#5Five Stars Media posted →Karbala
Explore tagged Tumblr posts
isiyasy · 5 years ago
Quote
Uwar yazidu dai itace "MAISUN" yar Bajdal Al-kalbiyya, kuma mu'awiyya ya Aureta ne tana kafira, sai bawansa yayi mata ciki ta haifi yazidu (l.a), hakan tasa mu'wiyya ya saketa ta tafi da tsinannen yaron can dangin mahaifanta Arna,  ya girma a can. saboda haka yazidu shege ne da duk ma'anar shegantaka. Yazidu (l.a) ya hau mulki ne bayan mutuwar babansa MU'AWIYYA (l.a) a shekara ta 60. Yazidu (l.a) yayi mulki ne na shekaru uku da wata 8. Ga yadda mulkin nasa ya gudana: A shekarsa ta farko ya tura rundunoni suka kashe IMAMU HUSAIN (AS), da sauran zuriyar manzan Allah (saww), kuma suka tsire kawukansu a masu suna zagayawa dasu gari gari, yara da mata kuwa suka dauresu a matsayin fursunonin yaqi.  inna lillahi..... A shekarar mulkinsa ta biyu kuma ya tura rundunoni a karkashin wani shege wai shi MUSLIM wanda malaman tarihi ke kiranshi da "MUSRIF" suka je madina suka yayyanka sahabban manzan Allah (s.a.w.a) fiye da dubu hudu, domin sun nuna kin yardarsu da mulkin yazidu, kuma suka yiwa mata fyade a cikin masallacin manzan Allah (saww), kuma suka dinga shafe maniyyi da Takardun Alkur'ani, inna lillahi...     haka kuma sun daure dawakai akan kabarin manzan Allah (saww) dawakan suka yi fitsari da kashi akan kabarin manzan Allah (s.a.w.a)inna lillahi wa inna ilaihi raji'uun!! Bayan Waqi'ar da shekara daya malaman Tarihi suka ce akalla saida aka haifi jarirai dubu da ba'asan mahaifansu ba. inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!! wannan itace ake kira WAQI'ATU HARRA wacce ta shahara a tarikhi, sunna da shi'a. A shekara mulkinsa ta uku kuwa ya harbi KA'ABA, da majajjawa ya kona sattarar ka'abar ta kone kurmus. MUTUWAR TSINANNEN... A shekarar mulkinsa ta hudu kuwa ya kama hanya da nufin zai je makka ya hau kan dakin Allah yasha giya yayi rawa. yana cikin tafiya ne tare da fadawansa, sai ya hangi Barewa a cikin daji, sai ya bita da nufin zai kamota domin dama ya saba yin farauta, haka yabar fadawansa ya bi barewar akan dokinsa yana gudu barewar na kara yi masa nisa,haka- haka har barewarta bace masa a cikin sahara, ya juyo zai dawo hanya ta bace masa, ya rasa inda zai je, Qishi ya dame shi gashi ba gida gaba ba gida baya,  can sai ya hangi wata Bukka a cikin dajin, yana zuwa sai ya taradda wani tsoho a ciki da Tulun ruwansa mai sanyin gaske irin wanda mai Qishi ke bukata. sai yace da tsohon ya bashi ruwa ya sha, sai tsohon yace A'a, ni ruwana ba na sha bane, Yazidu yace to ka siyar min ko nawa ne zan siya, Tsohon yace ruwa na ba na siyarwa ba ne, sai yazidu yace: Halan baka san Ni ko waye ba ne da zaka yiman wannan rashin kunyar,!? Nine fa Sarkin musiulmi YAZIDU DAN MU'AWIYYA!! Yana fadin haka sai tsohon yace Inna lillahi wa inna ilaihi raji'uun!!   dama kai ne Yazidu dan mu'awiyya makashin IMAMU HAUSAIN!??  sai tsohon ya dauko sanda zai bugi yazidu, sai dokin yazidu ya tsorsta ya zabura da karfi ya sukwana tare da yazidu, haka dokin yayi ta gudu babu kama hannun yaro, can!! sai Yazidu ya zame ya fado akan dokin amma sai kafarsa ta maqale a cikin likkafar dokin, haka dai dokin yayi ta gudu, yana lilo da jikin tsinannen Allah, har kan yazidu ya cire, Qirjinsa ya fita, cikinsa ya fashe hanjinsa suka zubo, haka - haka har duk jikinsa ya  qare a cikin daji. Gari kuwa sai kuka, ana neman sarki bai dawo ba. can sai ga doki ya dawo da guntun kafar yazidu a cikin likkafar doki, jikin tsinannen kuwa ya zama abincin kuraye idan dare yayi. wannan shine karshen Yazidu dan mu'wiyyya (l.a) , wato ya mutu ne bayan kashe Imamu Husain (as) da shekare uku da wata biyu da kwana hudu dai dai. Mai son yayi bincike kan ta'addancin yazidu da aka Ambata musamman ma na WAQI'ATUL HARRA" Yaje ya duba TARIKHU DIMASHK na babban malamin sunna wato IBNU ASAKIR,  juzu'i na 27 shafi na 19,  da kuma Juzu'i na 34 shafi na 287. Allah zai cika hasken sa ko da ka firai da munafukai sun ki.
http://www.5five-stars.com.ng/2019/10/mutuwar-yazidu-dan-muawiyya-la.html
0 notes
isiyasy · 5 years ago
Quote
haqiqa kun karanta wannan kal mar kullu yaumen ashura wa kullu ardhin kharbala. wanna kalmace ta tar bubiyya. Bamuna nufin ma'anarta shine ko wanne rana Karbala ba. kuyi kuka. ku duba kugani wanne irin fagene yayi kama da zaluncin da akayiwa iyalen gidan annabi a karbala? wannan fagen na zalunci Sa mam-mene ako wanne rana ako wacce kasa.  shine na fada tsa kanin Musulunci da kafirci shine fafatawa tsakanin tsakanin adalci da zalunci. shi wannan Sa mam mene akowacce qasa da kowacce rana.  kada qarancin rundunar muminai yasa kuji tsoron fiskantan rundu nar kafirai da batada imani.  kada kuji tsoron karancin yawa ko rashin nasara afagen fiskantar azzalumai yayin da aiki ya zama ana yinsa saboda Allah. to babu wata asara atattare da shi Dazaa kashe mutum awannan fagen shada yayi kuma yana cikin en Aljanna. Allah ya kiyaye dukkan yan uwa Baki daya mumasu yin hidima agarekune wannan wasu kala maine na margayi imam Khomeini (k).  To Alhmdu lillah Al'amarin tattaki yana ta  wayar da kan al'umma game da zalunci da a ka yi wa iyalan Annabi (S), Allah yaqara kare yen uwa daga sharrin azzalume.
