratar da mutanen garin da kuma raunana ruhin masu son yi masa tawaye. Daga nan aka dawo da wannan kai mai albarka zuwa fada, don wucewa da shi zuwa Sham a kan mashi mai tsawo(14). Haka dai aka wuce da wadannan kawuka, na Husain (a.s) na gaba kana sauran kuma suna baya suka keta hamadan kasar Iraki. A baya gare su kuma ga Zainab (a.s) wacce ta karbi tutan wannan yunkuri tun daga ranar da aka kashe Husaini (a.s). Kamar yadda kuma sauran mata da yara da Aliyu bn Husaini (a.s) wanda yake cikin sarka tun daga kafarsa har wuya(15) suke biye, an dora su dukkansu akan rakuma marasa sirdi(16). Haka dai aka wuce da wadannan kawuka da kuma fursunonin yakin zuwa Damaskus babban fadar gwamnatin Umayyawa, bisa umarnin Yazid bn Mu'awiyya cikin wasikar da ya aike wa Ibn Ziyad yana mai ce masa 'ka gaggauta aiko da fursunonun yakin zuwa wajena(17), ta hakan kuwa yana so ne ya bayyanar da tsananin kiyayyarsa ga Iyalan Manzon Allah (s.a.w.a) da za su tsaya a gabansa alhali suna cikin mawuyacin hali. ____________ (1)- Wannan ibara ce da take nuni da irin ha'inci da rashin cika alkawarin da mutanen Kufan suka yi. (2)- Tsiron da ke cikin bola: Duk tsiron da ke rayuwa cikin najasar dabbobi, zahirinsa na da kyau to amma jijiyoyinsa suna cikin kazanta da kashi dabbobi. (3)- Azurfan da take cikin kabari, zahirinta na da haske amma babu komai a kasanta in ban da mutuwa. Hakan gugan zana ne da ke nufin ha'inci. (4)- Wannan huduba tana cikin Maktal al-Husaini na al-Khawarizmi, juzu'i na 2, shafi na 40-42. (5)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 243, Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafi na 349 da kuma Ibn Kathir, juzu'i na 8, shafi na 190. (6)- Arayin gidan Manzon Allah (s.a.w.a) sun iso garin Kufa ne daga Karbala rana ta biyu bayan isowar kan Husaini (a.s) ne. (7) - Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 244. (8)- Anan tana nuni ne da ayar nan mai girma ta cikin Suratul Ahzab 33:33, inda Allah Ya ke cewa: "Allah kawai na nufin ya tafiyar da kazamta ne daga gare ku, Ya ku Mutanen babban gida, Ya kuma tsarkake ku tsarkakewa". (9)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 244. (10)- Kamar na sama. (11)- Yana daga cikin mabiya Imam Ali (a.s) da kuma Ahlulbaiti. (12)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 244. (13)- Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafin 351, da Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 83, haka nan kuma al-Kufi cikin littafinsa Al-Futuh ya kawo wani abu daga cikin labarin al-Azdi da kuma yadda ya yi shahada, dubi juzu'i na 3, shafi na 144 zuwa gaba. (14)- An ba wa Jazr bn Kais nauyin daukan kan Husaini (a.s) da sauran kawukan sahabbansa daga Kufa zuwa wajen Yazid bn Mu'awiyya a garin Damaskus. (15)- Ibn Athir cikin al-Kamil fi al-Tarikh, juzu'i na 4, shafi na 83. (16)- Ibn Athir cikin al-Kamil fi al-Tarikh, juzu'i na 4, shafi na 83 da kuma A'atham al-Kufi cikin al-Futuh juzu'i na3, shafi na 147. (17)- Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir juzu'i na 4, shafi na 84 da kuma Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafi 354.
http://www.5five-stars.com.ng/2019/10/tafiya-da-iyalan-manzon-allah-kufa.html
0 notes
isiyasy · 5 years ago
Quote
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata da Manzonsa da dukkanin Alayensa. Allah Ya yi gaskiya a yayin da ya ce: Sa'an nan karshen wadannan da suka aikata mugun aiki ya kasance mafi muni, saboda sun karyata ayoyin Allah, kuma suka kasance suna izgili da su". (Surar Rum:10). Ya Yazid, shin kana tsammani ka kwace kasa da sama ne daga gare mu don ana yawo da mu kamar yadda ake yawo da fursunoni, sannan kuma mu wulakantattu ne a wajen Allah kai kuma mai daukaka? Saboda wannan nasara ta zahiri ne da ka samu ya sa kake alfahari da dagawa, kana mai tsammanin ka sami wata kyauta ce ta duniya kuma lamurranka sun daidaita haka nan kuma mulkinka ya dawo hannunka. To amma ka dakata kadan, kada ka yi farin ciki. Shin ka mance da fadin Allah Madaukakin Sarki ne cewa: "Kuma kada wadanda suka kafirta su yi zaton cewa, lalle ne, jinkirin da Muke yi musu alheri ne ga rayukansu. Muna yi musu jinkirin ne domin su kara laifi kawai, kuma suna da azaba mai wulakantarwa". (Surar Al'Imrana: 178.  Ya kai dan sakakku! Shin wannan shi ne adalcinka, ka bar 'ya'yaye da kuyanginka cikin sutura amma ka sanya ana yawo da 'ya'yan Manzon Allah titi-titi cikin mawuyacin hali a matsayin fursunoni. Ka ci mana mutumci ta hanyar bayyanar da fuskokinmu. Sojojinka sun dinga yawo da mu daga gari zuwa gari, dukkan nau'oi na mutane, mazauna duwatsu da bakin teku suna kallonmu, Na kurkusa da na nesa, wulakantattu da madaukaka dukkansu suna kallonmu alhali kuwa muna cikin wani irin hali da babu wani namiji tare da mu da zai taimaka mana ko ba mu wata gudummawa. Ya Yazid, duk wani abin da ka aikata yana nuni ne da tawayenka ga Mahalicci da kuma rashin imaninka da Manzo (s.a.w.a), Littafin Allah da kuna Sunnar da Annabi ya zo da ita. Lalle ayyukanka ba za su kasance abin mamaki ba, don kuwa duk mutumin da kakanninsa suka ci hantar tsarkakakkun bayi, wanda namansa ya ginu daga jinin shahidai, wadanda suka yaki shugaban dukkan Annabawa, ba abin mamaki ba ne in ya wuce dukkan larabawa wajen kafirci, aikata sabo da kuma kiyayya da Allah da ManzonSa (s.a.w.a). Ka tuna fa wadannan munanan ayyuka da ka aikata sun samo asali ne daga kafirci da kuma kullin da kake da shi saboda kakanninka da aka kashe a Badar. Hakika duk mutumin da ya sanya idanuwan kiyayya da gabansa a kanmu ba zai yi kasa a gwuiwa wajen aiwatar da wannan kiyayya a kanmu ba. Lalle ya tabbatar da rashin imaninsa da kuma bayyanar da shi da harshensa lokacin da ya ce cikin farin ciki: "Na kashe 'ya'yan Manzon Allah da kuma mayar da iyalansa fursunoni" da kuma fatan da kakanninsa sun rayu su ga wannan nasara da ya cimma don su ce 'Ya Yazid, kada hannayenka su rasa wannan karfi, lalle ka dau mana fansa a madadinmu. Ya Yazid, shin kana dukan lebban Imam Husain ne da sandanka a gaban jama'a bayan kuwa Manzon Allah (s.a.w.a) ya sha sumbantan wadannan lebba, amma duk da hakan kana cikin farin ciki da annashuwa. Na rantse da Allah, lalle ka kara mana zafin ciwonmu da kuma cutar da mu gaba daya ta hanyar kashe Shugaban matasan Aljanna, dan shugaban larabawa (Ali) kana kuma tauraron iyalan Abdul-Mutallib mai haske. Ta hanyar kashe Husain bn Ali (a.s), lalle ka kusa isa ga makoman kakanninka marasa imani da Allah. Kana bayyanar da wannan aika-aika da ka aikata cikin alfahari da kuma fatan cewa idan kakannin naka suka ga aikin naka za su yarda da shi da kuma yi maka addu'an kada hannunka ya raunana. Ya Allah, Ka karbo mana hakkinmu, Ka dau mana fansa akan wanda ya zaluncemu, Ka nuna fushinKa ga wanda ya zubar da jininmu. Ya Yazid! Ka aikata duk abin da kake so, amma ka kwana da sanin cewa ka yanka jiki da namanka ne da kanka gunduwa-gunduwa. Nan gaba kadan za a gabatar da kai gaban Manzon Allah (s.a.w.a), lalle nauyin mummunan aikinka na zubar da jinin iyalansa da kuma wulakantasu zai gagare ka dauka. Za a kaika inda za a kaika ne a idanuwan iyalan gidansa, inda za a dau fansa kan azzalumai da kuma azabtar da makiya, Kada ka yi zaton wadanda aka kashe a tafarkin Allah matattu ne, A'a rayayyu ne su a wajen Ubangijinsu, ana ciyar da su. Suna masu farin ciki saboda abin da Allah Ya ba su na daga falalarSa, (Surar Al'Imrana: 169-170). Hakika Allah ya isa ya hukumtaka, Manzon Allah kuma ya kasance mai husuma da kai kana Jibrilu kuma shi ne mai taimakonmu. Lalle da sannu wadanda suka dora ka akan musulmi da kuma wahalar da su za su ga abin da ke jiransu, kuma lallai makomar azzalumai ta munana ta zama makoma. Ya Yazid! Ba wai ina maka wadannan maganganu da kuma nusar da kai irin azabar da ke jiranka don ko ka yi nadama kan abin da ka aikata ba ne, a'a, don kuwa kai kana daga cikin mutanen da zukatansu suka kekashe, wadanda rayukansu da jikkunansu suka tarbiyyantu da sabon Allah, wadanda kuma suke karkashin la'anar Manzon Allah (s.a.w.a). Lallai kai kana daga cikin mutanen da Shaidan ya yi musu tambari a kan zukatansu, ba abin da suke haifarwa in ban da sharri. Babban abin mamakin shi ne kisan gillan da 'ya'yan sakakkun masu sabo suka yi wa bayin Allah, ya'yan Annabawa da wasiyyai. Hannayensu sun zubar da jininmu kana kuma namanmu ya kasance musu kalace. Lallai muna jin zafi ga wadanda aka bar gawawwakinsu a yashe a fagen daga ba tare da an bisne su ba. Kai Yazid, idan har kana tunanin cewa wannan abin da ya same mu a matsayin wata nasara gare ka, to lallai za ka dandana kudanka kan hakan a lokacin da ba abin da za ka gani face abin da ka aikata, don kuwa Ubangijinka ba ya zaluntar bayinSa. Allah Shi ne abin dogaronmu kuma Shi ne kawai muka mika burinmu gare Shi. Ka yi dukkan makircin da ka ke iyawa, sannan ka yi dukkan kokarin da za ka iya, amma dai wallahi ba za ka iya shafe ambatonmu ba da kuma dushe haskenmu, haka nan kuma ba za ka kawar da wannan wulakancin da kake ciki ba. Shin akwai wani abin da ya rage wa kalamanka in ba rauni ba, haka nan kuma ranakunka face 'yan kididdigaggu ba. Lallai ka kiyaye ranar da mai sanarwa zai sanar da la'anar Allah a kan azzalumai. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai, Wanda ya cika wa na farkonmu da sa'ada da kuma gafara, kana na karshenmu kuma da shahada da rahama, muna rokon Allah da ya cika musu da lada Ya kuma kara musu Ya kuma kyautata mana halifanci, don kuwa Shi Mai rahama ne, kuma lalle Allah Ya isar mana kuma madalla da wakilcinSa. >==> Isiya Sy D Young-Gifted.
http://www.5five-stars.com.ng/2019/10/hudubar-zainab-al-kubra-fadar-yazid-bn.html
0 notes
isiyasy · 5 years ago
Quote
http://www.5five-stars.com.ng/2019/09/sakon-jamiar-kufa-zuwa-ga-imam-hussain.html
0 notes
isiyasy · 5 years ago
Text
SAKON JAMI'AR KUFA ZUWA GA IMAM HUSSAIN (AS)
"Da Sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin Kai(1): Zuwa ga Husaini bn Ali Amirul Muminina (a.s), daga 'yan shi'arsa (mabiyansa) kuma 'yan shi'an mahaifinsa Amirul Muminina (a.s); bayan haka: Hakika mutane fa suna nan suna jiranka, ba su yarda da kowa ba face kai, don haka ka gaggauta zuwa Ya Dan Manzon Allah (s). Lalle fa dabino ya riga da ya zama kore, haka nan kuma 'ya'yan itatuwan sun riga da sun isa, kuma kasa ta cika da ciyawa kamar yadda kuma bishiyoyi duk sun yi fure (duk hikaya ce ta nuna yadda al'umma suke cikin jiransa). Don haka idan har kana so kana iya isowa zuwa gare mu, za ka same mu cikin shirin tarbarka dakaru kuma suna jiran isowarka. Amincin Allah, rahama da albarkarSa su tabbata a gare ka, da kuma mahaifinka kafin nan(2)". Lokacin da Imam Husaini (a.s) ya samu wannan wasika, da kuma karanta abin da ta kumsa, sai ya tambayi wadanda suka kawo hakikanin wadanda suka rubutata, don kuwa tana kumshe ne da mubaya'a da kuma bayanin yadda yanayi yake a wancan lokacin da kuma kira zuwa gare shi da ya gaggauta isa zuwa gare su. Don haka sai wadannan mutane suka amsa masa da kuma ambaton sunayen mutanen da suka ta wasikar daya bayan daya. Wannan wasika dai ta bayyana wa Imam Husaini (a.s) yadda yanayi yake ne, da kuma tsayar masa da hujjar motsawa da kuma yunkurawa, sai dai kuma har ya zuwa yanzu hankalinsa bai kwanta da hakan ba tukun, don kuwa Ahlulbaiti (a.s) suna da tajruba kan irin wadannan alkawurra, kuma Imam Husaini (a.s) ya ga hakan da kansa tare da mahaifinsa Amirul Muminina (a.s) da kuma dan'uwansa Imam Hasan (a.s). Don haka dole ne ya tabbatar da yanayin tukun kafin ya dau matsaya. Don haka sai Imam Husaini (a.s) ya tafi Dakin Allah mai tsarki, ya tsaya gaba da Ubangijinsa ya yi raka'o'i biyu yana mai rokon Allah da ya zaba masa abin da yafi alheri da kuma shiryar da shi zuwa ga abin da ya fi dacewa. Bayan haka, sai Imam Husaini (a.s) ya ga cewa dole ne ya aika da wani manzo na daban wanda zai gane masayadda al'amurra suke, share masa fage da kuma sanar da shi halin da Kufan take ciki a daidai wannan lokacin, don ya iya daukar matakin da ya dace. To amma a irin wannan yanayi dole ne Imam Husaini (a.s) ya zabi wani mutum wanda zai iya daukan wannan gagarumin nauyi wanda kuma ya ke tare da hikima da jarunta, don haka sai ya zabi dan baffansa Muslim bn Akil don gudanar da wannan aiki. Daga nan sai ya kira shi ya bayyana masa duk halin da ake ciki da kuma abubuwan da wasikun da aka aiko masa suka kumsa, don ya san halin da ake ciki, kuma don ya sami damar gudanar da wannan babban aiki da aka dora masa. Ba tare da wani bata lokaci ba Muslim ya karbi wannan aiki mai wahalar gaske yana mai sauraron dukkan nasihohi da shiryarwar Husaini (a.s), (Ya umarce shi da tsoron Allah da kuma boye abin da ya kai shi, kuma idan har ya ga lalle mutane da gaske suke yi, to ya sanar da shi(3). Daga nan sai Imam Husaini (a.s) ya rubuta wasika zuwa ga mutanen Kufa ya ba shi yana mai ce masa: "Ka kama hanya zuwa Kufa, idan har abin da suka rubuto gaskiya ne to ka sanar da ni sai in same ka a can". Don haka Muslim bn Akil ya bar bar garin Makka zuwa kasar Iraki ne a ranar 15 ga watan Ramalana shekara ta 60 bayan hijira tare da wasu mutane guda biyu wadanda za su dinga nuna masa hanya. Daidai wannan lokaci kuwa ana cikin tsananin zafin bazara, rana tana da zafin gaske ga kuma zafin hamada, ga kuma nisan wuri. Wannan tafiya dai ta dauke su kimanin kwanaki 20 daga Makka zuwa Kufan, don kuwa Muslim ya isa Kufan ne ranar 5 ga Shawwal, bayan fuskantar wahalhalu kala-kala. Muslim dai shi kadai ya iso saboda abokan tafiyan nasa guda biyu sun mutu a hanya don wahala da kuma kishin ruwar da ya same su a hanya. Abin da ya faru kuwa shi ne a daya daga cikin darare, yayin da suke tafiya, sai suka bace daga hanya inda suka ta tafiya, sai da gari ya waye sai suka gano ashe sun kauce wa hanya din, don haka sai suka nuna wa Muslim hanyar da zai bi ya karasa zuwa Kufan don su ba za su iya karasawa ba saboda kishir ruwa da kuma raunin da ke damunsu, a nan dai suka zauna har suka mutu cikin kishir ruwa(4). Muslim dai ba zai iya daukan wadannan mutane ba, don haka sai ya bar su ya kama hanyarsa tare da wasu mutane da suka same su a hanya, sai suka gano asalin hanyar suka ci gaba da tafiya har lokacin da suka gano wata rijiya, inda suka yada zango a gurin suna cikin gajiya da kuma jin zafin rabuwa da abokan tafiyarsu na farko (masu nuna wa Muslim hanya). A nan Muslim ya dakata kusa da wannan rijiya, inda ya rubuta wa Imam Husaini (a.s) yadda tafiyar tasa ta kasance, da kuma irin wahalhalun da suka fuskanta a hanya, sannan kuma ya sanar da Imam Husaini (a.s) cewa yana jiran amsa da umarninsa kan abin da ya kamata ya aikata a gaba. Sai ya nade wasikar ya ba wa wani amintaccen mutum daga kabilar Hay mai suna Kais bn Musahhar don kai wa ga Imam Husaini (a.s) a Makka, lokacin da wasikar ta shiga hannunsa, Imam Husaini (a.s) ya rubuta wa Muslim bn Akil amsa yana mai umartansa da ya ci gaba da wannan aiki nasa(5). Isowar wannan wasika ta Husaini (a.s) ke da wuya, sai Muslim ya mike ya kama hanyar Kufa, a hanyarsa ta tafiya ya tsaya a wani yanki mai ruwa da kabilar Tay suke zaune na dan wani lokaci kana ya ci gaba har ya isa garin Kufa a ranar 5 din ga watan Shawwal, inda ya sauka a gidan Mukhtar bn Abi Ubaidah al-Thakafi da kuma daukar wurin a matsayin helkwatar ayyukansa na siyasa a garin Kufa. Muslim dai ya iso a matsayin wakilin Imam Husaini (a.s) wanda kuma ya ke dauke da wasikarsa, don haka mutane suka yi maraba da shi da kuma mika mubaya'arsu gare shi. Daga nan sai Muslim ya fara ganawa da mutane daban-daban da kuma fara gudanar da ayyukansa na siyasa cikin nitsuwa da kuma kwarin gwuiwa. Yana mai tara al'umma da kuma sanya musu ruhin gwagwarmaya bugu da kari kan karbar mubaya'a ga Imam Husaini (a.s), inda ya karbi mubaya'a mai yawan gaske daga mutanen garin, wadanda suke fashewa da kuka a duk lokacin da ya karanta musu wasikar Husaini (a.s) suna nuna shirinsu na tarbarsa da kuma bukatarsa da ya iso don jagorantarsu. Haka dai Muslim bn Akil ya ci gaba da gudanar da ayyukansa da kuma karbar mubaya'ar mutane ga Imam Husaini (a.s), ta yadda har sai da adadin mutanen da suka mika wuyansu da kuma yin bai'a suka kai mutane dubu goma sha takwas(6). Lokacin da Muslim ya ga irin wannan yanayi da kuma irin wannan adadi na jama'a da suka mika wuya da kuma tabbacin da yake da shi na cewa wannan adadi dai suna iya fuskantar duk wani karfi da zai yi adawa da jagorancin Imam Husaini (a.s), nan take sai ya rubuta wa Imam Husaini (a.s) wasika yana mai bayyanar masa da yanayin yadda al'amurra suke a garin na Kufa da kuma bayyana masa irin ayyukan da ya gudanar, bugu da kari kan bukatarsa da ya iso zuwa Kufan. Haka dai al'umma suka ta tuttudowa zuwa ga Muslim har sai da ya kasance irin jama'ar da suke tare da shi suka kasance abin tsoro da kuma hatsari ga hukumar Umayyawa, to sai dai kuma sanannen abu ne cewa irin wannan yanayi ba zai buya wa Yazid da kuma gwamnansa na Kufan wato Nu'uman bn Bashir ba. Da farko dai Nu'uman bn Bashir ya so kawo karshen irin wannan yanayi ta hanyar ruwan sanyi da kuma watsa wannan karfi na al'umma amma dai abin ya ci tura. Irin siyasar da Nu'uman din dai ya dauka wajen magance wannan matsala ba ta yi dadi wa wasu daga cikin 'yan amshin shatan wannan hukuma ba, suna masu tsoron rasa matsayin da suke da shi na siyasa da kuma zamantakewa, don haka sai daya daga cikinsu mai suna Abdullah bn Muslim ya rubuta wa Yazid wani rahoto yana mai bayyana masa yadda al'amurra suke gudana da kuma irin hatsarin da ake ciki, don