http://www.5five-stars.com.ng/2019/10/haqiqa-kun-karanta-wannan-kal-mar-kullu.html
0 notes
isiyasy · 5 years ago
Quote
Sakina (AS) ta kasance `ya ce ga Imam Hussaini (AS), ita ce `yarsa karama a mata. Imam Hussaini (AS) ya jima kullum yana addu'a a sallolinsa na dare Allah ya bashi `ya mace, Allah ya amshi addu'ansa ya bashi Sakina (AS). Imam Hussaini (AS) yana matukar son ta, har ma ta kai saboda shakuwarsa da ita kullum da daddare kafin tayi barci ta kan jima a wurin sa, ya na bata labarin Manzon Allah (SAWA) da yakukkuwan da kakanta Imam Ali (AS) yayi, ba zai tashi ba har sai ta yi barci a kan kirjinsa sannan ya mai da ta gun uwarta. Imam Hussaini (AS) ya sha faDan cewa: “Gidan da babu Sakina ba gidan zama bane’'. Kullum ta kasance a cikin fara'a da murmushi, wannan shi ya sa kowa na sonta. Sauran yara kullum su kan zo wurinta, ta kan kuma raba duk abinda take da shi da sauran yaran. Akwai alaka mai karfi tsakaninta da Baffanta Abbas (AS), yana son ta fiye da yadda yake son `ya`yansa. Ba abinda za ta nema Abbas (AS) bai samo mata shi ba. Tun daga biyu ga watan Muharram, lokacin da Sojojin Yazidu (LA) suka fara taruwa a Karbala, sai Imam Hussaini (AS) ya fada wa kanwarsa Zainab (AS) cewa: “lokaci ya yi da Sakina za ta kasance karkashin kulawarki, daga yanzu za ta daina yin barci a wurina”. Idan Sakina (AS) ta biyo shi saboda yin barci a wurinsa kamar yadda ta saba, ya kan Dauke ta ya kai ta gun Zainab (AS) ko kuma uwarta Ummu Rubab (AS). Lokacin da aka shiga 7 ga Muharram sai ruwa yayi karanci a wurin mutanen Imam Hussaini (AS) saboda mamaye kogin Furat da kuma hana ko Digon ruwa ya isa ga Imam Hussaini (AS) da Sojojin Yazidu (LA) suka yi. Sakina (AS) ta raba duk sauran ruwan da suke da shi da sauran yara. Lokacin da ya zamana babu ruwa ko Digo sai sauran yaran suka zo gun Sakina (AS) da tsammanin za ta taimakesu. Suna zuwa sai suka sameta tana rike da kaninta Aliyul Asgar (AS) Dan jinjiri, tana kuka yana kuka. Jinjirin yana lasan hawayen da suke gangarowa daga idanuwanta saboda tsananin kishi. A karshe har ta kai ko tayi kukan ma ba hawaye. Ganin yaran da suka zo wa Danda sun kai 42 wurinta neman ruwa yasa ta jagorancesu zuwa gun Bappanta Abbas (AS) a kan ya sama musu ruwa. Kogin da za a samo ruwan ya kasance a kewaye da Sojojin Yazidu (LA) sun hana ko da Digon ruwa ya isa ga jikan Manzon Allah (SAWA). Yadda Abbas (AS) yaga halin da yaran suke ciki saboda tsananin kishi ya sa hankalinsa ya tashi fiye da abinda ya gani a yinin. Sai ya amshi jakan ruwan a hannun Sakina (AS) ya ce mata: “ku saurara in Allah ya yarda yanzu zan kawo muku ruwa”. Sannan yaje ya nemi iznin Imam Hussaini (AS) ya tunkari Sojojin Yazidu (LA) da nufin samowa su Sakina (AS) ruwa. Tafiyan Abbas (AS) ke da wuya sai duk yaran suka taru a gun Sakina (AS), saboda sun san Abbas (AS) yana kawo ruwan, Sakina (AS) za ta fara basu ne kafin ita ta sha. Sakina (AS) ta tsaya kusa da Babanta Imam Hussaini (AS) idanunta kuma suna kan Tutar da Abbas (AS) yake rike da ita. Abbas (AS) yayi yaki sosai kafin ya isa bakin rafin Lokacin da ya isa bakin rafin sai ya tsugunna don ya debi ruwan. Tsugunawan da yayi sai Sakina (AS) ta bar hango tutar da ke hannunsa, sai ta tsorata sannan ta kalli Babanta Imam Hussaini (AS). Sai Imam Hussaini (AS) ya ce mata: “A halin yanzu Baffanki ya na bakin Kogi”. Sannan sai ta yi murmushi ta ce: “Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah”, sannan ta kira dukkan yaran a kan su zo su tarbi Abbas (AS). Bayan Abbas (AS) ya cikawa su Sakina (AS) goransu da ruwan sai ya juyo, duk kokarinsa shine ruwan ya isa ga yaran. Da kwamandan Yazidu (LA) ya ga cewa Abbas (AS) zai iya isar da ruwan ga tantin Imam Hussaini (AS) sai ya dakawa sauran makiyan tsawa ya na mai ce musu in har suka bari Digon ruwa ya isa ga su Imam Hussaini (AS) to ba za su taba samun nasara a kansu ba. A lokacin ne suka dinga harbo wa Abbas (AS) kibiya kamar ruwan sama. Abinda kawai Abbas (AS) ya sa a ransa shine ya kare ruwan har sai ya isa ga yaran ko da kuwa zai rasa ransa. A kokarin kare jakan ruwan ya rasa hannayensa biyu, aka caka masa kibiya a ido da kirji, ya faDo kasa daga kan dokinsa. Dukkan abinda ke faruwa hankalin Sakina (AS) na kan tutar da Abbas (AS) yake rike da ita ne. Lokacin da Abbas (AS) ya faDi sai ya zamana tutar ma ta fadi kasa. Ko da Sakina (AS) ta daina hango tutar sai ta kalli Babanta Imam Hussaini (AS), amma a wannan karo sai Imam Hussaini (AS) ya kautar da fuskansa. A lokacin ne idanun Sakina (AS) suka cika da hawaye, jikinta ya fara rawa saboda tsoro. Sannan sai ta Daga hannayenta sama ta ce: “Ya Allah kada ka bari su kashe Baffana, ba zan sake neman ruwa ba bayanshi”. Sai ta gudu zuwa gun mahaifiyarta Ummu Rubab (AS). Hankalin Sakina (AS) yayi matukar tashi lokacin da taga Imam Hussaini (AS) rike da Tutar Abbas (AS) cike da jini ta ko’ina, ta tabbatar an kashe Baffanta Abbas (AS). Haka ta kasance cikin hali na bakin ciki har lokacin da aka kashe Babanta Imam Hussaini (AS). Bayan shahadar Imam Hussaini (AS) da sahabbansa su 72, sai ya zamana yanzu ba kowa da ya saura sai mata da yara. Sai sojojin Yazidu (LA) bisa jagorancin Umar bin Sa’ad (LA) suka sa dawakai suka yi sukuwa a kan jikkunan waDannan bayin Allah da sukayi shahada, sannan suka raba kawukansu