haka ya bukace shi ya da tsige Nu'uman bn Bashir a matsayinsa na gwamna yana mai cewa shi mai rauni ne da kuma bukatarsa da ya aiko da wani mutum mai kakkausar hali wanda zai yi maganin lamarin da karfin cin tuwo. Kamar yadda wasu mutane na daban irin su Ammara bn Ukbah da Umar bn Sa'ad bn Abi Wakkas suka rubuta wa Yazid din suna bayyana masa halin da ake ciki. Ga abin da rahoto na farko ya kumsa: "Bayan haka, hakika Muslim bn Akil ya iso garin Kufa, kuma 'yan shi'a sun yi masa mubaya'a a madadin Husain bn Ali bn Abi Talib, to matukar dai kana da bukatuwa da garin Kufa, to ka aiko da wani mutum mai karfi da zai gudanar da umarninka da kuma aikata abin da kake aikatawa da abokan gabanka, don kuwa Nu'uman bn Bashir mutum ne mai rauni ko kuma yana gudanar da lamurransa kamar mutum mai rauni(7)". A wancan loakcin garin Kufa dai ya kasance gari ne da abubuwa suke ta faruwa, wanda kuma bangarori biyu suke ta gasa da kuma kokarin garin bayan juna, wato bangaren Ahlulbaiti (a.s) da kuma bangaren Umayyawa, don haka sai garin ya kasance cikin hatsarin gaske don komai na iya faruwa kuma a kowani lokaci, don kuwa hukumar Yazid tana kusa da ta fadi kasa war-was, in da ba don wasu dalilai ba. Manzanni daga Kufan dai sai isowa suke yi zuwa ga Husain (a.s) da kuma Yazid kowannensu na kiran da su gaggauta daukan matakin da ya dace don rike al'amurran gudanarwa da jagorancin al'umma. Wadannan manzanni da suke isowa wajen Yazid suna bayyana masa cewa fa ga wata guguwa nan tana son tasowa a garin Kufa, kuma gwamnansa mai rauni ne ba zai iya kawo karshenta ba, don haka dole ne fa ya dau matakin gaggawa. Don haka bayan isowar wadannan sakonni, sai Yazid ya fara tunani da kuma neman wani mutum wanda ya yi kaurin suna wajen ayyukan ta'addanci da kuma rashin tausayi da imani, mai tsananin son mulki, wanda kuma a shirye yake ya sayi mulkin komai tsadansa, haka nan kuma wanda ya fi kowa tsananin gaba da Ahlulbaiti (a.s). Don haka bayan bincike da shawarwari, bai ga duk wani mutumin da ya dace da wannan matsayi wanda kuma yake da wadannan siffofi ba in ban da Ubaidullah bn Ziyad, wanda a wancan lokacin shi ne gwamnan Basra. Daga nan sai Yazid ya yanke shawarar mika wannan aiki ga Ubaidullah bn Ziyad din bayan bayanin da Sarjun daya daga cikin bayin Mu'awiyya wanda ya ce masa: Ai tun lokacin Mu'awiyya na da rai ya nada Ubaidullah a matsayin gwamnan Basra(8), kuma har ya zuwa yanzu wannan takarda ta nadi tana tare da shi. Don haka nan take sai Yazid din ya yarda da hakan da kuma ba wa Ubaidullah wannan matsayi, yana mai umartansa da ya yi amfani da tursasawa da kuma kaushin hali bugu da kari kan zubar da jinin duk wani dan'adawa har sai an kawo karshen wannan adawa ga hukumarsa. Ga kadan daga cikin abin da wasikar Yazid din ta nada Ubaidullah ta kumsa: "Bayan haka, wasu mabiyana daga mutanen Kufa sun rubuto min cewa Muslim bn Akil yana can yana tara mutane a Kufa don rarraba kan al'ummar musulmi, don haka ka kama hanyar Kufa a duk lokacin da wannan wasika tawa ta isa hannunka, ka nemi Ibn Akil a duk lokacin da ka isa, idan ka same shi ka daure da sarka, ka kashe shi ko kuma ka kore shi daga garin. Wassalam(9)". ____________ (1)- Sayyid Ibn Tawus ya bayyana cewa wannan ita ce wasikar karshe da mutanen Kufa suka aikowa Imam Husaini (a.s), wadanda suka aiko ta kuwa su ne Hani' bn Hani' al-Sabi'i da Sa'id bn Abdullah al-Hanafi. Lokacin da suka kawo wannan wasika sai Imam Husaini (a.s) ya ce musu: "Ku ba ni labarin su wane ne suka rubuta wannan wasika da kuka kawo min? Sai suka ce: "Ya Dan Manzon Allah (s.a.w.a),Shabbath bn Rab'i,Hajjar bn Abjar, Yazid bn Harith bn Ruwaym, Urwah bn Kais, Amru bn al-Hajjaj da kuma Muhammad bn Umayr bn Atarud ko kuma (Muhammad bn Amry al-Tamimi), kamar yadda kuma Shaikh al-Mufid ya ambata cikin Al-Irshad, shafi na 203. (2)- Maktal al-Husain na Ibn Dawus, shafi na 15 da 16. (3)- Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 21. (4)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 204 (5)- Kamar na sama. (6)- Muruj al-Zahab na al-Mas'udi, juzu'i na 3, shafi na 54. (7)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 205. (8)- Ubaidullah bn Ziyad dai a wancan lokacin shi ne gwamnan Basra don haka sai ya ba da wannan mukami ga dan'uwansa Usman shi kuma ya kama hanyar Kufa. (9)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafin 206.
from Blogger https://ift.tt/32WCKYv
0 notes
isiyasy · 5 years ago
Quote
http://www.5five-stars.com.ng/2019/09/sakon-jamiar-kufa-zuwa-ga-imam-hussain.html
0 notes
isiyasy · 5 years ago
Quote
Haka dai kaddara ta gitta kan wannan al'amari kuma ta ci gaba da jagorantarsa, ta yadda bayan dan wani lokaci da kuma 'yar tafiya, sai sojojin Umayyawa suka katse wa Imam Husain (a.s) hanya lamarin da ya tilasta masa sauka. Daga nan sai Husaini (a.s) ya sauka yana tambaya, kamar yana neman Karbala ne: "Mene sunan wannan guri?", sai aka ce masa Kasar al-Taf, sai ya ce: "Shin akwai wani suna na daban kuma da ake kiran wannan waje da shi?", sai aka ce masa ana kiran wajen Karbala. Sai ya ce: "Ya Allah ina neman tsarinKa daga Karb (wahala, bakin ciki) da kuma bala' (bala'i)". Daga nan sai ya ce: "Wannan shi ne gurin wahala da bala'i (karb wa bala'), ku sauko, nan ne karshen tafiyarmu, wajen da za a zubar da jininmu, nan ne muhallin kaburburanmu, wannan dai shi ne abin da Kakana (s.a.w.a) ya ba ni labarinsa(1)". Wannan rana dai ita ce ranar Alhamis ta biyu ta cikin watan Muharram shekara ta 60 bayan hijira(2), inda Husaini (a.s) tare da sahabbansa suka sauka a kasar Karbala, kasar jini, sadaukarwa, shahada, tabbatuwa da kuma yunkuri. Daga nan sai Husaini (a.s) ya kafa tantinsa da gyara makamansa, yana rera wannan wakar: Ya kai lokaci, kaiconka a matsayin aboki, Shin kasa da sama kake da shi.Na daga mabukaci da abokai nawa suka mutu, Alhali kuwa lokaci ba ya wadatuwa da mamayi.Dukkan wani mai rai zai bi (wannan) hanya, Akwai alkawarin da yafi saukin cikawa kamar mutuwaLalle al'amarin yana hannun Mai Daukaka ne kawai(3). Haka Imam Husain (a.s) ya ci gaba da rera wannan waka ita kuwa Zainab, kanwarsa wacce kuma za ta kasance mai isar da sakon wannan yunkuri a nan gaba, ta saurara tana jinsa tana mai lura da irin halin da yake ciki da kuma abin da ya ke ji. Sai ita ma cikin sauti da ke cike da tausayi da kuma tada hankali ta ce: "Wannan kalami ne na mutumin da ya tabbatar zai mutu". Sai ya ce mata: "Lalle kan Ya 'Yar'uwata", sai ta ce: "A'a saboda irin halin da yake ciki, Husaini (a.s) yana sanar da ni mutuwarsa(4)". Haka dai wadannan sojoji suka ci gaba da kasancewa, shi kuma Ubaidullah bn Ziyad ya ci gaba da turo sojojinsa iyakan iyawarsa. Daga cikin mashahuran mutanen da ya dora wa wannan nauyi na aikata wannan mummunan aiki na kashe Imam Husain (a.s) shi ne Umar bn Sa'ad bn Abi Wakkas, duk da cewa daga farko ya ki amincewa da hakan, amma daga baya ya amince saboda barazanar da Ibn Ziyad din ya yi masa na hana shi mukamin da aka ba shi na gwamnan garin al-Ray. Kafin amincewa da wannan aiki dai, Umar bn Sa'ad ya shafe tsawon dare yana ta tunani kan ko ya zabi mulki da dan wani jin dadi na duniya ko kuma ya zabi kula da lahira da kuma kula da jiga-jiga na adalci da gaskiya wanda za su hana shi aikata wannan mummunan aiki da kuma zubar da wannan jini mai tsarki. Daga karshe dai ya amince da mulki da jin dadin duniya da kuma taimakawa wajen kashe masu kira zuwa ga gaskiya da kuma adalci. An jiyo shi yana ta nanata wadannan baituka na waka: Shin zan bar mulkin Ray alhali ya kasance burinsa, Ko zan koma in zama abin zargi don kashe Husaini. Lalle cikin kashe shi akwai wuta wacce ba ta da, Shamaki, sai dai mulkin Ray kuma abin so na ne(5). Don haka da gari ya waye sai ya amince da wannan nauyi da aka dora masa, ya kama hanya ya nufi inda Husaini (a.s) ya ke yana jagorantar kimanin dakarun dubu hudu, inda ya sauka a Nainawa da kuma mai da wurin sansanin sojojinsa. Lokacin da ya sauka a wurin da kuma kewaye Imam Husain (a.s) da sahabbansa, sai ya fara tattaunawa da Imam din (a.s) inda suka tsayar da wasu abubuwa tsakaninsu, daga nan sai ya rubuta wa Ibn Ziyad halin da ake ciki da kuma irin yarjejeniyar da suka kulla da Husaini (a.s) da ta hada da kawo karshen mamayan da suka yi wa masa da kuma ba shi damar komawa inda ya fito don kiyaye zubar da jinin da aka kama hanyar zubar da shi. Lokacin da wannan wasika ta Ibn Sa'ad ta shiga hannun Ibn Ziyad, da farko dai ya yarda da wannan shawara ko kuma yarjejeniya da Ibn Sa'ad ya cimma da Husaini (a.s), to sai dai kuma daga baya ya canza ra'ayinsa lokacin da Shimr bn Zil-Jawshan, wanda ya kasance daga cikin mafiya gaba da Husaini da kuma Ahlulbaiti (a.s), ya sa baki cikin lamarin da nuna masa cewa matukar ya bar Husaini (a.s) ya fita daga wannan hali da yake ciki, to kuwa zai sake zuwa ya tara karfi da kuma ganin bayan dakarun Umayyawan. Don haka babu wani abin da ya kamata ya aikata face ya bar shi cikin wannan hali da kuma tilasta masa yin mubaya'a da kuma mika wuya ga mulkin Ubaidullah bn Ziyad. Wannan shawara dai ita ce ta canza komai da kuma haifar da wannan mummunan ta'addancin da ya fi kowane ta'addanci cikin tarihi. Ta haka ne dai abubuwan da suka faru cikin tarihi suke fara faruwa saboda daukan wani mataki ko kuma bijiro da wani ra'ayi kamar wannan kalma ta Shimr bn Zil Jawshan, wacce ta taimaka nesa ba kusa ba wajen kisan gillan da aka yi wa Husaini (a.s) da mabiyansa, wacce daga baya ta yi sanadiyyar faduwar gwamnatin zalunci ta Umayyawa da kuma kawo karshenta. Ubaidullah bn Ziyad dai ya amince da wannan shawara ta Shimr, don haka sai ya rubuta wasika ta barazana ya ba wa Shimr din don ya kai wa Umar bn Sa'ad, yana mai umartansa da ya aikata abin da aka ce masa ko kuma ya sauka daga mukamin da aka ba shi ya mika shi ga Shimr bn Zil Jawshan. A cikin wannan wasika dai Ibn Ziyad ya rubuta cewa: "Ni ban tura ka wajen Husaini don ka yi sulhu da shi ko kuma ka lamunce masa ransa ba ko kuma ka nemi uzuri daga gare shi ko kuma ka nema masa ceto daga gare ni ba. Ka gane cewa, idan har Husaini da mutanensa sun yarda suka mika wuya, to ka aiko su zuwa gare ni, idan kuwa har sun ki amincewa da haka, to ka fada musu ka kashe su da kuma lalata jikkunansu, don kuwa sun cancanci hakan. Bayan kashe Husaini ka sanya dawaki su yi sukuwa akan kirgi da kuma bayansa, don kuwa shi dan tawaye ne, ina ganin hakan ba zai kasance mummnan abu ba bayan mutuwa. Wannan dai shi ne abin da nake so ka yi masa, in ka aikata hakan kuwa to za mu saka maka a matsayin mutum mai ji da kuma da'a. Idan kuwa ka ki aikatawa, to ka sauka daga aikinmu ka bar sojojinmu ka mika su ga Shimr bn Zil Jawshan, don kuwa mun riga da mun ba shi ikonmu. Wassalam(6)". Bayan rubuta wannan wasika sai Shimr ya karba ya kama hanya yana cike da sharri da kuma mugunta a cikin zuciyarsa, da isarsa sai ya mika wa Umar bn Sa'ad wasikar da take ba shi zabi biyu, ko ya fada wa Husaini (a.s) da mabiyansa, wanda zai kai shi ga samun mulki da kuma matsayi a wajen magabatansa, ko kuma ya ki aikata hakan ya rasa wannan matsayi, bayan karanta wasikar sai ya amince da zaban duniya da kuma mulki a kan gaskiya da kuma yardar Allah. Daga nan sai ya tsayar zai jagoranci wannan yaki da kuma zubar da jinin Husaini (a.s). Don haka a ranar 7 ga watan Muharram sai Umar bn Sa'ad ya tura sojojinsa da su kange Husaini (a.s) ta bangaren Kogin Furat, wato su shiga tsakanin Iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a) da yadda za su samu ruwan sha, don su mutu cikin kishin ruwa ko kuma su mika kai, hakan dai daya ne daga cikin makircin yaki. Kana kuma ya fara rarraba sojojinsa da kuma nada kananan kwamandoji da za su jagorance su, suna masu matsawa kusa da tantunan Husaini da mabiyansa. Wannan lamari dai na kusantan tantunan Husaini (a.s) ya faro ne daga ranar 9 ga watan Muharram, lokacin da sojojin Umayyawa suka fara daddaga takubba da masunsu cikin fushi da kurari. A daidai wannan lokaci kuwa Husaini (a.s) yana zaune a gaban tantinsa yana kallon wannan hamada ta al-Taf cike da tunanin irin wannan mawuyacin hali da ake ciki da kuma irin abubuwan da zai faru nan gaba ga wannan yunkuri da kuma ma'abuta son gaskiya da 'yanci. A daidai wannan lokaci dai Husaini (a.s) bai san matsayar da Umar bn Sa'ad ya dauka ba dangane da su na kai musu hari, don haka sai ga Zainab ta nufo shi tana mai cewa: "Ba ka ji sautin da ke zuwa kusa-kusa ba". Zainab ba ta bar wannan guri ba, sai ga Abbas bn Ali (a.s), kanin Imam Husain (a.s) ya iso yana cewa: "Ya Dan'uwana, abokan gaba fa sun iso". Nan take Husaini (a.s) ya mike yana ganin ya dace ya yi magana da sojojin Umayyawa don sanin halin da ake ciki, don haka sai ya bukaci Abbas da ya yi magana da su don jin ra'ayinsu. To sai dai kuma ina!, alkawarin mulki da shugabancin da aka musu ya sanya su cikin maye, don haka sai rige-rige suke yi wajen yakan Husaini (a.s) da zubar da jininsa mai tsarki don samun matsayi, mulki da kuma dukiyar da aka yi musu alkawari, don haka amsarsu dai ita ce: "Ko dai Husaini ya mika wuya ga mulkin sarki ko kuma mu yake shi". Daga nan sai Abbas ya komo ya gaya wa Husaini (a.s) matsayar kwamandojin sojin Umayyawan. Don haka dai Imam Husain (a.s) ba shi da wani abin yi in ban da yaki don kuwa ya riga da ya dau matsayar babu ja da baya "Hakika kamata ba zai yi mubaya'a ga mutum kamar Yazid ba", don haka sai ya ci gaba da fadin: "Wallahi ba na ganin mutuwa face sa'ada, rayuwa kuwa tare da azzalumai a matsayin wulakanci". Ya ci gaba kuma da bayyanar da taken nan da ya gada daga Manzon Allah (s.a.w.a), wanda kuma ya bayyanar da shi ga Umayyawa cikin 'yan kwanakin da suka gabata a yankin Al-Baidha': "Ya Ku Mutane! Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: 'Duk wanda ya ga wani ja'irin sarki, wanda ya ke halalta haramun din Allah, mai kwance alkawarin da ya yi, mai saba wa Sunnar Manzon Allah, mai zaluntar bayin Allah, amma ya zuba ido ba tare da ya yi kokarin gyara shi a aikace ko kuma da zance ba, to lalle hakkin Allah ne Ya shigar da shi makomarsa". Imam Husaini (a.s) dai yana ganin mulkin Yazid, siyasarsa da jami'an da suke tare da shi a matsayin misdaki ko kuma hakikanin irin mutanen da Manzon Allah (s.a.w.a) ya ke nufi a wannan kalami nasa, don haka babu wani abin da ya rage masa face shiri don fuskantar wannan makiyi, da kuma daga tutar jihadi da yunkuri don tabbatar da gaskiya da kuma gudanar da shari'ar Allah. Don haka sai ya bukaci Abbas da ya tafi wajen Ibn Sa'ad don neman ya ba su dama ta dare guda don yin tunani kan wannan al'amari da kuma daukar matsayar da ta dace a gobe (Goma ga watan Muharram -Ranar Ashura). Don haka Abbas ya tafi ya shaida wa Ibn Sa'ad wannan bukata ta Husaini (a.s), bayan tattaunawa da kwamandojinsa, ya amince da wannan bukata, shi kuwa Abbas ya koma ya gaya wa Husaini (a.s) abin da ya faru. ____________ (1)- Kamar na sama, shafi na 33. (2)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 227, Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 52, don haka shahadar Imam Husain (a.s) ta kasance ne ranar Juma'a ba ranar Litinin ba kamar yadda da dama suka tafi a kai. (3)- Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafi na 319, Maktal al-Husain (a.s) na Ibn Dawus, shafi na 33, haka nan kuma Shaikh Mufid cikin Al-Irshad, shafi na 232 ya ambato cewa, daga Aliyu bn Husain al-Sajjad (a.s) cewa Imam Husain (a.s) ya kasance yana rera wannan waka daren goma ga watan Muharram. (4)- Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafi na 319, Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 58 da kuma Maktal al-Husain (a.s) na Ibn Dawus, shafi na 34. (5)- Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 52, 53. (6)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 229 da kuma Tarikh al-Ummam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafi na 314.