daga jikkunan na su, suka kasa kawukan a tsakaninsu ciki kuwa da kan Imam Husain (AS) tsarkakakke. Bayan sunyi wannan duka kuma sai suka shiga cire tufafin da ke jikin waDannan bayin Allah suna rabawa a tsakaninsu. Haka suka bar su a kwance ba mai ko getto a jikinsa ciki kuwa har da Imam Husain (AS). Bayan nan kuma sai suka shiga tantin mata da yara suka rika kwace musu kayayyaki, kamar irin su abin wuya da sauransu. A nan ne Shimr (LA) wanda yafi kowa mugunta a cikin Sojojin Yazidu (LA) ya ga Sakina (AS) tana kuka na rashin mahaifinta, kawai sai ya daga hannu ya mareta a fuska sannan ya kama `yan kunnenta ya fincikesu har sai da jini ya dinga zuba daga kunnuwanta. WaDannan makiya Allah kuma la’anannu, ba su tsaya daga kwace musu kaya kawai ba, sai ma suka sa wuta a tantin da suke. Sai duk mata da yaran suka ruga waje a guje. Sakina (AS) yarin`ya `yar shekara biyar! Kayan jikinta sun kama da wuta, kunnuwanta su na zubar da jini, amma duk ba ta damu ba, damuwanta shine ta ga babanta. Sai ta shiga filin Karbala a guje ta na kira: 'Baba! Ina kake? Baba!!, Baba!!! Kamin magana mana'. Da daddare (wato daren Ashura), a lokacin da Imam Hussaini (AS) da sahabbansa suke kwance a filin karbala ba mai ko getto a jikinsa. Zainab (AS) ta tattaro dukkan yara da mata wuri Daya, sai ba ta ga Sakina (AS) ba. Ta tambayi Ummu Rubab (AS) Mahaifiyar Sakinan ita ma ta ce ba ta san inda take ba Sai duka su biyun suka fita nemanta. Suka duba ko ina, amma basu ganta ba. Da suka rasa inda take sai Zainab (AS) ta je inda su Imam Hussaini (AS) suke kwance cikin duhu sannan ta fada cikin kuka: “Ya! Dan uwana, Sakina da ka bari a karkashin kulawana, yanzu bamu san ina take ba. A ina ne zan nemeta a cikin duhun nan?”. Kawai sai ta ga wuta ta haska daga sama, sannan sai Zainab (AS) ta ga Sakina (AS) tana kwance a kan kirjin Babanta Imam Hussaini (AS) kamar yadda ta saba yi kullum. Sai Zainab (AS) ta Daga ta tana cewa: “Sakina! Ta yaya kika gane Babanki? A kan gane mutum ne kawai ta fuskarsa ko kuma kayan da ya sa, Babanki kuma duk ba shi da su”. Sakina (AS) ta mayar mata da amsa da cewa: “Ina so ne in fadawa Babana a kan abinda mutanen nan suka mana, ina so ne in fada masa yadda Shimr ya kwace `yan kunne da sarkan da ya bani, ina so ne in fada masa cewa Shimr ya fincikesu ne daga kunnnena har ya tsaga min fatun kunnena suna jini!, ina so ne in fada masa yadda wa dannan mugayen marasa tausayi suka mareni. A lokacin da nake gudu a cikin filin ne ban san inda zan ga Babana ba sai naji muryan Babana ya na fada min cewa gashi nan a nan. To shine sai na bi muryan har na same shi a kwance a nan. Na kuma na fada masa komai, sannan na kwanta a kan kirjinsa kamar ina bacci yadda na saba yi kullum har kuma kika zo”. Bayan Zainab (AS) ta dawo da Sakina (AS), sai ga matar Hur daga cikin mutanen Umar bin Sa’ad ta kawo musu abinci da ruwa. Sai Zainab (AS) ta dauki jakan ruwan ta je gun Sakina (AS) wacce take barci a lokacin. Ta tada ita, Sakina (AS) ta bude idanuwanta sannan sai Zainab (AS) ta ce mata: “Ga ruwa nan Sakina, ki tashi ki sha, kin jima kina jin kishirwa”. Sakina (AS) na jin kalman RUWA sai ta yi kuka mai tsanani, sannan ta ce: “Baffana ne ya dawo?”, Zainab (AS) ta ce mata a'a matar Hur ce ta kawo. Sannan sai Sakina (AS) ta je gun matar ta sunkuya ta gode mata. Sannan ta ce wa Zainab (AS) dukkanku kun sha ruwan ne? Zainab (AS) ta girgiza kanta alaman ba su sha ba. Sai Sakina (AS) ta tambaya, me yasa to kuma za ki ce ni in sha? Zainab (AS) ta ce mata saboda ke ce karama. Sai Sakina (AS) ta ce a'a Asgar ne karami. Sannan sai ta Dauki jakan ruwan taje inda aka binne kaninta Asgar da Sojojin Yazidu (LA) suka kashe saboda ance su bashi ruwa, tana kuka ta kama cewa: Ya Asgar! Ya Asgar!! Ya Asgar!!! Wannan shine yadda iyalan gidan Manzon Allah (SAWA) suka kasance a daren Ashura. Sun rasa komai, an kashe shugabansu Imam Hussaini (AS), an kashe mazajensu, an kashe `ya`yansu, an sace musu kayayyakinsu, an cinna wuta a tantinsu! Da gari ya waye sai aka harha dasu duka wuri daya zuwa Kufa. Imam Zainul-Abidin (AS) yana kwance ba shi da lafiya amma haka suka tilasta mishi tafiya da kafa. Aka dora matan a kan Rakumi ba ko sirdi hannayensu duk a daddaure. Ba irin wahalan da basu sha ba a han`ya. Kafin isowan su, an sa mutanen Kufa duk sun yi ado an sa furanni duk garin, an kuma yayata cewa Yazid ne ya yi nasara a kan wassu kangararru da suka bar musulunci, saboda haka mutane suna ta buki na murnan cin nasaran Yazidu. Sahl As-Sa’idi sahabin Manzon Allah (SAAW) ne, kuma mazaunin Kufa ne. ya ruwaito cewa lokacin da ya dawo daga aikin Hajji a cikin watan Muharram, ya samu an kawata garin Kufa da furanni na ado, kuma mutane suna ta buki na murna, ya kuma san wannan lokacin ba lokacin yin buki ba ne. saboda haka sai ya matsa kusa da wani dattijo ya tamabaye shi: “Me yake faruwa ne yau a garin?”, sai dattijon ya ba shi amsa da cewa: “Muna buki ne yau sabada yau ranan murna ne, Amirul Muminin Yazid ne ya ci nasara a kan wasu mutane wa danda su ka bar musulunci, kuma shi ne ya sa yau din ta zama rana na murna da farin cikin samun nasarar sa. Kuma yanzu haka ma an kusa a shigo da kamammu na yakin, shi yasa ka ganmu a nan, mu na jira ne mu gan su”. Sahl ya ce; sai na taya a wurin saboda ni ma in gan su, ba a jima ba sai ga su an shigo da su daddaure cikin sarkoki, dubawan da zan yi kuwa sai na hango kan Imam Hussaini (AS) a yanke, sai na tuna da ayoyi da hadisan da sukayi magana kan darajojinsa, sai na bi su har zuwa Sham. Lokacin da suka iso Kufa, sai Ibnu Ziyad (LA) (Gwaman Yazidu a Kufa) ya ba da umurni cewa kawukan waDannan bayin Allah da Sojojin Yazidu (LA) suka tafo da su, a soka su a masu a Daga, a kuma zagaya da su a kan tituna da kasuwar Kufa tare da mata da yara da ke Daure cikin sarkoki domin mutane su gan su. Kwatsam sai rakumin da Sakina (AS) take a kai ya tsaya kusa da wani gida. Sai Zainab (AS) ta lura fuskan Sakina (AS) da alaman akwai magana. Sai ta tambayeta sannan sai Sakina (AS) ta ce mata: “Ina so ne in tamabayeki wani abu amma na san a yanzu goggona ba zaki iya taimaka min ba”. Da Zainab (AS) ta matsa a kan sai ta faDa mata, sai tace: “Ya goggona makogorona ya bushe, bana iya tsammanin zan iya jure kishirwan”. Maganan Sakina (AS) sai yaje kunnen wasu mata da suke kan katangan gidansu suna kallonsu. Sai wata mata daga cikinsu ta je gida ta kawo mata ruwa. Lokacin da matar ta iso gun rakumin su, sai ta fadawa Zainab (AS) cewa tana bukatan a lokacin da yarinyar nan ta shayar da kishirwanta ta mata addu'a. Da Zainab (AS) ta ji haka sai ta hana Sakina (AS) fara shan ruwan har sai ta yi wa matar addu'a, sannan ta juya ta tambayi matar me take so a roka mata, matar ta ce: “Ina so ne ta roka min ka da `ya`yana su dawo marayu kamar ku”. Sai sakina (AS) ta daga hannu tayi mata addu'a sannan ta sha ruwan. Tun daga lokacin da aka kashe Imam Hussaini (AS), Sakina (AS) ta daina ko da murmushi bare kuma dariya. Saboda sanin halin da mahaifiyarta za ta shiga in ta ji tana kuka ya sa Sakina (AS) sai dai ta yi kuka a boye ta share hawayenta. Kullum kuma cikin dare ta kan tashi ta zauna, in an tambayeta ko tana son wani abu ne, sai tace: 'Ina jin kukan jinjiri ne, shin Asgar ne? ya na kuma kira na'. Daga Kufa kuma za su yi Sham ne in da fadar Yazidu (LA) ta ke. Sakina (AS) tana Daure da sarka a bayan rakumin da baiyi da sirdi suka kama han`yan Sham daga Kufa. Kawukan shuhada’u su ne a gaba soke cikin masu, kayin da ke gaba shine kan Imam Husain (AS). Haka suka yi ta tafiya daga wannan garin zuwa wannan, a duk kowane gari aka iso sai anyi yekuwa ga mutanen garin domin su zo su gan su, duk yaro ko wata mace da ta yi kuka kuma sai su dake ta. Haka waDannan bayin Allah daga zuriyan Manzon Allah (SAAW) suka yi ta fama das hi hanya har suka isa Sam (Sham). Yazo a kan cewa sunyi kwana 16 a hanya kafin su iso. Bayan sun iso Sham ne sai aka je aka fadanwa Yazidu (LA) cewa sun iso. Lokacin da Yazidu (LA) yaji labarin isowarsu, sai ya umurci da a tsai da su a bayan gari, har sai shi da mutanensa sun`yi shirin buki na cin nasara. Haka aka tsai da waDannan zuriyan Manzon Allah (SAWA) a bayan gari har tsawon kwana huDu, hannayensu da kafafun su duk a daure. Ba irin wahalan da ba su sha ba. Imam Zainul Abidin (AS) ya fada bayan an sako su cewa mafi munin wahalan da su ka sha shine tsayuwansu a bayan garin Sham na kwana hudu. Sannan aka umurci da su shiga cikin gari. An kawata cikin garin da ado da furanni kuma an umurci kowa yayi ado don murnan cin nasara a kan `yan tawaye! Aka kuma tilasta musu bi ta cikin kasuwa inda mutane suka taru, daddaure kuma a cikin sarka kowa na ganinsu har suka isa fadan Yazidu (LA). A hanyan zuwa fadan Yazidu (LA) ne wani dattijo ya zo wajen Imam Zainul Abidin (AS) ya ce: ‘Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya halaka ku Ya tabbatar da Amirul-Muminina (Yana nufin Yazid)’. Sai Imam Zainul Abidin (AS) ya ce mishi: ‘Ya kai wannan dattijon, shin kana karanta Alkur’ani?’ Sai dattijon ya ce: ‘Kwarai kuwa, ina karantawa’ Sai Imam Zainul Abidin (AS) ya ce mishi: “Ko ka karanta faDar Allah madaukaki; ‘Kace ba na tambayar ku wani lada a kan shi, face kaunar makusantana’? Da faDarsa Madaukaki, ‘Ku ba (kowane Daya daga) makusanta hakkinsu. Da faDarsa Madaukaki, ‘Ku sani cewa lallai abin da ku ka ganimantu daga wani abu lallai Allah da ManzonSa da Makusanta na da Khumusinsa (kashi daya bisa biyar)? Sai dattijon ya ce: ‘Kwarai na karanta hakan. Sai Imam Zainul Abidin (AS) ya ce: “Wallahi mu ne makusanta a wadannan ayoyin” Sannan sai Imam Zainul Abidin (AS) ya sake ce masa: “Ko ka karanta faDar Allah Madaukaki, ‘Lallai Allah na nufin kawar da duk wata dauDa daga gareku Ahlulbaiti, ya kuma tsarkakeku, tsarkakewa’? Sai dattijon ya ce: ‘kwarai na karanta’. Sai Imam Zainul Abidin (AS) ya ce masa: ‘Mune Ahlulbait Din da Allah ya kebe su da tsarkakewa’. Sai dattijon ya ce: ‘Don Allah ku ne waDannan? Imam Zainul Abidin (AS) ya ce masa: ‘Hakika mu ne su ba shakka’. Sai dattijon ya ciji hannu don takaicin abinda ya faDa, ya kuma roki gafaran Imam Zainul Abidin (AS). Bayan sun je fadan Yazidu (LA), ya nemi ya tozarta su, inda ya sa wani mawaki a fadansa ya zagi Imam Hussaini (AS) da Imam Ali (AS). Sai Imam Zainul Abidin (AS) ya ce ya na so a bar shi shima yayi magana, sai Yazidu (LA) yaki yarda, amma sai mutane suka matsa a kan lallai sai ya bar shi aji me zai ce. Sai Yazidu (LA) ya ce: “Ba na son in bar shi ya yi magana ne saboda su sun gaji ilimi da fasaha”. Mutanen da suke fadan dai suka matsa lallai su suna so suji