http://www.5five-stars.com.ng/2019/09/kasar-da-aka-yi-alkawari.html
0 notes
isiyasy · 5 years ago
Quote
Haka dai kaddara ta gitta kan wannan al'amari kuma ta ci gaba da jagorantarsa, ta yadda bayan dan wani lokaci da kuma 'yar tafiya, sai sojojin Umayyawa suka katse wa Imam Husain (a.s) hanya lamarin da ya tilasta masa sauka. Daga nan sai Husaini (a.s) ya sauka yana tambaya, kamar yana neman Karbala ne: "Mene sunan wannan guri?", sai aka ce masa Kasar al-Taf, sai ya ce: "Shin akwai wani suna na daban kuma da ake kiran wannan waje da shi?", sai aka ce masa ana kiran wajen Karbala. Sai ya ce: "Ya Allah ina neman tsarinKa daga Karb (wahala, bakin ciki) da kuma bala' (bala'i)". Daga nan sai ya ce: "Wannan shi ne gurin wahala da bala'i (karb wa bala'), ku sauko, nan ne karshen tafiyarmu, wajen da za a zubar da jininmu, nan ne muhallin kaburburanmu, wannan dai shi ne abin da Kakana (s.a.w.a) ya ba ni labarinsa(1)". Wannan rana dai ita ce ranar Alhamis ta biyu ta cikin watan Muharram shekara ta 60 bayan hijira(2), inda Husaini (a.s) tare da sahabbansa suka sauka a kasar Karbala, kasar jini, sadaukarwa, shahada, tabbatuwa da kuma yunkuri. Daga nan sai Husaini (a.s) ya kafa tantinsa da gyara makamansa, yana rera wannan wakar: Ya kai lokaci, kaiconka a matsayin aboki, Shin kasa da sama kake da shi.Na daga mabukaci da abokai nawa suka mutu, Alhali kuwa lokaci ba ya wadatuwa da mamayi.Dukkan wani mai rai zai bi (wannan) hanya, Akwai alkawarin da yafi saukin cikawa kamar mutuwaLalle al'amarin yana hannun Mai Daukaka ne kawai(3). Haka Imam Husain (a.s) ya ci gaba da rera wannan waka ita kuwa Zainab, kanwarsa wacce kuma za ta kasance mai isar da sakon wannan yunkuri a nan gaba, ta saurara tana jinsa tana mai lura da irin halin da yake ciki da kuma abin da ya ke ji. Sai ita ma cikin sauti da ke cike da tausayi da kuma tada hankali ta ce: "Wannan kalami ne na mutumin da ya tabbatar zai mutu". Sai ya ce mata: "Lalle kan Ya 'Yar'uwata", sai ta ce: "A'a saboda irin halin da yake ciki, Husaini (a.s) yana sanar da ni mutuwarsa(4)". Haka dai wadannan sojoji suka ci gaba da kasancewa, shi kuma Ubaidullah bn Ziyad ya ci gaba da turo sojojinsa iyakan iyawarsa. Daga cikin mashahuran mutanen da ya dora wa wannan nauyi na aikata wannan mummunan aiki na kashe Imam Husain (a.s) shi ne Umar bn Sa'ad bn Abi Wakkas, duk da cewa daga farko ya ki amincewa da hakan, amma daga baya ya amince saboda barazanar da Ibn Ziyad din ya yi masa na hana shi mukamin da aka ba shi na gwamnan garin al-Ray. Kafin amincewa da wannan aiki dai, Umar bn Sa'ad ya shafe tsawon dare yana ta tunani kan ko ya zabi mulki da dan wani jin dadi na duniya ko kuma ya zabi kula da lahira da kuma kula da jiga-jiga na adalci da gaskiya wanda za su hana shi aikata wannan mummunan aiki da kuma zubar da wannan jini mai tsarki. Daga karshe dai ya amince da mulki da jin dadin duniya da kuma taimakawa wajen kashe masu kira zuwa ga gaskiya da kuma adalci. An jiyo shi yana ta nanata wadannan baituka na waka: Shin zan bar mulkin Ray alhali ya kasance burinsa, Ko zan koma in zama abin zargi don kashe Husaini. Lalle cikin kashe shi akwai wuta wacce ba ta da, Shamaki, sai dai mulkin Ray kuma abin so na ne(5). Don haka da gari ya waye sai ya amince da wannan nauyi da aka dora masa, ya kama hanya ya nufi inda Husaini (a.s) ya ke yana jagorantar kimanin dakarun dubu hudu, inda ya sauka a Nainawa da kuma mai da wurin sansanin sojojinsa. Lokacin da ya sauka a wurin da kuma kewaye Imam Husain (a.s) da sahabbansa, sai ya fara tattaunawa da Imam din (a.s) inda suka tsayar da wasu abubuwa tsakaninsu, daga nan sai ya rubuta wa Ibn Ziyad halin da ake ciki da kuma irin yarjejeniyar da suka kulla da Husaini (a.s) da ta hada da kawo karshen mamayan da suka yi wa masa da kuma ba shi damar komawa inda ya fito don kiyaye zubar da jinin da aka kama hanyar zubar da shi. Lokacin da wannan wasika ta Ibn Sa'ad ta shiga hannun Ibn Ziyad, da farko dai ya yarda da wannan shawara ko kuma yarjejeniya da Ibn Sa'ad ya cimma da Husaini (a.s), to sai dai kuma daga baya ya canza ra'ayinsa lokacin da Shimr bn Zil-Jawshan, wanda ya kasance daga cikin mafiya gaba da Husaini da kuma Ahlulbaiti (a.s), ya sa baki cikin lamarin da nuna masa cewa matukar ya bar Husaini (a.s) ya fita daga wannan hali da yake ciki, to kuwa zai sake zuwa ya tara karfi da kuma ganin bayan dakarun Umayyawan. Don haka babu wani abin da ya kamata ya aikata face ya bar shi cikin wannan hali da kuma tilasta masa yin mubaya'a da kuma mika wuya ga mulkin Ubaidullah bn Ziyad. Wannan shawara dai ita ce ta canza komai da kuma haifar da wannan mummunan ta'addancin da ya fi kowane ta'addanci cikin tarihi. Ta haka ne dai abubuwan da suka faru cikin tarihi suke fara faruwa saboda daukan wani mataki ko kuma bijiro da wani ra'ayi kamar wannan kalma ta Shimr bn Zil Jawshan, wacce ta taimaka nesa ba kusa ba wajen kisan gillan da aka yi wa Husaini (a.s) da mabiyansa, wacce daga baya ta yi sanadiyyar faduwar gwamnatin zalunci ta Umayyawa da kuma kawo karshenta. Ubaidullah bn Ziyad dai ya amince da wannan shawara ta Shimr, don haka sai ya rubuta wasika ta barazana ya ba wa Shimr din don ya kai wa Umar bn Sa'ad, yana mai umartansa da ya aikata abin da aka ce masa ko kuma ya sauka daga mukamin da aka ba shi ya mika shi ga Shimr bn Zil Jawshan. A cikin wannan wasika dai Ibn Ziyad ya rubuta cewa: "Ni ban tura ka wajen Husaini don ka yi sulhu da shi ko kuma ka lamunce masa ransa ba ko kuma ka nemi uzuri daga gare shi ko kuma ka nema masa ceto daga gare ni ba. Ka gane cewa, idan har Husaini da mutanensa sun yarda suka mika wuya, to ka aiko su zuwa gare ni, idan kuwa har sun ki amincewa da haka, to ka fada musu ka kashe su da kuma lalata jikkunansu, don kuwa sun cancanci hakan. Bayan kashe Husaini ka sanya dawaki su yi sukuwa akan kirgi da kuma bayansa, don kuwa shi dan tawaye ne, ina ganin hakan ba zai kasance mummnan abu ba bayan mutuwa. Wannan dai shi ne abin da nake so ka yi masa, in ka aikata hakan kuwa to za mu saka maka a matsayin mutum mai ji da kuma da'a. Idan kuwa ka ki aikatawa, to ka sauka daga aikinmu ka bar sojojinmu ka mika su ga Shimr bn Zil Jawshan, don kuwa mun riga da mun ba shi ikonmu. Wassalam(6)". Bayan rubuta wannan wasika sai Shimr ya karba ya kama hanya yana cike da sharri da kuma mugunta a cikin zuciyarsa, da isarsa sai ya mika wa Umar bn Sa'ad wasikar da take ba shi zabi biyu, ko ya fada wa Husaini (a.s) da mabiyansa, wanda zai kai shi ga samun mulki da kuma matsayi a wajen magabatansa, ko kuma ya ki aikata hakan ya rasa wannan matsayi, bayan karanta wasikar sai ya amince da zaban duniya da kuma mulki a kan gaskiya da kuma yardar Allah. Daga nan sai ya tsayar zai jagoranci wannan yaki da kuma zubar da jinin Husaini (a.s). Don haka a ranar 7 ga watan Muharram sai Umar bn Sa'ad ya tura sojojinsa da su kange Husaini (a.s) ta bangaren Kogin Furat, wato su shiga tsakanin Iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a) da yadda za su samu ruwan sha, don su mutu cikin kishin ruwa ko kuma su mika kai, hakan dai daya ne daga cikin makircin yaki. Kana kuma ya fara rarraba sojojinsa da kuma nada kananan kwamandoji da za su jagorance su, suna masu matsawa kusa da tantunan Husaini da mabiyansa. Wannan lamari dai na kusantan tantunan Husaini (a.s) ya faro ne daga ranar 9 ga watan Muharram, lokacin da sojojin Umayyawa suka fara daddaga takubba da masunsu cikin fushi da kurari. A daidai wannan lokaci kuwa Husaini (a.s) yana zaune a gaban tantinsa yana kallon wannan hamada ta al-Taf cike da tunanin irin wannan mawuyacin hali da ake ciki da kuma irin abubuwan da zai faru nan gaba ga wannan yunkuri da kuma ma'abuta son gaskiya da 'yanci. A daidai wannan lokaci dai Husaini (a.s) bai san matsayar da Umar bn Sa'ad ya dauka ba dangane da su na kai musu hari, don haka sai ga Zainab ta nufo shi tana mai cewa: "Ba ka ji sautin da ke zuwa kusa-kusa ba". Zainab ba ta bar wannan guri ba, sai ga Abbas bn Ali (a.s), kanin Imam Husain (a.s) ya iso yana cewa: "Ya Dan'uwana, abokan gaba fa sun iso". Nan take Husaini (a.s) ya mike yana ganin ya dace ya yi magana da sojojin Umayyawa don sanin halin da ake ciki, don haka sai ya bukaci Abbas da ya yi magana da su don jin ra'ayinsu. To sai dai kuma ina!, alkawarin mulki da shugabancin da aka musu ya sanya su cikin maye, don haka sai rige-rige suke yi wajen yakan Husaini (a.s) da zubar da jininsa mai tsarki don samun matsayi, mulki da kuma dukiyar da aka yi musu alkawari, don haka amsarsu dai ita ce: "Ko dai Husaini ya mika wuya ga mulkin sarki ko kuma mu yake shi". Daga nan sai Abbas ya komo ya gaya wa Husaini (a.s) matsayar kwamandojin sojin Umayyawan. Don haka dai Imam Husain (a.s) ba shi da wani abin yi in ban da yaki don kuwa ya riga da ya dau matsayar babu ja da baya "Hakika kamata ba zai yi mubaya'a ga mutum kamar Yazid ba", don haka sai ya ci gaba da fadin: "Wallahi ba na ganin mutuwa face sa'ada, rayuwa kuwa tare da azzalumai a matsayin wulakanci". Ya ci gaba kuma da bayyanar da taken nan da ya gada daga Manzon Allah (s.a.w.a), wanda kuma ya bayyanar da shi ga Umayyawa cikin 'yan kwanakin da suka gabata a yankin Al-Baidha': "Ya Ku Mutane! Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: 'Duk wanda ya ga wani ja'irin sarki, wanda ya ke halalta haramun din Allah, mai kwance alkawarin da ya yi, mai saba wa Sunnar Manzon Allah, mai zaluntar bayin Allah, amma ya zuba ido ba tare da ya yi kokarin gyara shi a aikace ko kuma da zance ba, to lalle hakkin Allah ne Ya shigar da shi makomarsa". Imam Husaini (a.s) dai yana ganin mulkin Yazid, siyasarsa da jami'an da suke tare da shi a matsayin misdaki ko kuma hakikanin irin mutanen da Manzon Allah (s.a.w.a) ya ke nufi a wannan kalami nasa, don haka babu wani abin da ya rage masa face shiri don fuskantar wannan makiyi, da kuma daga tutar jihadi da yunkuri don tabbatar da gaskiya da kuma gudanar da shari'ar Allah. Don haka sai ya bukaci Abbas da ya tafi wajen Ibn Sa'ad don neman ya ba su dama ta dare guda don yin tunani kan wannan al'amari da kuma daukar matsayar da ta dace a gobe (Goma ga watan Muharram -Ranar Ashura). Don haka Abbas ya tafi ya shaida wa Ibn Sa'ad wannan bukata ta Husaini (a.s), bayan tattaunawa da kwamandojinsa, ya amince da wannan bukata, shi kuwa Abbas ya koma ya gaya wa Husaini (a.s) abin da ya faru. ____________ (1)- Kamar na sama, shafi na 33. (2)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 227, Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 52, don haka shahadar Imam Husain (a.s) ta kasance ne ranar Juma'a ba ranar Litinin ba kamar yadda da dama suka tafi a kai. (3)- Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafi na 319, Maktal al-Husain (a.s) na Ibn Dawus, shafi na 33, haka nan kuma Shaikh Mufid cikin Al-Irshad, shafi na 232 ya ambato cewa, daga Aliyu bn Husain al-Sajjad (a.s) cewa Imam Husain (a.s) ya kasance yana rera wannan waka daren goma ga watan Muharram. (4)- Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafi na 319, Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 58 da kuma Maktal al-Husain (a.s) na Ibn Dawus, shafi na 34. (5)- Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 52, 53. (6)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 229 da kuma Tarikh al-Ummam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafi na 314.