me zai ce. A dole Yazidu (LA) ya bar Imam Zainul-Abidin (AS) yayi magana. Bayan ya yabi Allah da Manzon Allah, sai yace: “Ya ku mutane an bamu abubuwa shida, an kuma fifitamu da wasu bakwai. An bamu ilimi, hakuri, yafiya, fasaha, gwarzantaka da kauna a cikin zukatan mutane. An kuma fifita mu da cewa a cikinmu akwai Annabi, a cikin mu akwai Siddiki, a cikinmu akwai mai tashi sama (Jafarud Dayyar), a cikinmu akwai Zakin Manzon Allah (SAAW) (Imam Ali (AS), a cikinmu akwai Shugabar matan duniya Fatimatu al-Batul da jikoki biyu na wannan al’umma. Ya ku mutane! Wanda ya sanni ya sanni, wanda kuma bai sanni ba, yanzu zan bashi labarin dangina da matsayina. Ni ne Dan Ka’aba da Minna, ni ne Dan Zam-Zam da Safa, ni ne Dan wanda ya Dauki bakin dutse da gefen mayafi, ni ne Dan mafi alherin wanda ya sa sutura da mafi alherin wanda ya yi Dawafi, ya yi sa’ayi, ya yi hajji ya amsa kiran Allah. Ni ne Dan wanda aka Dauka a Buraka kuma Jibrilu ya kai shi Sidratul Muntahah, sai ya kasance kamar kusancin tsakiyar baka ko fiye da haka. Ni ne Dan wanda ya yi Sallah da Mala’ikun sama. Ni ne Dan wanda Mabuwayi ya yi mishi wahayin abin da ya mishi wahayi. Ni ne Dan Fatimatuz Zahra da kuma Khadijatul Khubra. Ni ne dan wanda aka yanka a Karbala!”. Daidai lokacin da ya kawo nan sai duk mutanen da suke wurin suka fashe da kuka, saboda sun fahimci gaskiya. Da Yazidu (LA) ya ga haka sai ya ce mai kiran Sallah ya tashi ya kira Sallah wai lokacin sallah ya yi don ya yanke Imam Zainul Abidin daga hudubar sa. Imam Zainul Abidin ya saurara wa mai kiran sallan har sai da ya gama faDar Ash-hadu Anna Muhammadar Rasulullah; sai ya cewa mai kiran sallan ina gama ka da Allah da kayi shiru har sai nayi magana da wannan (Ya nuna Yazid), sannan sai ya juya gun Yazidu (LA) ya ce masa: “Wannan manzon mai girma, mai daraja da mai kiran Sallah ya ambata kakanka ne ko kakana? In ka ce kakan ka ne to dukkan wa danda suke nan da ma dukkan mutane za su tabbatar cewa kai makaryaci ne, in kuma ka ce kakana ne to me ya sa ka kashe babana bisa zalaunci, ka kama matansa? To Bone ya tabbata a kanka (ya Yazid) ranar kiyama idan kakana ya kasance shine abokin jayayyanka”. HuDubar ta sa ne ta sa mutane su ka fahimci ashe waDannan da aka yi wa haka ba wasu kangararru 'yan tawaye bane kamar yadda da fari aka yaDa musu, a'a zuriyan Manzon Allah (SAWA) ne kaf a wurin. Da Yazidu (LA) yaga mutane sun fara fahimtan matsayinsu, sai yayi umurni da a kai su gidan fursunoni da yafi kowanne muni kuma na karkashin kasa, ga duhu da dotti, har ta silin kin gidan yarin ya faDo. A gidan Yarin Sakina (AS), yarinya `yar shekara biyar ta kan gagara yin barci saboda tunanin Babanta. Zainab (AS) ta kan rarrasheta da cewa nan gaba kaDan za ta ga Babanta, waDannan maganganun na Zainab (AS) su suke sa wa ta yi barci Dan kaDan. A cikin gidan yarin akwai sabbon tsuntsaye, in magariba tayi sakina (AS) ta kan fito tana kallon yadda tsuntsayen suke dawowa suna shiga gidajensu, sai kuma ta juya gun Zainab (AS) ta tambayeta cewa: “Yanzu Sakina ma za ta koma ta shiga gida kamar yadda waDannan tsuntsayen suke shiga gidajensu?” A wani dare, bayan Sakina (AS) ta fara barci kawai kwatsam sai ta farka ta kama kuka da karfi, ta kuma shiga neman Babanta ta ko ina. Dukkan matan da suke gidan yarin sun yi ta bata hakuri a kan ta daina kukan, amma ina sai ma karawa take yi. Sannan ta kalli Zainab (AS) ta ce mata: “Ya goggona! Ina Babana yake? Mintuna kadan da suka wuce ina tare da shi har ya sumbanceni ya ce min `ya ta Sakina an jima kadan za ki kasance tare da ni. Amma yanzu ban gan shi ba, ina Babana? Ina Babana??”. Bayan Sakina (AS) ta fadi mafarkin da ta yi, sai duk matan gidan yarin suka kama kuka. Lokacin da kuka ya yi yawa a gidan sai Yazidu (LA) ya turo bawansa ya tambaya me ya faru. Sai aka fada masa cewa ai Sakina ce ta ke kuka saboda ta rasa Babanta, har ta sa sauran ma kuka. Lokacin da Yazidu (LA) ya ji dalilin kukanta sai ya tura da a Dauko kan Imam Hussaini (AS) a kawo mata. Lokacin da Sakina (AS) ta ga kan babanta a faranti sai ta rike kan da karfi ta ci gaba da kuka fiye da na da, tana cewa: “Waye ya cire kan Babana? Waye ya kashe Babana? Me ya sa aka mai da mu fursunoni? Tana maganan tana kuka da karfi kawai sai aka ji ta yi shiru, sai duk gidan fursunan yayi tsit kowa yayi tsammanin Sakina (AS) ta koma barci ne, amma wannan karon ba bacci ne na lokaci kankani ba, a'a barci ne na din-din-dim. Lokacin da Imam Zainul-Abidin (AS) ya je ya duba ta sai ya ji ta daina numfashi. Sai duk matan gidan yarin suka zagayeta suna kuka. Bayan an bunneta a cikin gidan yarin sai Mahaifiyar ta da duk sauran matan suka zagaye kabarinta suna kuka. Duk gidan yarin sai ya dauki karan abinda suke fada: Ya Sakina! Ya Mazluma!! Ya Sakina!!! Assalamu Alaiki Ya Sakina! Amincin Allah ya tabbata a gareki lokacin haihuwarki da lokacin wafatinki da lokacin da za a tayar da matattu!! Tammat Bi-Hamdillah! MADOGARA Mai son karin bayani yana iya duba waDannan littatafan: § Al-Ihtijaj na Alamma Abu Mansur Ahmad Tabrisi § Maktalul Husain na Muwak ibn Ahmad Alkawarizmi § Taskiratul khawas na Ibnu Jauzi § Tarikh al-Kamil na Ibn Asir § Bidaya wan Nihaya na Ibn kasir § Al-Sawa’ikul Muhrika na Ibn Hajar al-Askalani § Tarikhul Khulafa na Hafiz Jalaluddinis suyudi.
http://www.5five-stars.com.ng/2019/10/shahadar-sayyida-sakina-as-10-ga-watan.html
0 notes
isiyasy · 5 years ago
Quote
Rakuma dai suka kama hanyar Kufa suna dauke da iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a) a matsayin fursuno-nin yaki. Sun kama hanyar ne kuwa a rana ta biyu da faruwar wannan aika-aika (sha daya ga watan Muharram). Haka dai wannan ayari na fursunonin suka tsaga zafin hamada ba abin da ke tare da su in ban da tunanin wannan bala'i da kuma daren rabuwa mai ban tsoro, wato daren sha daya ga wata, wanda suka kasance a cikinsa a kan jikkunan shahidai da aka kashe. A wannan lokaci dai wadannan iyalai na Manzon Allah (s.a.w.a) suna kewaye ne da wadannan marasa imani, mashaya jini, wadanda suke jin dadin ganin halin kuncin da wadannan fursunoni suke ciki da kuma kukan da mataye da kananan yara suke yi da kuma halin da Aliyu bn al-Husaini (a.s) yake cikin saboda tsananin rashin lafiya da kuma sarkokin da aka daure shi da su. Haka dai wannan ayari suka shigo garin Kufa, mutanen garin Kufan kuwa suka fito bakin tituna cikin mamakin ganin halin da suke ciki, wasu suna tambaya wadannan fa su wane ne, wasu kuma wadanda suke da masaniyyar abin da ya faru suka kasance cikin damuwa, nadama da kuma kunya kan abin da ya janyo hakan. Haka dai wannan ayari ya kutsa kansa cikin mutanen Kufa, wadanda suke a kan hanyarsu ta zuwa fadar Ubaidullah bn Ziyad, suna masu kuka da juyayin abin da ya samu Iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a) saboda ha'inci da suka yi wa shugaban musulmi kana kuma jikan Manzon Allah, Imam Husain (a.s). A halin yanzu ga su nan suna ganin iyalansa, matansa, matan sahabbansa a matsayin fursunonin yaki, suna fuskantar dukkan wani nau'i na azaba daga Iyalan Ziyad. A waje guda kuma ga kan jikan Manzon Allah nan an tsire shi a kan saman garin Kufa a kan mashi mai tsawon gaske, alhali kuwa su suka kira shi don ya zamanto shugaban al'umma kana mai shiryar da su zuwa ga tafarki madaidaici. Zainab 'yar Aliyu bn Abi Talib (a.s) ta dubi wadannan mutane da suka taru hawaye na zuba mata saboda tunanin rashin dan'uwanta Husaini (a.s) da ta yi, cikin fushi ta ce musu su yi shiru da bakinsu don ta gabatar musu da jawabi. Nan take suka yi shiru don sauraron abin da Zainab, 'yar Fatima al-Zahra, 'yar'uwar Husaini (a.s) za ta gaya musu, ta fara da cewa: "Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, tsira da aminci su tabbata ga Babana Muhammad da iyalansa tsarkaka zababbu. Bayan haka, Ya ku Mutanen Kufa, Ya ku ha'inai maciya amana; shin kuna kuka ne? To kada Allah Ya sa hawayenku ya bushe, sannan kuma kada wannan juyayi naku ya kare. Ku dai tamkar macen da ta kuncen igiyar da ta riga da ta kitsa ta ne(1), imaninku bai kasance ba face ha'inci da yaudara. Shin a cikinku akwai wani mutum in ban da mai da'awar karya na girman kai, wulakantacce, abin kyama, dan koran sarakuna, abin harin abokan gaba, tsiron da ke cikin bola(2), ko kuma kamar azurfar da ke cikin kabari(3)? Ya munana abin da zukatanku suka kitsa muku, Allah Yana fushi da ku, kuma lalle za ku tabbata cikin azaba. Shin kuna kuka da nuna juyayi ne? To wallahi ku yi kuka da yawa kana ku yi dariya kadan, don kuwa ayyukanku sun munana ta yadda ba za ku iya wanke su ba. Shin ya ya za ku iya goge laifin kashe silsilar Cikamakin Annabawa, ma'adinin sakon (Musulunci), shugaban matasan Aljanna, makomar zababbunku, makomar da kuke komawa yayin musiba, hasken hujjojinku kana kuma mai kare sunnoninku. Lalle laifin da kuka aikata ya munana, kuma ya koma gare ku, babu tuba gare ku. Hakika kokarinku ya gaza kamar yadda hannayenku ma suka gaza, kun yi asara, ba abin da kuka sa kawukanku a ciki face fushin Allah, kamar yadda wulakanci da kaskanci suka fada muku. Kaiconku Mutanen garin Kufa! Shin kun san yadda kuka keta hantar Manzon Allah? Kuma wace 'yarsa ce kuka keta huruminta? Kuma wani jininsa ne kuka zubar kana kuma wani haraminsa ne kuka keta? Hakika ayyukanku sun munana kwarai da gaske, wanda munin nasu ya cika sama da kasa. Shin za ku yi mamaki idan sama ya yi ruwan jini? Lallai azabar ranar lahira ya fi zafi kuma ba ku da mataimaki. Kada jinkirin da aka yi muku wajen azaba ya rude ku lallai Ubangijinku Yana nan a madakata(4)". Daga nan sai tawagar fursunonin gidan Manzon Allah (s.a.w.a) suka wuce cikin hanyoyin garin Kufa zuwa fadar mulki don su gana da Ubaidullah bn Ziyad wanda yake zaune a fadar tasa yana karban gaisuwar mutanen da suka zo masa barka da samun nasarar da ya yi kan wadanda suka yi kokarin tunkude mulkin Umayyawa. Ya zauna cikin girman kai alhali kan Husaini (a.s) yana gabansa yana wasa da shi da kuma bugun kan da bulaliyar da take hannunsa cikin farin ciki da annashuwa. Wannan yanayi dai ya sosa wa wani tsohon sahabi mai suna Zaid bn Arkam rai, sai ya kalli Ibn Ziyad wanda a daidai lokacin yana dukan fuskar Husaini (a.s) ya yi masa tsawa ya ce: "Daga bulaliyarka daga wadannan laba guda biyu, na rantse da Ubangijin da babu wani ubangiji sai shi, na ga labban Manzon Allah (s.a.w.a) guda biyu a cikinsu (labban Husaini) a lokuta da yawan da ba zan iya kirga su ba". Daga nan sai ya fashe da kuka. Sai Ibn Ziyad ya ce: "Allah Ya sa idanuwanka su zubar da hawaye, shin kana kuka ne saboda nasarar da muka samu? Da ba don kai tsoho ba ne wanda hankalinsa ya fita daga gare shi ba, da na sare kanka". Nan take Zayd bn Arkam ya fice daga fadar cikin fushi, yana mai share hawayen da ke zubo masa da kuma tunanin yadda yake daukan wannan abin kauna nasa Husaini a lokacin yana dan karami. Yayin fitarsa daga fadar, an jiyo shi yana cewa: "Daga yau Ya ku Larabawa kun zama bayi, kun kashe dan Fatima kuka dora Ibn Marjana (a matsayin shugabanku), alhali kuwa yana kashe mafiya daukakanku da kuma daukaka mafiya sharrinku, kun yarda da wulakanci, Allah wadaran wanda ya yarda da kaskanci(5)". Fitan wannan tsohon sahabi ke da wuya sai aka shigo da fursunonin(6) yakin gidan Manzon Allah (s.a.w.a) cikin fadan mulki. Aka gabatar da mata da yara da Aliyu bn al-Husain al-Sajjad (a.s) gaban Ibn Ziyad, inda Ibn Ziyad din ya dubi Zainab, 'yar'uwan Husaini (a.s) wacce kuma ta dau tuta da kuma nauyin isar da sakonsa iya tsawon rayuwarta, ya ce mata: "Godiya ta tabbata ga Allah da Ya wulakanta ku, Ya kashe ku da kuma bayyanar da ikirarinku na karya(7)". Nan take Zainab ta mayar