http://www.5five-stars.com.ng/2019/09/kasar-da-aka-yi-alkawari.html
0 notes
isiyasy · 5 years ago
Quote
Bayan kisan gillan da aka yi wa Halifa na uku, Usman bn Affan, al'umman musulmi sun zabi Imam Ali (a.s) a matsayin halifa, inda suka mika masa ragamar gudanar da mulki da kuma gwamnati. To amma sai Mu'awiyya bn Abu Sufyan ya ki yarda ya mika mubaya'arsa ga halifan da al'umman suka zaba (Imam Ali) yana mai zame kansa da kuma bayyanar da kansa a matsayin halifan Sham wanda da man shi ne gwamnan wannan gari a lokacin halifanci Usman bn Affan. Hakika duk wanda ya karanci tarihin siyasa na wancan lokacin mai tsananin wahala cikin tarihin Musu-lunci, zai ga cewa Imam Ali (a.s) ya fuskanci wasu manyan barazana guda uku na siyasa, su ne kuwa: 1- Barazanar Umayyawa karkashin jagoranci Mu'awiyya bn Abi Sufyan. 2- Barazanar Khawarijawa wadanda suka fice daga cikin rundunar Imam Ali (a.s) da kuma yi masa tawaye. 3- Barazanar A'isha(1), Dalha da kuma Zubair bn Awwam. Bayan wani lokaci na yaki da kuma cacan baki tsakanin Imam Ali (a.s) da wadannan kungiyoyi da jam'iyyu na siyasa, Imam Ali (a.s) ya sami nasarar gamawa da barazana kungiyar A'isha, Dalha da kuma Zubair a yakin nan da aka fi sani da "Yakin Jamal" (Rakumi) wanda ya abku a garin Basra. Haka nan kuma ya sami nasara a kan Mu'awiyya a "Yakin Siffin", lamarin da ya kare ta hanyar yin sulhu amma Imam Ali (a.s) ya ki yarda da hakan bayan da ya fahimci cewa wannan sulhun ba wani abu ba ne face kawai yaudara ta siyasa da Mu'awiyya da 'yan koransa suka tsara, lamarin da ya haifar da kungiyar Khawarijawa da kuma ballewarsu daga bangaren Imam Ali. Daga baya kuma suka yi fito-na-fito tsakaninsu a "Yakin Nahrawan", inda Imam Ali (a.s) ya sami nasarar tarwatsa su. A daidai lokacin da ake cikin wannan rikici na siyasa da kuma zubar da jini, Khawarijawa, wadanda daman tuni sun bayyanar da adawa da kuma tawayensu ga Shugaban Musulmi Imam Ali (a.s), sun tsara wani tsari na kashe Mu'awiyya, Amr bn al-Aas da kuma Imam Ali bn Abi Talib (a.s), ta haka ne duniya za ta rasa daya daga cikin mafiya daukakan mutanenta, madaukin tutar tabbatarta, ma'abucin ilmi, jihadi da ayyuka na kwarai, wato Imam Ali bn Abi Talib (a.s). Wanda kuwa ya dauki nauyi gudanar da wannan mummunan aiki da kuma yin kafar ungulu wa tarihin dan'Adam shi ne Abdul-Rahman bn Muljam, inda ya kashe Amirul Muminina Ali bn Abi Talib (a.s) ta hanyar sararsa da takobi mai guba a kansa a yayin da yake sallar Asuba a masallacin Kufa ranar 19 ga watan Ramalana shekara ta 40 bayan hijira, kana kuma ya yi shahada a ranar 21 ga wannan watan na Ramalana. Da wannan shahada ta Amirul Muminina Ali (a.s), wanda ya kasance shugaban gwamnati, jihadi da kuma siyasa, mutum mai riko da gaskiya da akida, wanda ya ba da dukkan karfinsa wajen tabbatar da adalci da daidaituwa, wanda ba ya taba yin sassauci a kan gaskiya ko kuma yin sako-sako da akida, al'amurra daban-daban na siyasa da kuma sabbin abubuwa suka kunno kai, haka nan kuma aka haifar da wani sabon yanayi cikin tarihi. An jujjuya al'amurra, an dagula al'amurran siyasa da zamantakewar al'umma, an shigar da wasu al'amurran da ba su dace ba cikin lamarin halifanci, haka nan kuma Mu'awiyya ya ci gaba da fadada mulkinsa da ikon da ya ke da shi. Duk da irin imanin da al'umman musulmi suke da shi kan girma da daukakar Imam Hasan (a.s) da kuma irin tsarki da matsayinsa na siyasa da zamantakewa wanda babu wanda ya mallake su a wancan lokacin, hakan nan kuma duk da irin bayyanar da matsayinsa da Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi cikin nassosi da hadisansa da kuma wasiyyar da mahaifinsa Imam Ali (a.s) ya yi da kuma mubaya'ar da al'umma suka yi masa a matsayin halifa bayan mahaifinsa, duk da wadannan abubuwa, to amma shahadar Imam Ali (a.s) ke da wuya, sai Mu'awiyya ya sanar da kansa a matsayin halifan musulmi. Bayan haka kuma ya rubuta wa Imam Hasan (a.s) yana bukatarsa da ya sauka daga matsayin da al'umma suka dora masa na jagorantarsu, yana mai masa barazanar yakansa matukar ya ki yarda da hakan. Hakika tarihi ya kiyaye mana dukkan wadannan wasiku guda biyu, wato wasikar da Mu'awiyya ya rubuta wa Imam Hasan bn Ali (a.s) da kuma amsar da shi Imam Hasan din ya rubuta masa. Ga wasikar da Mu'awiyyan ya rubuta wa Imam Hasan (a.s) yana bukatarsa da ya saukar daga karagar halifancin musulmi: "Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai. Bayan haka, hakika Allah Madaukakin Sarki Yana yi da bayinSa yadda Ya so, kuma babu wanda ya isa ya yi jayayya da hukumcinSa, kuma Shi mai saurin yin hisabi ne. Ka yi hankali kada mutuwarka ta kasance a hannun mafi muguntar mutane, kuma ka bar tunanin za ka samu rauni a tattare da mu. Lalle matukar dai ka bar abin da kake kai, kana kuma ka yi min mubaya'a, to lalle zan cika maka alkawarin da na yi maka kuma zan ba ka abin da ka bukata. Kuma zan kasance kamar yadda A'sha bn Kais bn Tha'alabah ya bayyana (cikin baitoci): Idan wani ya baka amanar wani abu, Ka mayar masa, bayan mutuwarka za a kira ka amini. Kada ka yi hassada wa shugabanka in yana cikin wadata, Kada ka kaurace masa, idan ya talauce. Bayana halifanci zai kasance naka ne, don kuwa kai ne kafi dacewa da shi daga dukkan mutane. Wassalam". Daga nan sai Imam Hasan ya rubuta masa amsa yana mai cewa: "Bayan haka: wasikarka ta iso hannuna kana mai ambaton abin da ka ambata a cikinta. Ban ki amsa maka wasikar taka ba ne don kada in kasance ban maka adalci ba, Allah Ya tsare ni daga hakan. Ina kiranka da bin gaskiya za ka gano cewa ni ma'abucinta ne, lalle zan dauki alhakin abin da na fadi idan har karya ne, Wassalam(2)". Imam Hasan (a.s) dai bai amince da wannan bukata ta Mu'awiyya ba na ya sauka daga halifancin da al'umma suka dora masa ba, face ma dai yana ganin wajibcin ci gaba da rike wannan nauyi na jagorantar al'umma. Don haka sai ya fara shirya dakaru don yakan Mu'awiyya da kuma kare Musulunci daga sharrinsa, to sai dai kuma alamun nasara suna komawa ne ga bangaren Mu'awiyyan saboda ha'incin da wasu kwamandojin Imam Hasan din suka nuna saboda sayensu da Mu'awiyyan ya yi da dai sauran dalilai. Don haka Imam Hasan (a.s) ya kasance ba shi da wata mafita face ya yi sulhu da Mu'awiyya don kare zubar da jinin musulmi da kuma kare Musulunci wanda yake fuskantar barazanar bakin haure (daular Rum) da abokan gaba wadanda da man suke jiran faruwar hakan. Don haka sai ya yi sulhu na wani lokaci don ko yanayi zai dawo yadda ya kamata bayan mutuwar Mu'awiyya don ya samu damar yin gyara da kuma dawo da al'amurran yadda suke. Ta haka ne Imam Hasan (a.s) ya bar wannan hakki nasa, ya yi sulhu da Mu'awiyya kan wasu lamurra kamar yadda tarihi ya ruwaito mana su: 1- Wannan shi ne sulhun da aka yi tsakanin Hasan bn Ali bn Abi Talib da kuma Mu'awiyya bn Abi Sufyan, kan cewa Hasan bn Ali zai bar halifancin musulmi ga Mu'awiyya bisa sharadin zai yi aiki da littafin Allah da kuma sunnar Manzon Allah da kuma tafarkin shiryayyun halifofi, kuma cewa Mu'awiyya ba zai nada wani a matsayin halifa ba bayansa(3). 2- Kan cewa Hasan shi ne zai kasance halifa bayansa (Mu'awiyya)(4), idan kuma wani abu ya same shi to dan'uwansa Husaini ne zai kasance halifan(5). 3- Kan cewa (Mu'awiyya) ba zai bukaci wani abu akan mutanen Madina, Hijaz da Iraki kan yadda suka kasance lokacin halifanci Imam Ali ba(6). 4- Kuma jami'an gwamnatin Mu'awiyyan ba za su la'anci Imam Ali a kan mimbarorinsu ba haka nan kuma ba za su fadi muggan kalmomi akansa ba da kuma yin kunuti(7) a kansa ba. 5- Mutane za su kasance cikin aminci a duk inda suke(8). 