masa da kakkausar martani da ya jijjiga duk wadanda suke wannan fada, inda ta ce: "Godiya ta tabbata ga Allah da Ya karrama mu da Annabinsa Muhammadu (s.a.w.a), Ya kuma tsarkake mu tsarkakewa(8), sannan kuma ya wulakanta fasiki, fajiri wanda ba shi daga cikinmu". Sai Ibn Ziyad ya ce: "Ya ya kika ga yadda Allah Ya yi da iyalanki?". Sai ta ce: "Allah Ya rubuta musu mutuwa, don haka suka gaggauta zuwa makomarsu, kuma da sannu Allah Zai tada kai da su, kuma za ka amsa tambayoyi a gabanSa(9)". Haka dai maganganu masu zafi suka ci gaba da fitowa daga bakin Zainab da Ibn Ziyad har lokacin da aka zo da Aliyu bn Husain al-Sajjad (a.s) don tsayawa gaba ga Ibn Ziyad. Sai Ibn Ziyad ya tambaye shi: 'Kai wane ne?', sai Imam Sajjad (a.s) ya amsa masa da cewa: "Ni ne Aliyu bn al-Husain". Sai Ibn Ziyad ya sake tambayarsa: "A'a ashe Allah bai kashe Aliyu bn Husain ba?, nan take sai al-Sajjad (a.s) ya mayar masa da martani da cewa: "Lalle ina da wani kani da ake kiransa shi ma Aliyu, amma mutanen sun kashe shi". Sai Ibn Ziyad ya ce: "A'a Allah ne dai Ya kashe shi", nan take sai al-Sajjad ya mayar masa da martani: "A'a, Allah Yana daukan rai ne lokacin mutuwarta". Wannan kalami na al-Sajjad dai ya bata wa Ibn Ziyad rai, don haka sai ya dubi sojojinsa yana ce musu: 'Ku sare kansa'. Ganin haka sai Zainab ta zabura ta ce: "Ya Ibn Ziyad zubar da jininmu ya ishe ka haka nan, wallahi ba zan rabu da shi ba, idan har za ka kashe shi sai dai ni ma ka kashe ni tare da shi(10)". Ibn Ziyad dai ya amince da wannan bukata ta Zainab, don haka sai ya fita ya tafi masallaci don yin jawabi ga mutane da kuma sanar da su batun kashe Husain (a.s) da kuma 'nasarar' da Yazid ya samu. Daga cikin wadanda suke gurin har da Abdullah bn Afif al-Azdi(11) wanda kuma ya ji shi yana cewa: "Godiya ta tabbata ga Allah Wanda ya bayyanar da gaskiya da ma'abutanta da kuma ba wa Amirul Muminina Yazid da 'yan kungiyarsa nasara, Ya kuma wulakanta makaryaci dan makaryaci Husain bn Ali da 'yan shi'ansa(12)". Wannan kalami dai ya bata wa Abdullah rai don haka sai ya mike don fuskantar Umayyawa duk kuwa da karfin takobi da bulali da suke da shi, yana mai cewa: "Ya Ibn Marjana, kai da babanka ne makaryaci kuma dan makaryaci da kuma wanda ya dora ka akan karagar mulki da kuma babansa. Ya Ibn Marjana, shin za ka kashe 'ya'yan Annabawa ne sannan ka yi magana da kalaman masu gaskatawa(13)". Wannan kalami na Abdullah dai ya yi girma wa Ibn Ziyad da kuma bata masa rai alhali kuwa ga shi nan yana cikin giyan mulki, babu wani abin da kawai zai sa ya huce face dai ya kashe shi, don haka sai ya ba da umarnin a kashe shi. To sai dai kuma hakan bai samu ba don kuwa kimanin mutane dari bakwai daga cikin kabilar su Abdullah din sun mike da kuma nuna rashin amincewa da hakan. To amma Ibn Ziyad dai bai hakura, don sai da ya aike da sojojinsa cikin dare suka tafi gidan Abdullah bn Afif din suka fito da shi, suka kashe shi da kuma tsire gawarsa. Ta haka ne dai ya samu ya yi shahada yana mai jaddada kalmar gaskiya ga ja'irin shugaba. Wannan gaba da kiyayya ta Ibn Ziyad dai ba ta kare ba, face dai sai da ya fito garin Kufa a rana ta biyu yana yawo da kan Husaini (a.s) a kan titunan garin, yana mai tsoratar da mutanen garin da kuma raunana ruhin masu son yi masa tawaye. Daga nan aka dawo da wannan kai mai albarka zuwa fada, don wucewa da shi zuwa Sham a kan mashi mai tsawo(14). Haka dai aka wuce da wadannan kawuka, na Husain (a.s) na gaba kana sauran kuma suna baya suka keta hamadan kasar Iraki. A baya gare su kuma ga Zainab (a.s) wacce ta karbi tutan wannan yunkuri tun daga ranar da aka kashe Husaini (a.s). Kamar yadda kuma sauran mata da yara da Aliyu bn Husaini (a.s) wanda yake cikin sarka tun daga kafarsa har wuya(15) suke biye, an dora su dukkansu akan rakuma marasa sirdi(16). Haka dai aka wuce da wadannan kawuka da kuma fursunonin yakin zuwa Damaskus babban fadar gwamnatin Umayyawa, bisa umarnin Yazid bn Mu'awiyya cikin wasikar da ya aike wa Ibn Ziyad yana mai ce masa 'ka gaggauta aiko da fursunonun yakin zuwa wajena(17), ta hakan kuwa yana so ne ya bayyanar da tsananin kiyayyarsa ga Iyalan Manzon Allah (s.a.w.a) da za su tsaya a gabansa alhali suna cikin mawuyacin hali. ____________ (1)- Wannan ibara ce da take nuni da irin ha'inci da rashin cika alkawarin da mutanen Kufan suka yi. (2)- Tsiron da ke cikin bola: Duk tsiron da ke rayuwa cikin najasar dabbobi, zahirinsa na da kyau to amma jijiyoyinsa suna cikin kazanta da kashi dabbobi. (3)- Azurfan da take cikin kabari, zahirinta na da haske amma babu komai a kasanta in ban da mutuwa. Hakan gugan zana ne da ke nufin ha'inci. (4)- Wannan huduba tana cikin Maktal al-Husaini na al-Khawarizmi, juzu'i na 2, shafi na 40-42. (5)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 243, Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafi na 349 da kuma Ibn Kathir, juzu'i na 8, shafi na 190. (6)- Arayin gidan Manzon Allah (s.a.w.a) sun iso garin Kufa ne daga Karbala rana ta biyu bayan isowar kan Husaini (a.s) ne. (7) - Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 244. (8)- Anan tana nuni ne da ayar nan mai girma ta cikin Suratul Ahzab 33:33, inda Allah Ya ke cewa: "Allah kawai na nufin ya tafiyar da kazamta ne daga gare ku, Ya ku Mutanen babban gida, Ya kuma tsarkake ku tsarkakewa". (9)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 244. (10)- Kamar na sama. (11)- Yana daga cikin mabiya Imam Ali (a.s) da kuma Ahlulbaiti. (12)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 244. (13)- Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafin 351, da Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 83, haka nan kuma al-Kufi cikin littafinsa Al-Futuh ya kawo wani abu daga cikin labarin al-Azdi da kuma yadda ya yi shahada, dubi juzu'i na 3, shafi na 144 zuwa gaba. (14)- An ba wa Jazr bn Kais nauyin daukan kan Husaini (a.s) da sauran kawukan sahabbansa daga Kufa zuwa wajen Yazid bn Mu'awiyya a garin Damaskus. (15)- Ibn Athir cikin al-Kamil fi al-Tarikh, juzu'i na 4, shafi na 83. (16)- Ibn Athir cikin al-Kamil fi al-Tarikh, juzu'i na 4, shafi na 83 da kuma A'atham al-Kufi cikin al-Futuh juzu'i na3, shafi na 147. (17)- Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir juzu'i na 4, shafi na 84 da kuma Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafi 354.