6- Mu'awiyya ba shi da ikon sarrafa kudin da ke cikin Baitul Malin birnin Kufa, ikon sarrafasu yana hannun Imam Hasan (a.s) ne. 7- Mu'awiyya ba zai yi kokarin cutar da Hasan da Husaini ba, haka nan ma mabiyansu. Haka nan aka rubuta wannan sulhu kuma dukkan bangarorin biyu suka sanya hannu da kuma yarda da shi. To amma jin kadan da gama yarda da wadannan sharud-dan sulhun (bayan da ya dawo cikin mabiyansa) sai Mu'awiyya ya tashi a gabansu yana mai cewa: "Hakika na yi alkawarin ba wa Hasan wasu abubuwa kuma na ba shi, to sai dai dukkan wadannan abubuwa a yanzu suna karkashin tafin kafata ne kuma ba zan cika ko da guda daga cikinsu ba(9)". Ta haka ne shiryayyiyar halifanci ta kawo karshe ta hanyar saukar Imam Hasan (a.s) daga halifancin, inda ya komo birnin Madina bayan halifanci na watanni shida bayan babansa Imam Ali (a.s). Daga nan sai Mu'awiyya ya shiga garin Kufa tare da sojojinsa yana mai cewa: "Ya ku mutanen Kufa! Shin kuna ganin na yake ku ne don in tilasta muku yin salla, ku ba da zakka ko kuma ku je hajji, alhali kuwa na riga da na san kuna salla, kuna fitar da zakka kana kuma kuna zuwan hajji. Lalle ni na yake ku ne don in samu iko a kanku, kuma Allah Ya ba ni hakan alhali kuwa ku ba kwa so. Haka nan duk wata dukiya ko jinin da aka zubar a yayin wannan fitina sun zama ba a bakin komai ba, haka nan kuma dukkan wani sharadi da aka tsayar za su kasance ne a karkashin kafafuna ne wadannan(10)". Hakika da wannan jawabi Mu'awiyya yana so ne ya kafa wani karfafaffen shinge na fada da Imam Hasan (a.s) kamar yadda ya zo cikin bayanin nasa cewa: "Dukkan wani sharadi da aka tsayar za su kasance ne a karkashin kafafuna ne wadannan". Hakika babu wani abin da ya saura wa Mu'awiyya in ban da wasu 'yan kwanaki, inda ya fara gudanar da wasu abubuwa da suka saba wa wannan yarjejeniya ta sulhu da aka cimma. Wadannan tsare-tsare nasa kuwa na gaba (da Imam Hasan) suna nan ne kamar haka: 1- Gudanar da ta'addanci da cutarwa ga duk wani mutum ko kuma wata al'umma da take adawa da mulkin mulukiyyar Umayyawa musamman ma mabiya Imam Ali (a.s), da kuma amfani da duk wata hanya wajen rufe bakin duk wani dan adawa. Hakika, mai karatu, na iya gane yadda wannan lamari ya kai da baci ne cikin wannan wasiyya da Mu'awiyya ya aika wa daya daga cikin kwamandojin sojojinsa. Mu'awiyya ya aika masa da cewa: "Ka kashe duk wani mutumin da ka ci karo da shi wanda ya saba wa ra'ayin da kake kai, kana kuma ka ruguza duk wani kauye da ka bi ta cikinsa, ka lalata dukiya, don kuwa lalata dukiya tana daidai da kisan gilla, kai tafi hakan ma cutar da zuciya(11)". To wannan dai shi ne tsare-tsare da kuma dabi'ar Umayyawa, kamar yadda ya zo cikin wannan nassi da ya gabata, wanda kuma tun zamanin halifanci Imam Ali (a.s) suka tsara su, sai dai kuma sun fara gudanar da su ne cikin irin wannan mummunan yanayi na zubar da jinin bayin Allah da ba su ci ba su sha ba musamman mabiya Imam Ali (a.s). Har ila ya zo cikin wata wasika da Mu'awiyya ya rubuta wa gwamnoninsa da suke dukkan jihohin da suke karkashinsa cewa: "Ku duba ku ga duk wani wanda hujja ta tabbata a kansa cewa yana son Ali da Ahlulbaitinsa, to ku cire sunansa daga cikin diwani, ku hana shi abin da ake ba wa mutane(12)". Haka nan kuma ya zo cikin wata wasikar da ya rubuta cewa: "Duk wanda kuka zarga da yin biyayya ga wadannan mutane (Ahlulbaiti) to ku yi awun gaba da shi, kana kuma ku ruguza gidansa(13)". Imam Muhammad Bakir (a.s) ya bayyana irin wannan danyen aiki da cin zali cikin wannan bayani, inda ya ke cewa: "Suna kashe 'yan shi'anmu a dukkan garuruwa, sukan gutsure hannuwa da kafafu saboda zato kawai. Akan sanya duk wanda aka zarga da sonmu da komawa gare mu cikin gidajen yari, ko kuma a kwace dukiyarsa, ko kuma a ruguza gidansa, haka lamari ya ci gaba da baci da kuma karuwa har lokacin Ubaidullah bn Ziyad wanda ya kashe Imam Husaini (a.s)(14)". Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu cikin wannan zalunci da ayyukan ta'addanci mai tada hankali har da wasu sahabbai tsarkaka, irin su: Hijr bn Adi da al'ummarsa, Rashid al-Hijri, Amru bn al-Humk al-Khuza'iy, Awfa bn Husn da dai sauransu masu yawa. Mai son karin bayani kan irin wannan danyen aiki na Mu'awiyya da mutanensa sai ya koma cikin Tarihin Tabari, al-Kamil, Sharh Nahjul Balaga da dai sauransu. 2- Tattara dukiya da nufin sayan lamiran mutane don cin mutumcin gwarazan Musulunci da kuma yada bakar siyasa kaucacciya don cimma burinsu. Akwai nau'i biyu na mutanen da aka saye su a wancan lokacin don cimma wannan buri: (a)- Su ne malamai masu wa'azi da kuma tara hadisan Ma'aiki, wadanda suka ba da gagarumar gudummawa wajen kirkiro hadisan karya da kuma jingina su ga Ma'aikin Allah (s.a.w.a), wadanda babu bukatar sai mun kawo su a nan. (b)- Wasu masu fadi a cikin al'umma, wadanda ake jin tsoro tasirinsu matukar suka kirayi mutane wajen yin tawaye wa masu mulkin Umayyawa, wannan kuwa wani sanannen abu ne da aka san Mu'awiyya da shi da kuma mabiyansa. Misali kuwa shi ne makudan kudaden da Mu'awiyya ya aika wa Malik bn Hubaira al-Sukuni a matsayin cin hanci lokacin da labari ya zo masa cewa yana nuna rashin jin dadinsa da kisan gillan da Mu'awiyyan ya yi wa sahabin nan Hijr bn Adi da sahabbansa (r.a), da dai sauran irin wadannan misalai masu yawa. 3- Takunkumin tattalin arziki da kuma sauran nau'oi na cutarwa: Wannan yana daga cikin mafi muni da cutarwar tafarkin da Umayyawa suka dauka akan al'umma. Bisa la'akari da cewa wannan siyasa da muka ambata ta ginu ne akan fada da duk wani karfi da ke adawa da masu mulki na wancan lokacin (Umayyawa), don haka Mu'awiyya ya zabi mafi munin tafarki wajen takura wa mabiya Ahlulbaiti (a.s) kamar yadda tarihi ya tabbatar da haka. Daga ciki kuwa har da umarnin da ya aike wa gwamnoninsa kan cewa; "Ku duba ku ga duk wani wanda hujja ta tabbata a kansa cewa yana son Ali da Ahlulbaitinsa, to ku cire sunansa daga cikin diwani, ku hana shi abin da ake ba wa mutane". Yana da kyau mu yi tunani kan wannan mummunar siyasa wacce Umayyawa suka dauka, na lalata lamirin mutane da kuma sayansu da abin duniya, wacce babu shakka ba karamin abu ba ne kuma ba wani abu ne na dan karamin lokaci ba, face dai lamari ne da ya ci gaba tsawon shekaru, wanda ya lalata yanayin siyasa da zamantakewar al'umma. 4- Lalata dabi'un al'umma da kuma haifar da ruhin kabilanci, 'yan garanci da dai sauransu tsakanin al'umma da wannan ja'irar hukuma ta Umayyawa ta yi, lamarin da ya haifar da rikice-rikice da fadace-fadace. Misalin irin rikicin da ya barke tsakanin mutanen Yaman da Madina, ko kuma rikicin da ya faru tsakanin kabilun Iraki, da kuma wutar nuna banbanci da kiyayya da ta kunno kai tsakanin musulmi larabawa da wadanda ba larabawa ba, abin da tarihi ya kira shi da sunan Al-Mawali. Lalle ana iya ganin tasirin wannan bakar siyasa cikin wakokin Al-Darami, al-Farazdak, Jarir, al-Akhtal da dai sauransu(15). 5- Kisan gillan da aka yi wa Imam Hasan (a.s) a matsayinsa na mutum mai wakiltan tsarkakakken Musulunci a duniyar musulmi. Hakika al'umma sun riga da sun fahimci kuma ma suna ji a jikinsu cewa lalle fa har ya zuwa yanzu fa jinin Imam Husaini, jikan Manzon Allah (s.a.w.a) da aka zubar a Karbala yana nan yana gudana, haka nan kuma suna jin cewa babu wani abin da zai zama kaffara na wannan jini da kuma zaluncin da aka yi wa iyalan gidan Manzo in banda daukar fansa da kuma raya wannan yunkuri na Imam Husaini (a.s). Ta haka ne aka haifar da yunkurin Al-Tawwabun, jinin Imam Husaini (a.s) shi ne ya kasance wani abin da ya motsa jigon gwamnatin Umayyawa da kuma ka da shi. 6- Nadin da Mu'awiyyan ya yi wa dansa Yazid a matsayin halifan musulmi cikin tursasawa, barazana da kuma ba da cin hancin, sabanin yarjejeniyar da aka cimma tsakaninsa da Imam Hasan (a.s) na cewa ba zai nada wani a matsayin halifa ba bayansa in ba Imam Hasan din ba ko kuma Imam Husaini (a.s) idan har Hasan din ya rasu kafin wannan lokacin. Ta haka ne Mu'awiyya ya gama tsare-tsarensa na yin karen tsaye ga dukkannin sharuddan da aka tsayar a yayin yarjejeniyarsu da Imam Hasan ta sulhu, da kuma karen tsaye ga dukkan dokoki da kuma tsare-tsare da Musulunci ya tafi a kansu bugu da kari kuma kan gudanar da mulkin danniya da baba-kere, lamarin da ya sanya tsarin siyasar Musulunci cikin mawuyacin hali da kuma lalacewa, bugu da kari kan bakanta tarihin Musulunci. Hakika wannan karen tsaye wa dokokin Musulunci da Umayyawan suka tsara ma ya dada fitowa fili ne lokacin da Mu'awiyya ya nada dansa Yazid, wanda aka san shi da wargi da kuma aikata dukkanin sabo, a matsayin jagoran al'umman musulmi. Babu shakka, mika wa Yazid ragamar mulkin al'ummar musulmi da kuma tsara mata tafarkin da za ta bi, yana nufin ruguza kasantuwan Musulunci ne da kuma dokokinsa a aikace da kuma kowama zuwa ga jahiliyya, amma a wani tufafi na daban. Don kuwa shi wannan Yazid din - kamar yadda tarihi ya tabbatar - mutum ne maras dabi'u na kwarai, wanda kuma ba shi da wata masaniya kan dokokin Musulunci, wanda ya gudanar da dukkan rayuwarsa cikin wargi da munanan aiki na jahiliyya da ko kare ba zai iya cinsu ba saboda muni. Don haka ba abin mamaki ba ne idan Yazid ya yi kokarin lalata yanayin tarbiyyan al'ummar musulmi da Musulunci ya koyar da su. Hakika tarihi ya tabbatar mana da yadda wannan lalataccen da na Mu'awiyya yake gudanar da rayuwarsa a Sham, rayuwar da ke cike da wargi, caca, shan giya, wasa da birrai, neman mata, sauraron kide-kide da raye-raye da dai sauran nau'oi na sabon Allah(16). Yayin da yake ishara da irin wadannan halaye na Yazid, Al-Baladhuri yana cewa: "Yazid ya kasance yana da wani biri da yake tare da shi, ya kan kira shi da Abu Kais. Ya kasance yakan ce: Wannan dattijo ne daga cikin dattijan Bani Isra'ila da aka shafe saboda laifin da ya yi". Ya kasance ya kan sayar da shi wani nau'i na giya yana dariya kan yadda yake ni yayin da ya bugu...(17).". Haka nan Ibn Athir ma yana cewa: "An ruwaito cewa Yazid mutum ne da ya shahara da kide-kide, mashayin giya, mai wasa da maza, birrai da karnuka….babu yadda za a yi garin Allah ya waye face yana cikin maye...(18)". Al-Mas'udi ma cewa yake: "Yazid ya kasance ma'abucin kide-kide, wasa da dabbobin da ake farauta da su, karnuka da birrai, haka nan kuma mutum ne da ya shahara da shan giya….. "Ayyukan fasikancin da Yazid yake aikatawa ya yi tasiri akan abokai da da masu masa hidima, a lokacinsa ne kide-kide suka shiga Makka da Madina, haka nan kuma mutane suka dinga bayyana shan giya a fili. Ya kasance yana da wani biri da ya sa masa suna Abu Kais, ya kan tawo da shi fada, ya sanya masa mimbari, ya kan dora shi a kan doki ana yin gasa da shi. Ya kan sanya wa wannan biri alkyabba da aka yi ta da hariri, sannan kuma ya sanya masa hula wacce aka yi ta da zaren hariri mai launuka daban-daban....(19)". Hakika wannan lamarin dai bai tsaya a nan ba, kamar yadda kuma yakin da Umayyawa suke yi da Ahlulbaiti (a.s) wanda ya samo asali tun farkon Musulunci bai kare ba. Lalle Imam Hasan da Husaini (a.s) sun kauce wa fagen siyasa a aikace, to amma duk da haka Mu'awiyya da mabiyansa sun ci gaba da cin mutumcin Ahlulbaiti da mabiyansu har lokacin da Imam Hasan (a.s) ya yi shahada kana kuma al'umma suka juya kan Imam Husaini (a.s) da kuma yi masa mubaya'a don ya jagoranci ganin bayan wannan lalatacciyar hukuma ta Umayyawa. Mu'awiyya dai yana da wani abu a zuciyarsa, wannan abu kuwa shi ne yana son dora dansa Yazid a matsayin halifan musulmi a bayansa kana kuma ya karba masa mubaya'ar al'umma da kansa sabanin abin da shari'ar Musulunci ta tsayar wajen zaban halifa. Lalle wannan kuduri na Mu'awiyya ya tada hankulan al'umman musulmi musamman ma sanannu daga cikinsu irinsu Imam Husaini (a.s), Abdurrahman bn Abubakar, Abdullahi bn Zubair, Abudllahi bn Umar da dai sauran sanannu mutanen wancan lokacin. Babu shakka tarihi ya nakalto mana irin nuna rashin amincewa da aka nuna da wannan matsaya, ga kadan daga ciki: "A shekara ta hamsin bayan hijira, musulmi sun sami nasarar kame Kuhistan, don haka a lokacin sai Mu'awiyya ya kirayi mutane Sham da su yi mubaya'a wa Yazid a matsayin halifa bayansa, inda suka amsa masa suka yi mubaya'ar. Don haka Mu'awiyya ya zamanto mutum na farko da ya nada dansa halifa, kana kuma na farko da ya nada halifan da zai gaje shi yana cikin koshin lafiyarsa. Daga nan sai ya aika da wasika zuwa ga Marwan wanda ya ke shi ne gwamnan Madina kan ya karbi bai'ar mutane ga Yazid a maimakonsa, yana mai ce masa: "Amirul Muminina ya yanke zai nada dansa Yazid a matsayin jagoranku (halifa) daidai da sunnar Abubakar da Umar", nan take sai Abdurrahman bn Abubakar al-Siddik ya mike ya ce: A'a hakan sunnar Khosro da Kaisar ne dai, don kuwa Abubakar da Umar ba su nada 'ya'yayensu halifa ba, ko kuma daya daga cikin mutanen gidansu ma ba". Haka nan kuma a shekara ta hamsin da daya, Mu'awiyya ya yi aikin hajji, inda ya karbi bai'a wa dansa Yazid. Daga nan sai ya aika a kira masa Ibn Umar yana mai ce masa: "Ya Ibn Umar, ka kasance kana gaya min cewa ba ka son ka kwana alhali ba kana karkashin ikon wani shugaba ba, don haka ina gargadinka da kada ka haifar da rarrabuwa ko kuma yada fasadi tsakanin al'umma". Jin haka sai Ibn Umar ya gode wa Allah ya ce: "Bayan haka, hakika kafinka an yi halifofi wadanda suke da 'ya'yaye, kuma danka bai fi nasu 'ya'yan ba, amma ba su wa 'ya'yansu abin da ka yi wa naka dan ba (nada shi halifa), to amma su sun zaba wa musulmi ne abin da yafi musu alheri. Ka gargade ni da kada in shuka tsiron rarrabuwa tsakanin musulmi, lalle ba zan yi haka ba, don ni na kasance daya daga cikin musulmin, idan har sun tafi a kan wani abu ai ni ma daga cikinsu nake (zan yarda da shi)". Sai Mu'awiyya ya ce masa, Allah Ya yi maka rahama. Daga nan sai Ibn Umar ya fita ya yi tafiyarsa. Daga nan kuma sai ya aika a kira masa Ibn Abubakar, ko da ya iso sai ya fara gaya masa wannan bukata tasa ta nada dansa a matsayin halifa, sai Ibn Abubakar ya katse shi yana mai cewa: "Wallahi ba za mu taba yarda da haka ba, don Allah, ka mayar da wannan al'amari tsakanin mutane su zabi wanda suke so, ko kuma mu tilasta maka yin haka", sai ya fice. Sai Mu'awiyya ya ce: Ya Allah! Ka isar min a kansa da abin da Ka so, sai ya ci gaba da cewa: "Ya kai wannan kada ka gaya wa mutanen Sham (Siriya) abin da ya faru, don ina tsoron za su fada maka, ka hakura har sai da maraice lokacin da zan gaya musu cewa ka yi mana bai'a, daga nan sai ka yi duk abin da kake son yi". Sai ya aika a kira masa Ibn Zubair, ya ce masa: "Ya Ibn Zubair, hakika kai ba ka kasance ba face kamar dila mai wayo, ka shiga nan ka fita ta can, kai ne ka sanya wadannan mutane biyu suka canza ra'ayinsu. Sai Ibn Zubair ya ce: " Idan har ba ka son shugaban-cin ne to ka sauka, idan har muka yi mubaya'a wa danka, to a cikinku ku biyun wane ne za mu saurara da kuma yi masa da'a? Don kuwa ba abu ne mai yiyuwa ba mu yi mubaya'a gare ku ku biyun". Sai ya tashi ya fita: Sai Mu'awiyya ya hau kan mimbari, ya gode da kuma tsarkake Ubangiji sai ya ce: "Hakika maganar da mutane suke yi mai cutarwa ta iso gare mu, suna cewa Ibn Umar, Ibn Abubakar da Ibn Zubair ba za su taba yin mubaya'a wa Yazid ba, to amma tuni sun riga da sun saurara masa kana kuma sun mika mubaya'arsu gare shi". Sai mutanen Sham suka ce: "Wallahi ba za mu amince da hakan fa face sai sun yi mubaya'ar a gaban mutane, in ba haka ba kuwa mu sare kawukansu". Sai ya ce: "Godiya ta tabbata ga Allah! Kan yadda mutane suka gaggauta nufan Kuraishawa da sharri, kada in sake jin wannan zance daga bakinku daga yau". Sai ya sauka. Sai mutane suka fara cewa: "A'a ashe Ibn Umar, Ibn Abubakar da Ibn Zubair sun yi mubaya'a wa Yazid su kuma suka ce wa mutane: wallahi ba mu yi hakan ba, mutanen kuma suka ce: a'a kun yi mana. Daga nan sai Mu'awiyya ya tashi ya tafi(20)". Ta haka ne al'umma ta fada cikin wannan tsaka mai wuya na tarihin rayuwarta, ta kasance babu komai a gabanta face zabi biyu: Ko dai ta ki amincewa da wannan abu da ke fuskan-tarta koma dai me ya tafasa ya kone, ko kuma ta amince da wannan wulakanci da jifa da abin da Musulunci ya tafi a kai. To ya ya lamarin ya kasance? ____________ (1)- A'isha dai ita ce matar Annabi (s.a.w.a) kana kuma 'ya ta ke ga halifa na biyu Abubakar bn Abi Kahafa. (2)- Makatil al-Talibin na Abul Faraj al-Isfahani, shafi na 59. (3)- Al-Fusul al-Muhimma na Ibn Sabbagh al-Maliki, shafi na 163. (4)- Tarikh al-Khulafa' na Jalaluddeen Suyuti, shafi na 191. (5)- Sulh al-Hasan na Shaikh Radhi Al' Yasin, shafi na 260, yana mai nakaltowa daga littafin Umdatul Talib. (6)- Tarikh al-Khulafa' na Jalaluddeen Suyuti, shafi na 191. (7)- Wato ba za su dinga yin munanan addu'oi a kansa ba, saboda a wancan lokaci Mu'awiyya da jami'ansa sun kasance suna zagi da fadan munanan kalmomi ga Amirul Muminina Ali (a.s) a gaban jama'a bayan an idar da salla. Haka nan kuma sun kasance sukan ba da kyauta ga duk wanda yake zagin Imam Alin (a.s). Dubi Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 3, shafi na 414 da kuma 472, da kuma Sharh Nahjul Balagah na Ibn Abil Hadid, juzu'i na 3, shafi na 56-63. (8)- Al-Fusul al-Muhimma na Ibn Sabbagh al-Maliki, shafi na 163. (9)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 191. (10)- Sharh Nahjul Balagah Ibn Abil Hadid, juzu'i na 16, shafi na 15. (11)- Kamar na sama, juzu'i na 2, shafi na 86. (12)- Kamar na sama, juzu'i na 11, shafi na 45. (13)- Kamar na sama. (14)- Kamar na sama, shafi na 43. (15)- Thauratul Husainiyya na Muhammad Mahdi Shamsuddin, shafi na 61 zuwa sama. (16)- Al-Imam Husain na Abdullah al-Alayili, shafi na 345. (17)-Ansab al-Ashraf na Baladhuri, juzu'i na 4, shafi na 1 da 2. (18)- Al-Bidaya wan Nihaya na Ibn Athir, juzu'i na 8, shafi na 236. (19)- Muruj al-Zahab wa Ma'adin al-Jawhar na Al-Mas'udi, juzu'i na 3, shafi na 67 da 68. (20)- Tarikh al-Khulafa' na Jalaluddeen al-Suyuti, shafi na 196 da kuma 197.
http://www.5five-stars.com.ng/2019/09/wani-bangare-na-gwagwarmayar-husaini-as.html
0 notes