http://www.5five-stars.com.ng/2019/10/tafiya-da-iyalan-manzon-allah-kufa.html
0 notes
isiyasy · 5 years ago
Quote
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata da Manzonsa da dukkanin Alayensa. Allah Ya yi gaskiya a yayin da ya ce: Sa'an nan karshen wadannan da suka aikata mugun aiki ya kasance mafi muni, saboda sun karyata ayoyin Allah, kuma suka kasance suna izgili da su". (Surar Rum:10). Ya Yazid, shin kana tsammani ka kwace kasa da sama ne daga gare mu don ana yawo da mu kamar yadda ake yawo da fursunoni, sannan kuma mu wulakantattu ne a wajen Allah kai kuma mai daukaka? Saboda wannan nasara ta zahiri ne da ka samu ya sa kake alfahari da dagawa, kana mai tsammanin ka sami wata kyauta ce ta duniya kuma lamurranka sun daidaita haka nan kuma mulkinka ya dawo hannunka. To amma ka dakata kadan, kada ka yi farin ciki. Shin ka mance da fadin Allah Madaukakin Sarki ne cewa: "Kuma kada wadanda suka kafirta su yi zaton cewa, lalle ne, jinkirin da Muke yi musu alheri ne ga rayukansu. Muna yi musu jinkirin ne domin su kara laifi kawai, kuma suna da azaba mai wulakantarwa". (Surar Al'Imrana: 178.  Ya kai dan sakakku! Shin wannan shi ne adalcinka, ka bar 'ya'yaye da kuyanginka cikin sutura amma ka sanya ana yawo da 'ya'yan Manzon Allah titi-titi cikin mawuyacin hali a matsayin fursunoni. Ka ci mana mutumci ta hanyar bayyanar da fuskokinmu. Sojojinka sun dinga yawo da mu daga gari zuwa gari, dukkan nau'oi na mutane, mazauna duwatsu da bakin teku suna kallonmu, Na kurkusa da na nesa, wulakantattu da madaukaka dukkansu suna kallonmu alhali kuwa muna cikin wani irin hali da babu wani namiji tare da mu da zai taimaka mana ko ba mu wata gudummawa. Ya Yazid, duk wani abin da ka aikata yana nuni ne da tawayenka ga Mahalicci da kuma rashin imaninka da Manzo (s.a.w.a), Littafin Allah da kuna Sunnar da Annabi ya zo da ita. Lalle ayyukanka ba za su kasance abin mamaki ba, don kuwa duk mutumin da kakanninsa suka ci hantar tsarkakakkun bayi, wanda namansa ya ginu daga jinin shahidai, wadanda suka yaki shugaban dukkan Annabawa, ba abin mamaki ba ne in ya wuce dukkan larabawa wajen kafirci, aikata sabo da kuma kiyayya da Allah da ManzonSa (s.a.w.a). Ka tuna fa wadannan munanan ayyuka da ka aikata sun samo asali ne daga kafirci da kuma kullin da kake da shi saboda kakanninka da aka kashe a Badar. Hakika duk mutumin da ya sanya idanuwan kiyayya da gabansa a kanmu ba zai yi kasa a gwuiwa wajen aiwatar da wannan kiyayya a kanmu ba. Lalle ya tabbatar da rashin imaninsa da kuma bayyanar da shi da harshensa lokacin da ya ce cikin farin ciki: "Na kashe 'ya'yan Manzon Allah da kuma mayar da iyalansa fursunoni" da kuma fatan da kakanninsa sun rayu su ga wannan nasara da ya cimma don su ce 'Ya Yazid, kada hannayenka su rasa wannan karfi, lalle ka dau mana fansa a madadinmu. Ya Yazid, shin kana dukan lebban Imam Husain ne da sandanka a gaban jama'a bayan kuwa Manzon Allah (s.a.w.a) ya sha sumbantan wadannan lebba, amma duk da hakan kana cikin farin ciki da annashuwa. Na rantse da Allah, lalle ka kara mana zafin ciwonmu da kuma cutar da mu gaba daya ta hanyar kashe Shugaban matasan Aljanna, dan shugaban larabawa (Ali) kana kuma tauraron iyalan Abdul-Mutallib mai haske. Ta hanyar kashe Husain bn Ali (a.s), lalle ka kusa isa ga makoman kakanninka marasa imani da Allah. Kana bayyanar da wannan aika-aika da ka aikata cikin alfahari da kuma fatan cewa idan kakannin naka suka ga aikin naka za su yarda da shi da kuma yi maka addu'an kada hannunka ya raunana. Ya Allah, Ka karbo mana hakkinmu, Ka dau mana fansa akan wanda ya zaluncemu, Ka nuna fushinKa ga wanda ya zubar da jininmu. Ya Yazid! Ka aikata duk abin da kake so, amma ka kwana da sanin cewa ka yanka jiki da namanka ne da kanka gunduwa-gunduwa. Nan gaba kadan za a gabatar da kai gaban Manzon Allah (s.a.w.a), lalle nauyin mummunan aikinka na zubar da jinin iyalansa da kuma wulakantasu zai gagare ka dauka. Za a kaika inda za a kaika ne a idanuwan iyalan gidansa, inda za a dau fansa kan azzalumai da kuma azabtar da makiya, Kada ka yi zaton wadanda aka kashe a tafarkin Allah matattu ne, A'a rayayyu ne su a wajen Ubangijinsu, ana ciyar da su. Suna masu farin ciki saboda abin da Allah Ya ba su na daga falalarSa, (Surar Al'Imrana: 169-170). Hakika Allah ya isa ya hukumtaka, Manzon Allah kuma ya kasance mai husuma da kai kana Jibrilu kuma shi ne mai taimakonmu. Lalle da sannu wadanda suka dora ka akan musulmi da kuma wahalar da su za su ga abin da ke jiransu, kuma lallai makomar azzalumai ta munana ta zama makoma. Ya Yazid! Ba wai ina maka wadannan maganganu da kuma nusar da kai irin azabar da ke jiranka don ko ka yi nadama kan abin da ka aikata ba ne, a'a, don kuwa kai kana daga cikin mutanen da zukatansu suka kekashe, wadanda rayukansu da jikkunansu suka tarbiyyantu da sabon Allah, wadanda kuma suke karkashin la'anar Manzon Allah (s.a.w.a). Lallai kai kana daga cikin mutanen da Shaidan ya yi musu tambari a kan zukatansu, ba abin da suke haifarwa in ban da sharri. Babban abin mamakin shi ne kisan gillan da 'ya'yan sakakkun masu sabo suka yi wa bayin Allah, ya'yan Annabawa da wasiyyai. Hannayensu sun zubar da jininmu kana kuma namanmu ya kasance musu kalace. Lallai muna jin zafi ga wadanda aka bar gawawwakinsu a yashe a fagen daga ba tare da an bisne su ba. Kai Yazid, idan har kana tunanin cewa wannan abin da ya same mu a matsayin wata nasara gare ka, to lallai za ka dandana kudanka kan hakan a lokacin da ba abin da za ka gani face abin da ka aikata, don kuwa Ubangijinka ba ya zaluntar bayinSa. Allah Shi ne abin dogaronmu kuma Shi ne kawai muka mika burinmu gare Shi. Ka yi dukkan makircin da ka ke iyawa, sannan ka yi dukkan kokarin da za ka iya, amma dai wallahi ba za ka iya shafe ambatonmu ba da kuma dushe haskenmu, haka nan kuma ba za ka kawar da wannan wulakancin da kake ciki ba. Shin akwai wani abin da ya rage wa kalamanka in ba rauni ba, haka nan kuma ranakunka face 'yan kididdigaggu ba. Lallai ka kiyaye ranar da mai sanarwa zai sanar da la'anar Allah a kan azzalumai. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai, Wanda ya cika wa na farkonmu da sa'ada da kuma gafara, kana na karshenmu kuma da shahada da rahama, muna rokon Allah da ya cika musu da lada Ya kuma kara musu Ya kuma kyautata mana halifanci, don kuwa Shi Mai rahama ne, kuma lalle Allah Ya isar mana kuma madalla da wakilcinSa. >==> Isiya Sy D Young-Gifted.
http://www.5five-stars.com.ng/2019/10/hudubar-zainab-al-kubra-fadar-yazid-bn.html
0 notes